***
"Wai Ammah mi ki ke ji wajen wannan zanen ne? Tun ɗazu fa naga kina ta yi abu yaki ci yaki cinyewa".
Murmushi ta yi ta ce "Gwaggo ba ki san yanda nike son yin zanen nan ba, yana dauke mun kewar rashin zuwa makarantar da ba na yi".
Dafa kanta Gwaggo ta yi,tausayin Ammah ya kama ta "Ba komi Ammah wata rana sai labari, ke dai ki dage da karatun islamiyyar da ki ke yi Allah zai taimake ki".
"In Shaa Allahu Gwaggo zan dage, amma ina jin haushin ganin an bar su Mubarak na zuwa makarantar boko amma ni banda ni, har Abdullahi dan karami da shi Baba yasa shi. Wai Gwaggo dama ita mace ba ta da 'yancin zuwa makaranta ne?".Kalar idanunta zuka canza launi, alamar hawaye ke son gangarowa.
Gwaggo ta kalleta tana mamakin kalaman Ammah.
"Sau nawa zan faɗa ma ki ki daina maimaita maganar nan Ammah, kin riga da kin san cewa Malam bai son karatunki, ki hakura mana idan Allah yasa kina da rabon yi ko ba jima ko ba dade sai kin yi karatun bokon nan".
Kai ta gyada alamar gamsuwa da bayanin Gwaggo, sannan ta cigaba da zanen da take yi, wanda take jin shi har cikin ranta.KARFE 01:56PM
Da gudu ya shigo gidan yana haki. Yaro ne da bai wuce shekara hudu ba.
"Lafiyar ka kuwa Abdullahi kadan ya hana baka fado kaina ba".
Cikin harshensa da bai gama warware ba ya ce "Yusuf ne ya biyo da gudu dan na siya caras (carrot) ban ba shi ba Yaya Ammah".
Da sallama su ka shigo gidan, Ammah ta ce "Kai dai Yusuf an yi babban kobo yanzu saboda karas din Naira biyar ka biyo yaron nan, da ya ji ciwo fa?".
"Yaya Ammah kuɗin Yaya Mubarak ne fa shi ne na ce ya sammani karas ɗin sai ya rugo da gudu".
"Toh daga yau ka rinka hakuri ka ga ai kai ne yayansa ne".
Ya daga kai.
"Toh maza ku wuce Gwaggo na ɗaki ku gaidata, Inna taje cikin gari ta dawo".
Ba musu su ka bi umarninta, dakin Gwaggo suka nufa su ka gaidata.
Randar da ke gefen rijiya Mubarak ya bude ya zuba masu ruwa a buta suka yi alwala. Sun idar da sallah Gwaggo ta zuba ma su abincinsu, cikin tire (tray) mai faɗi, sun wanke hannayensu su ka fara ci tare dukkansu har da Ammah.
Hakan al'adarsu ce, tare su ke cin abinci.
Su na gama ci,kwanciya su ka yi kafin lokacin sallar la'asar ya yi su yi shirin islamiyya.
Ammah dakin Gwaggo ta koma ta kwanta, Gwaggo na kallonta ta na jin kaunar Ammah tamkar ita ta haifeta.***
KARFE 03:30PM
"Ammah tashi lokacin sallar la'asar ya karato".
Salati tayi haɗe da mika, sannan ta tashi ta nufi dakin Inna dan ta taɗa su Mubarak, turus ta tsaya bakin kofar ganin Inna a cikin ɗakin, za ta juya ta tafi, ta tsinkayi murnar Innar na cewa "ke ya aka yi ne?".
"Da ma su Mubarak na zo tadawa su shirya lokacin sallah ya kusa ".
Innar ba ta kara cewa komi ba, ta tada su Mubarak.
Alwala Ammah tayi, sannan ta sa kayan islamiyyarta.
Su Mubarak na dawowa daga masallaci suka fita.
"Mubarak mu biya gidan su Sa'a, na san ta shirya ita ma".
Gidansu Sa'a su ka nufa, da sallama su ka shiga gidan. Mahaifiyar Sa'a Inna Habiba ta amsa masu.
Su ka gaidata.
"Inna ina Sa'a?" fadin Ammah.
"ai kuwa yanzun nan ta fita za ta kai dinkunan makarantarta daga nan ta wuce islamiyya".
"Inna ta samu makarantar kwanan ne?".
