BABI NA BIYAR

2.8K 265 37
                                    

MADUBI
©AYEESH CHUCHU

BABI NA BIYAR
***
"Muntari ɗazu budurwarka Asma'u ta zo gidan nan nemanka".
"Kai Hajja ki daina haɗa ni da wannan ballagazar yarinyar, a ina ki ka ga budurwa na bin saurayi gida?".
"Sai a wannan zamanin na ku, ni sam yarinyar ba ta kwanta mun ba, yarinyar da uwarta ke juya gidan, sai abin da uwar ta ce ake yi a gidan".
"Hajja ba ku rabo da surutunku na mata, ina ki ka ji wannan zancen kuma?".
"Ina fa idan ba wajen mutane ba, ai yanzu an daina kiwon dabba sai mutum, duk abin da ka ke yi mutane na nan suna nazarinka".
"Hakane Hajja, bari in je gidansu Ammah ina son in dawo da wuri in dan kwanta har zuwa la'asar".
"Sannu da kokarin taimako Muntari, Allah sa ka fi haka. Yaushe za ka kawo man kanwar ta ka ne?".
"Amin Hajjata, mi kike ci na baka na falling down, har gida zan kawo ma ki ita, kullum sai ta ce in gaida ma ta ke".
Da haka ya sa kai ya fita.
Tafiyar da ba wuce mintuna goma ba ta kai shi gidansu Ammah.
Sallama yayi sai da aka amsa ma sa sannan ya shiga gidan.
"Lale marhabin Muntari".
"Gwaggo ina kwana?".
"Lafiya lau, ya ka baro Hajiya?".
"Ta ce a gaishe ku".
"Toh Madallah, ai kuwa yanzu Ammah ta fita daga gidan ta je gidansu Sa'a sun yi hutu, bari in sa a kira ta".
"A'a barta Gwaggo su gaisa da kawarta gobe ma yi karatun dama akwai inda zan biya, mu ma mun kusa komawa makaranta bai fi wata ðaya ba".
"Allah sarki Muntari, Allah shi bada sa'a, ai nagode wallahi da irin kulawar da ka ke ba Ammah fagen karatu, Allah shi baka mafi hakan".
"Amin Gwaggo ".
Daga haka ya mike ya fita daga gidan.

"Laa Sa'a wancan kamar Ya MK".
"Waye haka kuma?".
"Ke bari idan kin zo gida in baki labari".
Ba ta bari Sa'a ta yi magana ba, tayi saurin isko shi.
"Ya MK".
"Na'am kanwa Ammah". Ya faɗa cikin kasalalliyar murya.
"Ba dai har za ka tafi ba, na je gaida Sa'a ne".
"Eh ina da wajen zuwa Shiyasa ban jira ki ba".
"Laa na manta, Ina kwana?".
"Ba zan amsa ba, sai yanzu da ki ka tuna".
"Ka yi hakuri don Allah Ya MK",ta yi maganar cikin canza yanayin fuskarta zuwa ta shagwaɓa.
Murmusawa ya yi ya ce "it's ok".
"Toh mu koma gida in nuna ma aikin da ka bani na yi, kuma ba ka ga zanen motarka da na yi ba, ya yi kyau".
"Ki bari sai na dawo gobe kinji? Take care of yourself for me".
Murmushi ta yi tare da gyada kai, ta wuce cikin gida.

