... GISHIRIN ZAMAN DUNIYA

2.4K 188 46
                                    

The Kabir's study room

MADUBI
            ©AYEESH CHUCHU
BABI NA ASHIRIN DA HUDU

... GISHIRIN ZAMAN DUNIYA

"Ina jin ka Ya Deeq".
"Yauwa. Ki natsu fa. Magana ce mai muhimmanci".
Murmushi ta yi.
"Akwai yarinyar da na ke so Maryam sunanta, ita ma ta na sona. We really love each other. Matsalar ta ɗaya ba ta kwalliya irin na ƴan mata dana ga suna yi, abin na burge ni. Ko wannan jambaki ba ta shafawa, dan kyau ta na da kyau. Amma dai kin fita haske. Kayanta daga abaya's da hijabai. Abin na ban haushi. She is outdated, but I love her that".
"Ya Deeq bi hankali, ban gane maganar ka ta ƙarshe ba".
"Opps! Yi hakuri. Ina nufin komi na ta ba ta bin zamani, amma dai ina sonta a haka".
Murmushi Ammah tayi.
"Ya Deeq mi ye abin damuwa toh? Ni wallahi ta birgeni. Ka fi son ta riƙa yawo rabi tsirara? Ko ta bayyana ma duniya kyanta?".
Ya girgiza kai.
"A iya tunanin ka mi ya ja hankalin ka wajenta?".
"Kyawawan halayenta da dabi'unta. Da kuma natsuwarta".
"Madallah! Abinda na ke son ji kenan. Ka ga kenan ba kyanta ko jikinta ya ja hankalinka ba. Ka cigaba a haka kada ka canza, ku sami matsaya kai da ita. Ta faɗi ma ka ka'idojinta, ita ma ta ji na ka. Ta hakan za ku warware matsalolin ku. Kwalliya ba laifi ba ne, ka nuna ma ta kana son kwalliyar kamar in za ka je taɗi. Tunda ƙila fita ne ba ta son yi da ita. Ko kuma dai tafi son rayuwarta a haka ba tare da ta jawo hankalin maza gare ta ba ta hanyar da ba ta dace ba. Duk wanda zai so ta ba zai so ta dan jikinta ko iya kwalliyarta ba. A'a sai dan ya hango wata kimtsatstsiyar dabi'a a tattare da ita".
"Inyeee! Dama kin iya bayani haka Ammah".
  Murmushi ta yi.
"Toh da mi ka maidani Ya Deeq".
"Ina tunanin ba za ki iya magana ba. Kawai dai na ji hankali na yafi kwanciya mu tattauna maganar da ke. Kuma yanzu na fahimta kin ƙara ankarar da ni wasu muhimman abubuwa. Nagode Ammah".
"Ai ba godiya tsakaninmu".
"Na ji! Mun samu mai bada shawara a gidan nan".
Daga nan ya sa kai ya fita, ta cigaba da karatunta har sai da taga la'asar ta kusa.
    ***
BAYAN WATA HUDU
"Alhamdulillah! Mami ɗiyarki fa ta cinye intabiyun da ta yi. Abin mamaki duk tambayoyin da suka ma ta ta bada amsarsu dai-dai gwargwado. Sun bata JSS 3".
"MashaaAllah! Ni dama na san Ammah ba za ta ban kunya ba, akwai self-confidence ba ta yadda gadona ba. Kamar gobe ne za ka ga ta gama. Yanzu ai ta cika shekara sha hudu. Bata yi latti ba".
"Ai za ki yi mamaki, ba wuya shekara hudu in dai da rai da lafiya. Kuma ba ta da girman jiki ".
" In Shaa Allah. Layla SS 2 take ko?".
"Eh Mami".
  Ammah da Layla ne su ka shigo cikin hijabansu kalar ruwan ƙasa, yadin na ta kyalli da daukar ido.
Khalifa na ta kwance saman kafaɗar Ammah yayi bacci.
  Daga gidan Ya Hashim su ke.
"Ni ko hajaban nan naku na mun kyau gaskiya. Next time Idan mun je Bakori zan sa Gwaggo ta siyo man inda ta siyo su".
Layla tayi farat ta ce "Mami ko yanzu idan kina so sai a kira mai hijaban, kin san yadin hijaban ƴan Katsina ba daga baya ba. Ina da lambarta da Gwaggo ta sa aka turo man, wasu suka gani suna so".
"Wai dama dinkakkunsu ake saidawa?".
"Eh Mami, sunan hijaban ma fa AUNTYSIS MODESTY HIJABS".
"A'a lallai mata sun dage da neman sana'a. Ki kara ta ina son guda hudu, zan faɗa ma ki kalolin da na ke so".
"Toh Maminmu".
"Ammah barka fa, sati mai zuwa sai makaranta koh?".
"In Shaa Allah Mami".
"Toh Allah ya bada sa'a".
"Amin Mami".
  Abba ne ya shigo Mami ta tashi ta amshi jakar hannunshi.
Su kai ma sa sannu da zuwa. Ya rage su kadai a falon, sai Ya Deeq da ke amsa waya.
Yana ganawa.
"Best Friend zo ki ji".
"Wai Ya Deeq sai ku yi ta kus-kus ku bar ni. Ka dai Abba".
Gwalo Ammah ta yi ma Layla.
"Ammah zan kama ki".
Ta ruga ɗaki.
"Yanzu Maryam ke ce min Iyayenta sun ce na turo magabatana".

"Alhamdulillah! Ya Deeq angon Maryama".
Murmushi ya yi.
"Bari in jira Abba ya huta mu yi maganar".
"Allah shi bada sa'a Ya Deeq. Bari in je in lallashi Twinnie".
"Wannan haɗin kan naku, i don't feel safe my secret with you. Zan canza special adviser".
"Haba dai BFF abin da ya zama dole kawai na ke faɗa ma ta".
Ta yi dariya tare da rugawa.
"Wa ki ka bar ma Khalifa, fita zan yi".
"Ga Inna Hindu nan".
Tana shiga daki ta isko Layla ta kunna MacBook ɗinta.
"Twinie".
"I'm angry with you".
"Subhanallah! Kaina bisa wuya. Sorry twinie, bari in baki labari mai dadi".
"Ban so. Ni ki wuce wajen Ya Deeq ".
" Iyayen Maryam sunce Ya Deeq ya turo da magabatansa".
  Wani irin tsalle Layla ta yi "Alhamdulillah!".
Sannan ta fara juyi tana rawa.
"Kai har na ƙagara inga bikin Ya Deeq. Na ga bakin Mami. Ya Deeq na mutane".
"Bari kawai, ai BFF na da ban ne".
"Ina za ki haɗa shi da Ya ARK, yana can dai na ga matarshi dan ta shiga uku".
"Ke irinsu mata murza su suke son ran su, nan in kin bibbiya ya mutu kan son wata tana ta gasa shi".
Layla ta kyalkyale da dariya.
"Twinie kin iya mugunta wallahi. Ai ko ni nafi son ya samu mai casa shi, mutum da yazo waje kamar mutuwa ta gibta".
Suka sake darawa.
"Ehrmmm".
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel". Abin da Ammah ta iya fada kenan.
Layla ta zaro ido.

MADUBI Where stories live. Discover now