MADUBI
©AYEESH CHUCHUBABI NA BAKWAI
"Haba Innani minene na kuka kuma? Ki yi hakuri abinda ki ke so shi za a yi".
" Toh ina so Halimatu ta fiddo miji, idan ba ta da shi ni kuma zan fitar ma ta".
"Shikenan Innani duk yadda kika yi dai-dai ne".
Da kyar ya mike tsaye ya fita daga ɗakin. Yanayin da Inna ta gan shi ta tabbatar da babu lafiya.
"Malam lafiya kuwa?".
"Ba komi Mairo". Ya shige turakarsa.
***
"Dadi na shirya mu tafi".
Tare suka jera kamar wasu abokai, sai dai yanayi fuskar da jikin ne zai bambance yawan shekaru da ke tsakaninsu.
Annuri ne dauke a fuskar MK, sai isar su kofar gidansu Ammah yasa yaji ya karaya.
"Yusuf shiga ciki idan Malam na nan ka ce ana sallama".
Yusuf ya shiga ciki don isar da sakon MK. Bayan ya isar ya leka dakin Gwaggo inda Ammah ke zaune tana bitar karatunta.
"Yaya Ammah yanzu naga Ya MK yana kofar gida ma".
Tsalle ta buga tare da juyi a tsakar ɗakin.
"Ashe ya dawo?".
"Eh, Baba yace a kira ma sa,shi da wani mutumi ne ma".
Shiru ta yi, tare da cije laɓenta na ƙasa.
***
Musabaha su ka yi da juna, bayan sun gaisa Malam ya ce "Alhaji ku shigo ai ba kwa tsaya waje ba".
Tabarma yasa aka shimfiɗa ma su, bayan su zauna aka sake gaisawa.
Farfesa ya ce "Dalilin zuwa na gidan nan saboda ɗiyarmu ce Ammah, na zo neman alfarma a wajenka Malam Iro, ka dubi girman Allah da kuma canjin zamani da muke ciki ka bar yarinyar nan ta yi karatun boko. Irin wadannan yaran ba'a so ana tauye su, ka ba ta dama ta nemi ilimin nan. Nayi alkawarin daga Naira ɗaya zuwa duk iya abinda ya sauwaka da be gagare ni ba akan karatun Ammah zanyi ma ta".
"Alhaji ban tari numfashinka ba, batun gaskiya Ammah ba za tayi karatun boko ba, ko da na amince Innani sam ba za ta yarda ba".
"Idan ba matsala sai mu je har inda Innanin take mu ji ta bakinta".
"Ba sai kun wahalar da kanku ba, ta nan gida ta zo da wani babban al'amari da ba ni zaton za ta yarda da ku".
Nan ya tashi don kiran Innani.
MK da tunda da aka fara magana kansa na ƙasa ya faɗa can wata duniyar.
Muryar Innani su ka tsinkaya "Sannunku da zuwa, lale marhabin".
Sun gaisa cikin mutunci da girmama juna.
Nan Prof. Usman ya sake ma Innani bayani kamar yadda ya yi daga farko.
"Alhaji sai dai ka yi hakuri da maganar karatun Ammah, dan maganar da ni ke ma yanzu maganar aurar da ita na zo yi".
"Aure?". Cewar MK
"Kwarai kuwa".
"Ni a bani aurenta".
Cikin kaɗuwa Farfesa ya ce "Mukhtaar lafiyar ka kuwa?".
"Dadi lafiyata lau,aurenta zan yi".
"Yaro dakata na riga na ma Halimatu miji, ni kwadayi ba zai sa in saida jikata ba".
Ganin Farfesa na niyyar tashi yasa MK saurin dakatar da shi.
"MK tashi mu tafi".
"Daddy.... ".
" I don't want to hear a word from you". Dole ta sa ya yi shiru tare da bin umarnin mahaifinsa.
***
BAYAN KWANA BIYU
"Gwaggo kin ga Yaya MK ya daina zuwa tun ranar da Yusuf ya ce mun gasu can a kofar gida ban kara ganin shi ba sati ɗaya har da kwana uku".
Gwaggo cikin jimami ta ce "Kila aiki ne ya ɓoye shi, hakanan banza Muntari baya kin zuwa gidan nan sai da dalili".
