CIKAR BURI

2.1K 168 37
                                    

MADUBI
©AYEESH CHUCHU
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR

"I could make you happy, make your dreams come true. Nothing that I wouldn't do. Go to the ends of the earth for you to make you feel my love."
~ Bob Dylan (Make You Feel My Love)

To list your names on this page, you deserve more than it. Your names are priceless. I'll keep praying for you Jazaakumullahu khair. May Allah blessed you all, grant you the best desires of your hearts. I means you my lovie-dovies.

CIKAR BURI

"Wannan shopping haka Ya MK? It's too much. Ina za ka kai wadannan kayan mata?".
"Yusie why all this questions?".
"Na ga kayan ne ba za su yi ma Momi ba. Kuma suna da yawa".
"Oooh! Sai na ce ma ki banda wadanda zamma tsaraba koh?".
"A'a ba haka nake nufi ba". Ta tura baki ta miƙe.
"C'mon girl! Kar kiyi fushi da Ya MK. You know you're my favorite sis right?".
Murmushi ta yi.
"Ya MK! Allah kai kamar zuma ka ke. Wata ran dadi wata ran harbi ".
" Kin san mi?".
"A'a sai ka faɗa".
"I'll surely miss you with your stubbornness, care and company".
"Ni Allah kamar na bi ka, na gaji da garin nan".
"Ke! Ba ki san yanda na ke ji ba. Shekara hudu da wasu watanni I'm a way from my family, from my motherland and the precious one. Haba! Nayi kokari. Idan da su Momi ba su zuwa ban san ya zan yi ba".
"Ya MK kar ka sani kuka. Bari in taya ka haɗa kayanka".
Tare suka haɗa kayan MK, duk wani abu da yake bukata.

***
Cologne Bonn Airport
Cologne Airport babban filin jirgin sama dake a tsakiyar Cologne da Bonn. Babban filin jirgin sama ne mai dimbin tarihi a kasar Jamus.
"MK zan yi kewarka. Take care".
"Yusie ba za ki zo mu yi bankwana ba?".
Kuka take fuskarta ta yi jajir, tana ta shashsheƙa.
"Ka kyale Rigimammiyar nan. Yau dai za mu sha bori ".
Murmushi ya yi tare da daga masu hannu ganin fasinjoji sun fara shiga.
Hawaye su ka zubo ma sa, yayi saurin sa bayan hannunsa ya goge su.
***
FILIN JIRGIN SAMA NA YAR'ADUA
KATSINAN DIKKO

Rungume yake jikin mahaifinsa Dakta Usman.
" I missed you Dad".
"We missed you more".
Ya kalli Mahaifiyarsa da ƴanuwansa da ke zagaye da shi, ya ji wani irin farinciki mara misaltuwa a cikin ruhinsa.
***
"Wai MK baccin lafiya ya ke haka?".
"Dakta kenan! Dan gwal fa ya dawo. Ki kyale shi ya huta daga tafiya ya dawo".
"Kawai ina son ya zauna muyi fira sosai".
"Mukhtar ya matukar yin ƙokari, result dinsa ya burge ni matuka. 1st class a Educational Sociology ai abin alfahari ne".
"I'm proud to my son".

Kwana biyu MK yayi yana hutawa, be ji ko'ina ba. Sai da Momi ta addabeshi sannan ya shirya zuwa gidajen ƴan uwansa.
Ya fito cikin shigar ƙananan kaya kalar navy blue da blue chinos trouser samfurin Under Armour. Sumar kansa ta kwanta luf! Kamar yasa hair relaxer. Sai kyallin hair spray yake.
Momi ta kalli MK "Wow! You look handsome my son".
"Thank you Mum. Qila gobe in je Bakori inga Hajiya".
"Da ka kyauta kam. Ta yi kewarka".
Daga nan ya fita daga gidan.

BAKORI
Tunda ya shigo garin zuciyarsa ke ta bugawa. Gaban family house ɗinsu yayi parking.
Ya shiga gidan da sallama.
"Wa zan gani ni ƴasu? Ashe dama zan ƙara sa ka a ido Muntari".
"Kai Hajiya wai Muntari kin ji matsalata da ke wallahi".
"Dan jakar uba ai fa ka dawo".
Nan kuma suka hau gaisawa.
Sun dade suna firar yaushe gamo.
Har ya gangaro kan batun da yake son yi ma ta.
"Hajiya ina labarin Ammah?".
"Wacece haka kuma?".
Nan yai ta ma ta kwatance har ta gane.
"Ai ina ga yanzu kila tayi haihuwa ta biyu. Don yaronta na farko zayyi shekara hudu yanzu".
"Haihuwa yar wannan yarinyar?".
"Tsaya nan. Sai dai ka ji jikokinta. Duk bamu kai ta ba akai mana aure kuma ba abinda ya same mu".
Jikinsa ne ya hau kyarma, zuciyarsa ta jagule.
"Ashe mafarki na ba zai tabbata ba. Ina mafarkin zanga Ammah da na dawo. Hajiya ki taimake ni".
"Ikon Allah! Wai har yanzu son yarinyar nan ka ke? Matar mutanen Muntari! Wallahi ka ji tsoron Allah tun be yi fushi da kai ba. Ina kai ina mafarkin matar wani. Wato yahudancin da ka koyo kenan daga turan? Shiyasa fa banga amfanin fita ƙasashen nan ba. Su iyayen na ku ai duk a ƙasar nan suka yi nasu bokon".
Ta yi tsaki,tare da miƙewa tsaye.
"Hajiya ki tsaya ki ji mana. Ni fa ban san tayi aure ba. Kin fassara ni".
"Toh ai yanzu ka ji ai".
"Kai Hajiya na zo muyi fira duk kin kashe min jiki".
"Soyayya dai ta kashe ka".
Nan kuma suka cigaba da hira, kamar wani abu be faru ba.
Da niyyar kwana ya zo amma ji yake ba zai iya kwana ba, a ranar ya juya zuwa Katsina jikin shi a mace.
Momi tayi tambayar duniyar nan ya ce ba komi. Dole ta haƙura ta kyale shi.

MADUBI Where stories live. Discover now