"Eh Ammah ta samu wannan makarantar kwanan da ke Sandamu Daura".
Ammah ta zaro idanu "Wai Allah wannan garin mai nisa inda 'yar gidansu Jamila ke karatu".
"Eh can ne".
"Allah shi basu sa'a, ya kuma sanya alheri".
"Amin Halimatu Ammah".
Murmushi ta yi, su ka tafi islamiyyar ita da kannanta.
Farin ciki ta ke ta ji, kamar Ita ta samu makarantar.
Suna zuwa islamiyyar har an fara taren 'yan makara,jikinta ya fara kyarma. Ba abinda ta tsana irin bulala shiyasa sam ba ta yarda ta makara.
Tun kafin azo kanta ta fara kuka.
Can ta ji wasu yan mata na kus-kus.
"Shatu duba ki ga wannan mai kama da baturen, sabon Ameer da yazo kwanannan, naji ance wani aiki ya zo yi, jikan Hajiya Zainab ne".Mukhtar da ke tsaye yana kallon Ammah da ke ta tsalle da hawaye tun kafin a bata na ta kason, ya yi murmushi.
Ganin shi na biyu kenan da ganin Yarinyar, amma ta na burge shi, duk cikin sa'ointa ba wanda ya kai ta tsabta.
A hankali ya tako gaban su, ya kalli Amirar islamiyyar (shugabar dalibai mata) yace "Asma'u sauran matan da su ka rage ki sa su share harabar makarantar nan, ga datti nan ko ta ina".
Ba dan ranta ya so ba, ta kallesu "ku wuce ofishin Malam Isah ku dauko tsintsiya ku share harabar".
Wani farinciki ya sauka akan fuskar Ammah, har da daga hannayenta sama ta furta "Alhamdulillahi".
Da gudu suka bar wajen, Mukhtar ya bi su da kallo.
Asma'u ta karaso wajen da Mukhtar ke jingine jikin bango ta ce "Ameer babban yaro".
Murmushi ya yi tare da shafa sumar kan shi ya ce "Asma'u babbar yarinya, wuce mu tafi aji na san yanzu haka Mal. Abu ya shiga ajin".
Ajin 'yan hadda su ka shiga.
Mukhtar ya wuce wajen da' yan uwansa maza da ke zaune, Asma'u kuma wajen mata.
Tana zama Lubabatu ta yi magana kasa-kasa ta ce "Kinga yanda ku ka yi kyau ke da mutuminki da kuka shigo".
Asma'u tayi far da ido "Kawata yau dai ya bayyana mun sirrin zuciyarshi".
"kai haba?".
"Wallahi koh, yanda nike sonshi, haka shi ma yake kaunata".
"Lallai kin dace, Mukhtar ai one in town ne, yaro mai jini a jika".
"bari kawata ni na san na dace".
"Asma'u kina ganin Abbanki zai bari ki auri Mukhtaar kuwa? Kin san fa akwai alkawarin Sulaiman akanki, sannan SS2 fa kike, ko gama secondary school ba ki yi ba".
"Ke dalla kyale ni, ke kan ki kin san abinda nike so shi Mama za ta sa amin, ni idan har na samu Mukhtar ba wani karatun da zanyi".
"Lallai Asma'u, kin san dai da kyar Mukhtar zai yi aure kusa-kusa, mutumin da duka aji uku fa aka ce yake a UMYUK, IT ko minene ya zo yi a, asibitin bayan gari, kuma yanda na ji ance 'yan gidansu' yan boko ne, ke karan kanki kin sani kaf ya'yan gidan Haj. Zainab babu wanda be yi karatun boko ba, iyayensu kenan bare kuma jikokin 'yan na gada".
"Zan iya komi dan...".
Ba ta idasa maganarta ba Malam Abu ya shigo ajin, suka fara karatun TAJWEED.Here we go.. Show me some love by clicking on the votes and comment icon ..
Anyway.. I do lobiyu guys.
Remain blessed
Shatu KwankiyalPlease for any shawara or gyara just click on the ff social media platforms, I'll respond quickly.
Sankiyu beri moc fo za lov an kiya.
chuchungaye.wordpress.com
Wattpad @ayeesh_chuchu
Facebook Ayeesh Chuchu
Twitter @ayeesh_chuchu
IG @ayeesh_chuchu
email ayeeshasadeeq2010@gmail.com
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...