MADUBI
AYEESH CHUCHUBABI NA SHA TAKWAS
I dedicated this chapter to my baby doll Amaaa Princess and Hafsat Ermum Happy birthday 🎂 in advance. Age with grace deariez ❤.
Sannan ina mika sakon gaisuwa ga uwa Yabi Babba Kaita bisa rasuwar da aka yi, Allah ya ji kan musulmi ya bada hakurin rashin da aka yi.WUYA MAKARANTAR KARE
"Na so a ce yarinyar nan gida ta je wanka Salisu, amma tunda ka ƙeƙashe kunnuwanka shi kenan, amma dai ka dawo da ita nan gidan. Kada a bar ɗiyar mutane ita kadai a gida babu mai kula haihuwa yau ko gobe".
"Sai dai ta dawo nan gidan".
"Yauwa hakan ma yayi, ina so kafin ka tafi ka sayo duk abinda ya kamata ka saya".
"Ba matsala".
Daga nan ya sa kai ya fita daga gidan.
Gidansa ya wuce kai tsaye.
Kwance take a saman ledar falon, ba ta ji sallamarsa ba, sai jin naushi tayi ta gefen cikinta.
Firgigit ta tashi, wani raɗaɗi ya farma gefen mararta.
"Washhhh".
"Dalla can rufe man baki, dama jira kike daga yin abu sau daya sai ciki, ni ban shirya zama uba ba. Dan haka ina ƙara ja ma ki kunne ki nemi uban cikin jikinki. Kayan haihuwa kuma kisan yanda za ki yi. Ki kuma shirya kayanki can babban gida za ki haihu".
Hawaye ne suka wanke fuskarta. Ga radadin da take ji a kasan mararta.
Da kyar ta dafa kujera ta miƙe tsaye, a daddafe ta shirya kayanta.* * *
BAKORI
"Halima ki kira min Ibrahim ya zo?".
"Toh Innani, sannu".
Ta gyada kai da kyar alamun tana jin jiki.
Gwaggo ta fita daga dakin zuwa kiran Malam.
"Innani sannu da jiki?".
"Yauwa, dama so nake in ce maka ka dawo da Amma gida tunda ance ciki gareta ta kusa haihuwa ta zo gida wanka. Mafarkinta nayi ".
" Ai mijin ya zo rannan gidan nan, yana ma sauri ne Shiyasa be shigo ba. Can gidansu Amma za ta yi wanka har ta koma ma".
"Ba fa zan yarda ba, ina son ganin Amma. Nan kuma za tayi wanka".
"Innani kiyi hakuri, kinga yanzu banda iko da ita, ba hurumina bane. Zan tuntube su inji idan ma Halima za ta je can Karofin ayi magana shi kenan".
"Ka ƙokarta ka dawo man da Ammah".
"Idan Allah ya so Innani".A ranshi yake ayyana abubuwa da dama, bayan fitowarshi daga dakin.
"Idan ba rigimar Innani ta yaya miji yazo ya fada cewa Ammah ta dawo gida wanka, bayan ma duk ita ta assasa auren Ammah".
Jijjiga kai ya yi, ya fice daga cikin gidan.
Gwaggo dake tankaɗe suna fira da Inna ta ce "na so a ce Ammah gida ta zo wanka, amma yaran zamani su kwakwafe ba inda matansu za su".
" Ai na san za ta samu kulawa sosai ma a can".
"Ba'a shedar mutum Mairo, duk yanda za a ba ta kulawa be kai ga nan ba. Amma ba yanda za muyi sai hakuri. Ita ma dole ta yi biyayya ga mijinta".
"Hakane kuwa, ai aljanna ta ke nema".
"Allah dai shi sauke ta lafiya ".
" Amin Gwaggo ".
Nan suka cigaba da hirarsu akan lamuran duniya.KAROFI
09:23am
" Hasbunallahu wa ni'imal wakeel. Bayana! Cikina ciwo suke. Zan mutu,Wayyo Allah na".
Zufa ce take ta ketowa ta goshinta.
"Lafiya Ammah?".
"Inna cikina".
"Haihuwa ce ta taho. Bari in dauko maganin da unguwar zoma ta kawo jiya dama na jiƙa shi".
Nishi take sama-sama, tana ta ambaton sunan Allah.
"Ungo kurɓa nan ki kuskure bakinki".
