IDAN RANA TA FITO...

2.4K 181 48
                                    

MADUBI
       ©AYEESH CHUCHU

I dedicated this chapter to all my lovie_dovies,you guys has touched my life in one way or the other. Thank you so very much. I love you from the electrons round on the orbital..
Thanks a million for the birthday wishes, really appreciated 😍😍😘😘😘

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

IDAN RANA TA FITO...

"Ammah tashi har anyi sallah fa, ina ta tada ki".
  Kamar an jeho ta ƙasa haka ta wuntsulo daga kan gado tana murza idanunta.
Cikin azama ta faɗa banɗaki,tayo alwala . Nan ta isko Layla na azkar,ta shimfiɗa ma ta daddumar sallah.
  "Ga riga da hijabin sallah nan na ajiye ma ki".
  Ta idar da sallarta ta dau Alƙur'ani da ke ajiye ta fara karantawa cikin zazzaƙar muryarta.
  Layla na jingine da bango tana lumshe ido saboda daɗin ƙira'ar.
  Sai wajen bakwai saura suka tashi,suka koma bacci.

Bacci Ammah take tare da mafarkai masu daɗi cike da burirrika.
Ƙarar alarm ɗin da Layla ta seta ne ya tashi Ammah.
Tana tsaka da hamma Layla ta farka.
Ta kalli gundumemen tsaron da ke kan Amma guda biyu da tsagar ma ta haɗe sai jelar gashinta da ke reto a saman kafaɗunta.
Yamutsa fuska tayi.
"Amma tashi kiyi wanka kin san zamu fita,a gyara ma ki kanki".
Ta gyada ma ta kai.
"Mu je ki ƙara gwada min bayin can na ku mai wuyar sha'ani".
Murmushi Layla tayi.
"With time za ki saba".
Sai da tabbatar ta haɗa ma Ammah duk wani abu da take buƙata tukunna ta fito.
  Wardrobe ɗinta ta buɗe ta fiddo da dogayen riguna abaya guda biyu ,ɗaya mai ratsin baƙi da ja,ɗayar kuma baƙi da golden brown.
   Ta gyara gadonsu ta kakkaɓe,Ammah ta fito daure da towel da face towel tana goge fuskarta.
  Stool ɗin da ke gaban dressing mirror ta ja ta zauna.
"Mai kadai za ki shafa ga turaruka nan kisa kayanki kafin in fito".
Ƙofar fita daga ɗakin tayi ,corridor ne  ya miƙe . Gaban shoe rack ta tsaya ta fiddo takalma biyu wadge sandals mai kalar ja da golden brown. Ta goge su,sannan ta koma ɗakin.

      ***
Kamar su ce ta fito muraran,murjewa da hasken fata Layla za ta gwada ma Ammah saboda hutu sai mulmulallen jiki da take da shi,wanda ya boye tsayinta.
Jerawar da suka yi da Ammah ya fiddo da tsayinta.
Kafaɗun Ammah ta kama.
"Oyaa dubi kanki a MADUBI ki gani.. You're more than beautƴ".
Baki Ammah ta buɗe tana kallon fuskarta da ta ji foundation sai hodar ta kwanta lumui a fuskarta.
  Bakinta dan tsugut mai dauke da kissable lips sunyi gwanin ban sha'awa cikin dark purple lip liner da light purple lipstick mai hadari-hadarin pink.
Zara-zara gashin idonta sun ƙara miƙewa samɓal kamar tayi ƙari a sakamakon mascara da Layla ta shafa ma ta.
Tayi kyau matuƙar kyau. Sai zuba ƙamshin setin Tomford masu ƙamshi da tsada.
Kamar ƴan biyu haka suka jero.
Gaban shoe rack suka tsaya saka takalmansu.
   Ɗakin Mami suka nufa,sunyi sallama ta amsa,ta na fesa turare.
Nan suka haɗa baki suka gaidata.
"MashaaAllah! You all look cute. A tafi a gaida Abba a shirya dinningtable gamu nan fitowa". Suka amsa ma ta tare da sa kai su ka fita.
  Falon Abba suka shiga ,ƴana zaune yana kallon TVC news,ya rage ƙarar tv suka gaida shi ya saka masu albarka.
Kicin suka shiga suka iske Hindu ta kammala haɗa kayan karin safe.
Suka taimaka wajen jerawa saman dinning table.
  Wani sassayan ƙamshin Oud Wood tare da Voyage D  ne ya doso kicin ɗin.
"Yaya ARK goodmorning".
"Morning". Ya faɗa tare da dauke kansa.
"Ina kwana?".
"Lafiya". Ya faɗa a gajarce.
"Inna Hindu ki haɗa mun kunun gyaɗa kawai shi nake son sha".
"Toh yallaɓai".
Ya fita daga kicin ɗin ya na taku cikin isa da ƙasaita.
"Yaya ya cika tsurfa wallahi. Da ni ce ke Inna Hindu bazan yi ba".
"Rufa man asiri uwar ɗakina".
"Layla daga gani faɗa gare shi koh? Ni har na fara tsoronshi be da sakin fuska".
"Ai Yaya ARK gwani ne wajen faɗa idan ka shiga gonarsa,amma idan kayi takatsan-tsan ba abinda zai haɗa ka da shi,ina ma ya zauna bare har ka ganshi yanzu ma da aikinsu ya fito shikenan mun huta".
 
   ***
Ƙarar cokula kawai ka ke ji,babu mai magana.
Sai da suka kammala karin safensu.
"Mami kin sami twins fa".
"kaga ƴan matana ɗagwas-ɗagwas Sadeeq .Taimakona za ka yi ka fita da su ga list nan na rubuta na duk abinda ake buƙata".
"Toh Mami ba matsala".
"Kayi amfani da credit card ɗina ayi duk abinda ya kamata".
"In Shaa Allah Daddy. Allah shi ƙara buɗi".
Suka amsa da "Amin".

MADUBI Where stories live. Discover now