AURE YAƘIN MATA

1.9K 185 14
                                    

MADUBI
©AYEESH CHUCHU

BABI NA SHA UKU

I dedicated this chappy to all my fans.
AURE YAƘIN MATA

  Kiran sallar assalatu ya tashe ta daga baccin da take, da kyar ta iya motsa jikinta da yayi ma ta tsami kamar an niƙa ma ta na jaki. A hankali ta yi miƙe tare da motsa bakinta alamar tana addu'a.
  Tagumi tayi da hannunta rashin sanin ina ta dosa.
Labule ta daga, minshari da gurnanin da ke fita zai tabbatar da cewa baccinsa yake cikin kwanciyar hankali. Kamar an tsikareta ta yi saurin ja da baya ta koma falon.
  Ganin lokacin sallah na ƙaratowa yasa tayi wuf ta isa bakin ƙofa ta zare sakatar da aka sa.
Ƙafarta ta sauka akan dandamali, ta kai duba ga sararin samaniya inda taurari ke ta walƙiya.
  Carar da zakara yayi ya fargar da ita, ta dawo duniyar da take ciki.
  Ɓakar randa ta roba ta hanga ta nufi wajen, ga mamakinta cike take taf! Da ruwa ga kofi a samanta da buta. Ta tsiyaya ruwa ta hau dube-duben makewayi (toilet) dan ta rage mararta.                            ***
Tana zaune tana lazimi har rana ta fito,gurnanin Salisu be daina fitowa . Da kyar ta yakici zuciyarta ta nufi ɗakin. Ta yi sakato tana tunanin yanda za ta tada shi yayi sallah.
Mafeci (hand-fan) da ta gani a ƙasa ta dauka tare da zungurin ƙafarsa.
"Ka tashi lokacin sallah ya wuce fa".
Ta ƙara zungurinsa.
Ya buɗe idanunsa, suka sauka a kan na ta. Ya sa ƙafa zai harbeta, sai kuma ya tsaya.
"Ke dalla Malama daga yau kada ki kuskura ki ƙara tada ni ina tsakiyar baccina, idan ba haka ba jikinki zai gaya ma ki. Fin Allah kika fini ne ko kuwa?".
"Ka yi haƙuri". Shi ne furucin da ya fito daga bakinta.
Falo ta koma ta zauna, hannayenta sagale a kumatunta, ba za to ba tsammani hawaye su ka fara zarya a saman kumatunta.
  Sai da tayi kuka mai isarta, ta ga lokaci ya ja har ƙarfe tara ta kusa.
Har lokacin Salisu be tashi ba. Buɗe kofa tayi hasken rana ya dallare ma ta idanu.
Ta yi duba da tsakar gidan da ba wani girma gareshi ba. Daga can gefe aka yi makewayi da banɗaki (toilet & bathroom). Sai madafi (kitchen) da suke kallon juna. Daga bakin ƙofa an girke buhun gawayi (charcoal), ta buɗe madafin, tarkacen kwanoni ne da kuloli, sai risho (kerosene stove) dake cikin kwalinsa.
  Ƙuji cikin yayi tare da bada sautin yamutsawar halittun da ke cikin ciki.
  Dakinta ta dawo, wayam! Ba ta ga Salisu ba. Hakan ya ba ta damar cire kayan jikinta, ta daura zanin tare da saka hijabi ta tafi wanka.
  Cikin kayan da aka taho ma ta dasu tasa wata atamfa mai kalar kore shar! (green) da kalar ruwan dorawa (yellow), sai ratsin fari da baƙi a jiki. Atamfar ta ƙara fito da ita, dan dinkin ya zauna das! A jikinta, ta murza hoda tare da man laɓe (lip gloss) a bakinta, sai kwalli da ta zizara.
Duk da ba wata kwalliya ta yi ba, ta a zo a gani tayi kyau.
  Jin takun tafiya yasa ta rude ta na neman hijabi ko mayafi tasa. Shigowarsa ɗakin ya ƙara rudar da ita, ta daburce. Ya bita da kallon ƙurilla.
Sai kuma ya buga tsaki, ya fita daga dakin.
  "Ke! Zo ki kai man ruwan wanka bayi. Daga yau ban dauke ma ki kai mani ruwan wanka banɗaki ba".
Ta gyada kai, ta nufi bakin randa ta ɗebi ruwa ta zuba a bokiti ta kai masa har bayin.
 