Da kyar ta iya kurba ruwan tana ta murƙusu ta na juye-juye.
Durƙusawa tayi tare da yin guho, ba'a yi minti biyu ba ta kwanta.
Duk ta fita hayyacinta cikin lokaci ƙanƙani.
Hajiya ce ta shigo da kasko, ta kwanto wani ƙullin magani daga zaninta ta barbada, hayaƙi ya cika ɗakin.
"Ita shaƙar hayaƙin nan a samu faya ta fashe ma".12:46pm
"Wayyo Hajiya ruwa na ta zuba a jikina". Ta faɗa muryarta a dishe da kyar take fita dan wahala.
"Sannu Ammah faya ce ta fashe".
"Washhhh".
"Daure dai yanzu za ki haihu da yardar Allah ".
" Inna dan Allah mu tafi asibiti".
"Asibiti? Ai a tarihin gidan nan kowa gida yake haihuwa lafiya sumul, ba abin da asibiti za su nuna mana nan wajen. Duk wasu magunguna da ya kamata unguwar zoma ta hada ma ki. Kar ki kuskura in kara jin asibitin nan".
WASHEGARI
"Ikon Allah tun jiya ake abu daya unguwar zoma".
"anya kuwa Hajiya kunyi amfani da magungunan da na baku dai-dai?".
"Duk yanda kika ce haka aka yi".
"Yarinyar ta matukar galabaita, amma ku fita mu gani yanzu za ta haihu".
Suna fita dakin unguwar zoma ta fara daddana cikin Ammah gefe-gefe.
Wata irin ƙara Ammah ta yi, wanda ke hade da ƙara.
"Daure kin ji yar nan".
***
01:20pm
Kukan jariri ne ya karaɗe ɗakin.
"Madallah ta sauka".
"Ayyiririyiriyiri". Fadin unguwar zoma. Ammah da ke kwance gefe ko yatsanta ba ta iya ɗagawa saboda tsantsar wahalar da ta ci.
"Unguwar zoma ita mai jegon fa, naga duk tayi yaushi sosai?".
"Za ta warware da ta yi wanka ta ci abinci. Yanzu dai a gyara jaririn tukunna".
Ta na nan kwance har gab da maghriba, duk da ta yi wankan ba ta jin dadin jikinta. Ga ruwan nono be zo ba.
Jariri na ta kuka, ganin Inna ta fita ta rarrafa a hankali ta kalli fuskar ɗanta, wanda ke fari sol, har wani sirƙin ja-ja-ja-ja ke gare shi tamkar Balarabe.
Addu'a ta tofe shi da shi, sannan ta koma makwancinta. Tana jin ƙaunar ɗanta na ratsata."Ikon Allah ashe dai ina da rabon ganin gudan jininka Salisu".
"Uhmmm aikam dai gashi nan kin gani".
"Ai sak! Kai ya dauko hancin Ammah kadai gareshi. Shiga ciki ka ga kyautar Allah".
Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya shiga ɗakin, Ammah na kusa ta jaririn ta kura ma sa idanu.
"Na fada ma ki ki nemo ma ɗanki uba".
Ko kallon jaririn be yi ba, bare a sa ran zai dauke sa ya masa khudbah kamar yanda kowane uba ke yi.
Hawaye suka hau zarya a saman fuskar Ammah.
"Salisu idan ka fito ka aika gidansu Ammah ta sauka".
"Toh Hajiya".
Daga haka ya fito daga ɗakin.
BAKORI
"Ammah fa ta sauka lafiya ta sami ɗa namiji". Faɗin Baban Ammah a yayin da ya shigo gidan.
"Alhamdulillahi, barkanmu da samun ƙaruwa nayi sabon miji".
"Ba ki da dama Halima, yanzu dai gobe da safe sai kuje Tunda maraice tayi ".
" Allah shi kai mu lafiya ".
Bakin Gwaggo yaƙi rufuwa.
Inna dai murmushi kawai take tana ta hamdala.
" Naga Ammah da jariri, yar kurut da ita. Anya zan iya bacci kuwa?".
"Gwaggo kenan!".
* * *
"Innani dan Allah ki yi hakuri ki bari da kaina zan sa mota ta kai ki, kinga baki da cikakkiyar lafiya".
"Miyasa tun jiya ba'a faɗa mun ba, sai bayan sun tafi?".
