CUTA BA MUTUWA BA

2.3K 190 74
                                    

MADUBI
        AYEESH CHUCHU
BABI NA ASHIRIN DA DAYA

     I dedicated this chapter to Aunty Sis, Gwaggo Kuluwa (Maijidda Musa), Aunty Dalal, Lubie Maitafsir and Dijah Shariff (Aminis). Thank you all for your support and love 😍. I'm forever grateful.

CUTA BA MUTUWA BA

  "A'a sannunku da zuwa". Fadin Inna
Ammah da ke ta sharar bacci, hayaninyar gaisuwar jama'ar ɗakin ya farkar da ita.
  Jin ta cikin lema ya sa ta furta "Inna bari in tashi a cire zanin nan ya jiƙe".
"Sannu Ammah".
"Yauwa Gwaggo".
"Ba ki ga anyi baƙi ba?".
Sannan ta kai dubanta ga mutanen da ke kewaye da gadonta.
"Laaa! Aunty Ayeeesha ". Ta faɗa idanunta a waje.
" Ammah". Ta matso kusa da ita tare da kama hannayenta.
"Kina cikin irin wannan lalura ki kasa faɗi man Ammah, sau nawa muna waya?".
"Ba ni son in daura ma ki hidimar da ba ta ki ba".
"Ba dai ki kyauta ba".
"Su waye wadannan?".
"Yan uwanki ne Ammah".
"Yan uwana?".
Ta girgiza ma ta kai. Cikin sanyin murya ta gaishe da su.
Mami da ke tsaye tausayin Ammah ya gama ratsata.
"Ba mu da lokacin ɓatawa fa, mu je mu amshi sallamarta a wuce da ita".
  Kan Inna da Ammah duk a cunkushe, kowannensu na buƙatar ƙarin bayani.
                      * * *
Da dare suna zaune, duk firarsu akan yadda rayuwarsu ta kasance su ke yi.
"Wai ina mazajen nawa ne?"
"Ai sun tafi motel din da za su kwana".
"Au toh! Ita wannan miskilar matar ba ta mqgana ne?".
"Innani ai Laila ba ta da saurin sabo shiyasa".
"Ai kuwa nan za ki bar ta wajena".
Laila da ke kwance tayi matashi da ƙafar Mami tayi saurin tashi.
"Lallai ma tsohuwar nan".
Ta shige ɗakin Gwaggo, suka yi dariya.
  "Innani gobe fa zamu tafi saboda lalurar Ammah, Hashim ya kira likita abokin karatunshi da ke aiki a asibitin Murtala, da yake akwai sashin da aka ware da ake ma masu yoyon fitsari aiki. Toh ya ce gobe kafin mu iso zai mana duk wani taimako da ya kamata".
  "Toh hakan ma yayi, ba dan Amma da kin kwana biyu nan. Amma ya za a yi da Khalifa yaron da bai isa yaye ba?".
Ta sa gefen zaninta ta share hawayenta.
"Innani kiyi hakuri, ki bi ni mu tafi kawai. Gaskiya yanayin da Ammah ke ciki lafiyarta ta fi komi, yara nawa mahaifiyarsu ke rasuwa ranar da ta haihu ko nonon uwar ma ba su sha ba. Madara za a riƙa ba shi, gobe idan Allah ya kai mu Gwaggo sai ta kai shi asibiti a rubuta masa madarar da ta dace da shi".
Ta girgiza kai.
"A'a na fi son zama nan. Takardar sakin Ammah kawai nake so a amso ma ta daga wajen azzalumin mijin nan da ya so kashe mun Ammata".
"In Shaa Allah ba matsala, dole ya bada takardar shaidar sakinta. Zan dawo ko da sati mai zuwa ne".
"Ai Mami kotu na so a maka dan banzan wallahi". Fadin Ayeesha da ke ba Ajwad tea.
"Tunda dai zuri'a ta haɗa a kyale shi Allah na nan. Ni samun lafiyar Ammah yafi damuna". Fadin Gwaggo.
"In Shaa Allah za ta warke ko Hashim zai taimaka tun da kwararren likitan mata ne (gynecologist)".
"Madallah! Ƴaƴanki dai kowanne na da madafa. Dadin ilimin kenan wallahi. Abin da nai ta nusar da Malam kenan, amma ina Allah be yi ba. Komi mukaddari ne, da yanzu Amma na nan tana karatu ita ma kamar sauran sa'anninta. Kinga ƙawarta Sa'a na nan aji huɗu fa".
"Komi rabo ne Gwaggo".
       
                     * * *
Washegari tun misalin bakwai na safe har sun shirya. Da kyar suka lallashi Innani da ke ta kuka. Mami da Alhaji Kabir suka cika Malam Ibrahim da abubuwan arziki.
"Gwaggo ga kuɗin da na ce a kai Khalifa asibiti a duba madarar da ta dace da shi".
Ta ciro bandir ɗin ƴan Naira ɗari ta miƙa ma Gwaggo.
  Amma ta rungume Gwaggo ta na kuka. Ammah kai duban ta ga Khalifa da ke jikin Inna a lafe, ba ta san lokacin da ta fashe da kuka.
Tunanin yanda za ta bar jariri kamar sa take, tana ƙaunar ɗanta. Kunyar ta ke ji ta yi magana.
  A haka suka shiga mota bayan an shimfiɗa leda da tulin zannuwa a saman ledar sannan Ammah ta zauna.
  Hawaye suka tsiyayo ma Laila ta yi saurin tasa hannu ta goge.
Ta shiga gaban motar, Ayeesha na baya ita da Ammah.
Ya Hashim ya ja mota, Amma na ta daga ma su Gwaggo hannu har motar ta bace.

MADUBI Where stories live. Discover now