***
GIDANSU ASMA'U

"Asma'u wai ba za ki fita harkar yaron nan ba, tunda ya nuna bai sonki ai sai ki hakura".
"Umma wallahi ni ba zan iya rabuwa da Mukhtar ba, dan Allah ki taimaka mun".
"Kinga a wannan fannin sai dai kiyi hakuri, yaron da ko karatu bai kammala ba, bare aiki shi zan yarda ki aura. Ke ma duka-duka nawa kike Asma'u?".
"Umma ni ko minene haka nike son shi, idan har kina son farin ciki na".
"Ai sai ki yi, ba shiri muke da kakar yaron nan ba dan haka ba abinda ya shafe ni. Ga yaro dan arziki da ke kaunarki kina ma sa wulakanci duk da haka yaki tafiya ".
" Ni fa ban son Imrana, ya cika surutu Umma,har neman mata aka ce yake yi"
"Miya ruwanki da neman matansa, da kunyi aure zai daina, kuma yaron nan na da kuɗi. Ke ki huta nima uwar ta ki in huta. Ai an bar yayin auren talauci yanzu. Ina za ka saida akuyarka ta dawo tana ci ma ka danga".
"Shi ma fa Mukhtar ɗin 'yan gidansu na da kudi har mota babansa ya siya masa ".
" Ke raba ni da maganar Mukhtar din nan, Imrana ni ke so ki aura da kin gama aji shida mu sha biki, irin tagomashin arziki da yaron nan ke kawowa gidan nan ai ba'a magana ".
" Bari Abba ya dawo na san shi zai goya man baya".
"ooh Ni Ade, ka haifi yaro wata tara amma yaki jin maganar ka. Kan yaron nan sai in ma ki baki Asma'u. Da Ubanki bai son Imrana da bai amshi anininsa ba".
Shiru tayi ta cigaba da linke kayanta da take yi. Tana shawara ita da zuciyarta.
***
GIDANSU AMMAH
Ammah da Sa'a ne zaune a ɗakin Gwaggo su na hira.
"Ammah ba ki bani labarin yanda ku ka haðu da Ameer ɗin islamiyyarmu ba".
"Wai Ya MK ki ke nufi?".
"Eh shi fa".
"Ya MK ya taka rawar gani a rayuwata Sa'a, shi ya fara cika mun burin da na dade ina so. Ya mun abubuwa a rayuwa wadanda har abada ba zan manta da shi ba, a wata dayan nan na karu da abubuwa. Har zan iya karatu da rubutu na Hausa Sa'a ba karamin taimako ya mun ba".
"Gaskiya ya taimaka, ni ma kuma zan goya ma sa baya".
"Nagode Sa'ata, saura shirin Musabaka ranar asabar".
"Allah shi taimaka ya bada sa'a".
"Amin".
Sun dade suna fira, Sa'a na ba ta labarin makarantar bodin.
"Wai kin san Ammah muna zaune wata siniya ta kira mu daukar mata ruwa daga mono (borehole), ai kuwa ta fada mana ɗakin da za mu kai ma ta, muguwa ce sosai wallahi, tana tafiya kuwa Labiba ta yi fitsari cikin ruwan, dayan mu ka tofa yawu, mu ka kuma kai ma ta ruwan haka".
Baki Ammah ta saki tana dariya harda rike ciki.
"Kai Sa'a an kun iya mugunta, da kun barta da halinta amma hakan bai kamata ba".
"Ke baki san halin siniyas (seniors) din nan ba, mugunta garesu, hakanan ba ka yi laifin komi ba amma su dau karan tsana su daura ma".
"Ina ma ni ce, rayuwar bodin da dadi".
"ke bata da wani dadi sai wahala ba ki ga nayi baki da rama ba?".
"Eh da haka amma karatun da za ki samu ai yafi komai".

***
"Halimatu Ibrahim Liman daga MADARASATUL TAHFIZU QURAN WADDARASAT ta fito".
Ta fito ta zauna wajen da aka tanadar ma ta.
Karatun Al-Qur'ani ne ke fita cikin zazzakar murya, dubban idanun jama'a na kanta, hakan be hanata karatunta ba, cikin fidda tsoro da bama kowane harafi hakkinsa.
Bayan ta gama ne, mutane ke ta kabbara tare da jinjina ma ta.
***
GIDANSU AMMAH
"Innani sannu da zuwa ".
" Yauwa sannunku".
"Malam yace ba ki jin dadi, har muna shirin zuwa sai kuma ga ki".
"Eh ai na ji sauki, kin san yanayin tsufa Halima".
"Hakane, Allah shi kara lafiya da tsawancin kwana".
"Amin". Faɗin Inna.
"Wai ina Halimatu karama ne?".
"Ai kuwa suna can wajen Musabaka, da yake har da ita cikin masu karatun". "Abu yayi kyau, bari Iro ya shigo dama muhimmiyar magana ce ta kawo ni".

Pweeeeeeeeeeeeh! Guess what is on Innani's mind..

Huh! I'm so sorry for not updating MADUBI yesterday.. Oya take this as breakfast.
I'm so happy that we've reached 100 votes.
Thanks a million.
Please keep on voting and commenting.

MADUBI Where stories live. Discover now