"Ban son hankalinki ya tashi ne, lafiya lau take".
"Zan je suna dai, inga jinin Ammah. Allah sarki Halima ko tana wace duniya?".
"Ibrahim miyasa ba ka bani shawarar rungumar Halima ba a lokacin da tafi bukatarmu?".
"Innani kiyi shiru, abin da ya wuce ya wuce. Tana nan cikin kwanciyar hankali".
"Allah kada ya amshi rayuwata banyi tozali da Halima ba".
"Da yarda Allah za mu gana Innani".
Ya share ma ta hawayenta,tare da gyara ma ta kwanciya.
KAROFI
Gidan ya cika da yan gidansu Ammah tare da mahaifiyar Sa'a da kannenta.
"Sannu Ammah wannan ƙaton jinjiri tubarkallah da kika haiho mai kama da ubansa". Faɗin Mamar Sa'a.
"Kin kuwa kira wannan yarinyar kirkin Ammah?".
"Na manta shaf Gwaggo, bari in kira ta".
Wayar har ta gama ƙara ba'a dauka ba. Sai bayan wasu mintuna aka kira Ammah.
"Wa alaikumus Salam".
"Eh Aunty na sauka".
"Eh a can".
"A'a babu abin da ke damuna".
"Toh nagode kwarai. Allah shi saka da alheri ".
" A gaida Ajwad".
"Yayi ƙani kam".
"Eh sun zo gasu nan ma".
"Toh zasu ji".
Ta dan murmusa.
"Gwaggo wai za ta aiko da sako ta tasha kafin suna".
"Yarinyar nan dai na ƙaunarki, Allah shi biyata da mafificin alheri".
"Amin".
"yanzu dai sha kunun nan a samu ruwan nonon nan ya ciko sosai, damma angon nawa na da hakuri".Bayan la'asar su Inna suka tafi, aka bar Gwaggo da Ammah.
***
"Gwaggo sanyi ake ki hau gadon ki kwanta".
"A'a yi kwanciyarki, miƙo man gudan bargon can in lulluba".
Ta miƙa ma ta bargon ta kwanta.
BAYAN KWANA BIYU
"Ammah lallai yarinyar nan Allah ne ya hada ku. Irin wannan kaya haka cike da akwati harda kuɗi fa".
"Har mamakin halin Aunty na ke, daban take a cikin masu kuɗi. Kullum sai na ma ta addu'a".
"Ai ta cancanci hakan".
"Ke da kin gani kin san ma su tsada ne".
"Eh wallahi ".
" Yauwa Ammah wai zaurin mi nake ji ne cikin ɗakin nan? Dazu da zan dauki yaro yanda ki san an baza taki a kan gadon nan. Kuna ƙoƙari".
"Ka.. Ka.. Katifar ce Gwaggo, haka nan nake kwanciya kanta, na san Inna ma ba ta sani ba".
"Sai kuma kiyi shiru kiyi ta cutar kan ki don wauta?".
Tayi shiru kanta a ƙasa ba tace komi ba.
RANAR SUNA
Yaro yaci sunan mahaifin Salisu (Ahmad) ana kiransa da Khalifa.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Ammah mi zan gani haka?".
"Wallahi Allah Gwaggo tun ranar da na haihu nake yin haka. Nima ban san ina yi ba. Tsoro nake kar ku min fada".
Ta fashe da kuka.This is just the beginning!
Assalamu Alaikum my people.
Hope you're all doing well? I guess MashaaAllah.
Please don't forget to
Vote
Comment
Share
RecommendDon't hesitate to drop your views and suggestions it really makes me feel like dancing 🎶.
Ku cigaba da hakuri da ni, i know the chapters are kinda boring, sure! That's how MADUBI messages are written...
Life is always full of twist, not all time you taste the sweetness of life, it compromises both sweet, sour and bitterness.
Someone out there is struggling in life like Ammah.
They're many out there in our cities, villages and town like her.
Always be a strung women ♀, enjoy and appreciate what you've in the present.
Alhamdulillah!
ayeeshasadeeq2010@gmail.com
www.chuchungaye.wordpress.com
Masaa'al khair yaa habeebataini. Lol 😁
Don't mind my Arabic.
Ok! Cheer up guys 🍻
Allah hafeez
C you soonest.AYEESH CHUCHU
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...