                         ***
BAYAN WATA HUDU
"Zan yi kewarki Ammah, jibi zan koma makaranta. Shiyasa na zo dan mu yi bankwana.".
Ta fashe da kuka "Aiko na gode. Kinga ba kowa gidan sai ni kadai kadaici na damu na. Yanzu Sa'a shikenan ba zan yi karatun ba?".
"Kar ki fidda rai da tsammani Ammah. Mata nawa ne ke karatu a gidan mazajensu kuma kiga sun zama ababen koyi (role models) a cikin al'umma saboda kwazonsu. Ke ma ina da yaƙinin cewa za ki kai ga cimma burinki".
"Allah ya amshi addu'arki Sa'a. Ki dage kiyi karatunki Tunda kin samu dama".
"In Shaa Allahu. Ke dai ki cigaba da kai kukanki wajen Allah. Gwaggo ma tace in kara ja ma ki kunne kan haka".
Hawaye su ka gangaro ma ta, haɗe da murmushi "Allah sarki Gwaggota. Na yi kewarta sosai".
  "Dole! Shiyasa kika bi ki ka rame. Ki kwantar da hankalinki Ammah, dama ya ya lafiyar kura".
"Uhmmm".
"Ni dai tashi mu shiga kicin in ci girkin amaryar Salisu".
"Ummm Ummmmm! Dama fura zance in aika a sayo ma ki, tun da zafi ake. Kuma nononsu na da kyau".
"Wannan fura da ita zan tafi gida. Yanzu mu ci abinci dai Ammah rana ta yi".
  " Sa'a Babu kalanzir (kerosene) ne, kuma iccen ma ya ƙare".
"Bari mu aika a sayo mana. Kar dai ki ce mun tun safe ba ki ci komai ba?".
"Sa'a! Kar ki wahalar da kanki,kayan abincina sun ƙare".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Ki ke zaune ba abinci, tun yaushe?".
"Kwana uku kenan, fura nake sha ko a sayo man awara".
"Sannu da namijin kokari Ammah, kin yi wauta kar ki sake aikata haka. Mutum ya zauna da yunwa sai kame-kame, dole ki ke ramewa".
  "Uhumm! To ya zan yi Sa'a dole in haƙura, kudin da ke hannuna wadanda Gwaggo ta bani tun bikina sune ban taba ba nake amfani da su".
"Bari ki ji Tunda kin san mijinki ba mazauni ba ne, dole ki tashi tsaye ki nemi na kanki Ammah. Ke yanzu ba yarinya ba ce tunda da aurenki, za ki iya kula da wani. Kiyi amfani da kudin hannunki wajen neman sana'ar yi. Yanzu tun yaushe rabon ki da Salisu?".
  "Watansa biyu kenan da tafiya har yau be dawo ba".
  Tausayin Ammah ya kama Sa'a, ta sa hannu ta goge kwallar da ke niyyar zubo ma ta.
" Ki cigaba da haƙuri wata rana sai labari. Amma kar ki dau zalunci Ammah. Kiyi yaƙi da shi da duk ƙarfinki".
"Toh Sa'a. Yanzu mi kike ganin zan iya yi na sana'a?".
"Abubuwan da kika san ba'a samu a cikin ƙauyenku za ki sara".
  "In sayo kayan kwalama na yara kawai".
"Eh! Ko da shi kin tsira. Idan na koma gida zan sa Abubakar ya kawo ma ki duk abubuwan da kike bukata. Kar ki bari su Gwaggo su ji halin da kike ciki kada hankalinsu ya tashi. Ki koyi adana magana a cikin cikinki, kar ki riƙa bari mutum na uku (3rd party) na shiga lamuranki, saboda wasu gurguwar shawara za su baki".
"Nagode Sa'a, Allah ya biya ki da mafificin alheri".
"Amin Ammah ai kin wuce haka".
" Bari in duba yan aike mu sha furar".
   Ta fito daga ɗakin ta nufi ƙofar gida Sanye da lullubi.
  Zuciyarta ta harba da ƙarfi, ta firgita yayin da ta yi tozali da fuskarsa.
"Uban wa ya baki Ikon fitowa waje?".
"Ka yi haƙuri ɗan aike na ke nema".
  Ihu ta saki a yayin da ya kai ma ta harbi.
" Dan Allah ka yi haƙuri, ba zan ƙara ba".
"Ban gargaɗe ki da cewa kar ki sake kafarki ta taka waje ba. Watau ban isa ba koh? Jikinki zai gaya ma ki, marabar ki kenan yau".
  Belt din jikin wandonsa ya zaro ya daga zai lafta ma Ammah.
Ya ji an riƙe tamau.
"Ban san zaluncinka ya kai haka ba. Kabar mata tsayin watanni daga dawowarta ka hau ta da bugu. Ka wane irin miji ne?".
"Miye amfaninta idan ba bauta ba? Mace ce fa! Ba ki isa ki zo har gidana ki zage ni ba".
"Toh bari ka ji! Macen nan ita ta haife ka har ka kai yanzu. Idan ba ƙaddara ba ka san cewa Ammah ba sa'ar aurenka ba ce, saboda ita din mace ce mai daraja".
"Fita ki bar mun gidana tun ban karya ki ba".
" Yanzu kuwa zan bari ba sai anjima ba. Ke kuma Ammah ki zauna kar ki kwaci yancinki, ki zama baiwa".
Ammah da ke ta kuka ranta kamar zai fita ta kasa tashi daga kwanciyar da tayi ƙasa male-male.
  Fuuu Sa'a ta fita daga gidan zuciyarta na ƙuna.
Hawayen baƙinciki na zarya a kumatunta.
  Kwallo ya sake yi da ita "Daga yau kar in kara ganin wasu tarkace cikin gidana".
Ta gyada kai jikinta na kyarma.
"Ki tashi ki kawo man abinci na".
"Ka yi hakuri ba abinci ya kare. Tun kwanaki uku da suka wuce".
"Rufe mun baki. Shashashar banza,duk abincin da na bari kafin in tafi a ce duk sun ƙare. Talakan Babanki ki kai ma wa hala?".
  Wani irin kuka ya kubce ma ta, wani malolo ya tokare ma ta wuya,ta kasa magana, kalamansa ke yawo a cikin kwanyarta.

Ku daka ce ni!
It has been a while! I missed you more than words can say. You've become part of me. ILYSM 😍😘😘

Na san ni mai laifi ce a gare ku, ku gafarce ni.
"TAURA BIYU BA TA TAUNUWA".
It's kinda short chappy, manage with it In Shaa Allah another chappy will hit your screens tomorrow.
Show me some love 😍 by dropping your comments about th chappy what did you think of the next chappy.
Send your suggestions to ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Please make me smile ☺ with your votes. Just hit the orange star 🌟.

Happy international Women ♀ Day #IWD in advance
#BoldForChange
#StopViolenceAgainstWomen
#VAW
#SayNoToChildAbuse
#GirlsRising
#GirlsEducation

  Please participate in the above #hashtags and tag me whether on Facebook, Twitter or Instagram
@ayeesh_chuchu

MADUBI Where stories live. Discover now