Ta yi saurin tashi gudun kada Ammah ta sake jefo ma ta wata tambayar.
Ammah ta yi lamo akan gadonta, shakuwarsu da Yaya MK ya sa take jin kamar ta shekara ba ta ganshi ba.
Ga Sa'a ta koma makaranta, kadaici ya ma ta yawa.
Fitowa ta yi tsakar gidan, "Gwaggo don Allah inje gidansu Yaya MK in ji ko lafiya?".
"Ammah rufa man asiri, ina ki ka taɓa ganin anyi haka?".
"Gwaggo ganinshi kawai zan je inyi".
"Ai sai ki kama hanya ki tafi, kin samu mai lallaɓa ki ne".
Tashi tayi ta koma ɗakin.
"Mairo bani jin dadin abinda ki ke Ammah, ki sassauta ambar irin wannan abin yanzu. Kina ina yaran zamani da ke wasa da dariya ga ya'yansu, su yi fira tare, su ji matsalolinsu".
Girgiza kai ta yi, tana tunanin ba dan ta samu abokiyar zama kamar Gwaggo ba mai son ya'yanta da zuciya ɗaya duk da ita Allah be ba ta haihuwa ba, amma take nuna masu duk wata kulawa. Ba kamar Ammah da sam ba ta san ɗaɗinta ba.
Da ba dan Gwaggo mutumiyar kirki bace da Ammah ba ta samu tarbiyya yanda ya kamata ba.
"Wai ke Mairo naga sam ba ki damu da hukuncin da Innani ta yanke a kan Ammah, gaskiya da akwai yanda zan yi da na hana". Nan Gwaggo ta cigaba da maganar auren Ammah
"In banda abin ki Gwaggo mi zanyi akai, bayan Malam ma be isa ya ketare dokar nan ba, addu'a ce kawai mafita".
"Hakane, Allah yasa haka shi yafi alheri, ni bamma san ta ina zan fara ba,a ce kamar Ammah za a ma aure a wannan zamanin da sa'o'inta ke fafutukar neman ilimi. Sam Innani ba ta kawo hanya me ɓullewa ba".
Ammah da ke tsaye ta gama jin duk wani bayanin su, ta fashe da kuka tare da rugawa cikin ðaki. Cikin azama Gwaggo ta mike ta mara ma Ammah baya jin kukanta.
***
"Daddy please do something akan maganar Ammah, Momi ki sa baki".
"MK ka yi hakuri ba abinda zan iya tunda Iyayenta ba su so, kaima ka hakura".
"Idan ma banda MK ina shi ina haɗa kansa da ƙananan mutane, waɗanda ana nema masu gata basu gani".
"Haba Dakta ai duk ɗaya ba dan kakar yarinyar ta kafe ba, Mahaifinta be da matsala".
"Ai kansu su ka yi mawa".
"MK kayi haƙuri, Allah ya ga niyyarka ta alheri ".
" Ok! Dad".
Ya sa kai ya fita daga falon, farfajiyar gidan ya nufa ya zauna cikin gazebo inda aka tanaɗi kujeru masu kalar ruwan kasa, na alfarma a wajen.
Duka hannuwanshi biyu ya tallaɓe kansa da su, tunanin be wuce yanda zai taimakawa Ammah. Baƙincikin furucin Innani yasa shi kasa zama Bakori ya biyo Daddy a ranar.
Shakuwarsu da Ammah yasa yake jin kaɗaici zaman shi gida. Kamar wanda aka tsikara ya yi saurin tashi ya shige cikin gidan.
Hanyar matattakalar da za ta sada shi da ɗakunan baccinsu yayi, waɗanda ke a rukunin upstairs na gidan. Be ko kalli iyayensa ba dake zaune suna fira.
"Prof duba ka ga, kamar MK baya cikin hayyacinsa".
"Kar ki damu, he'll be alright. Duk abin da ze yi kar ki tanka ma sa.
A hankali yake sakkowa daga saman matattakalar benen, roɗi-roɗin da ke kwance a saman fuskarshi da yayi jajir! Shi zai tabbatar da cewa ran Mukhtar a ɓace yake.
Da kyar ya iya furta "Daddy,Momi na tafi Bakori".
"MK! Why the sudden change?"
"Tafi MK, Allah shi kiyaye hanya, ka gaida Hajja".
Ya gyaɗa kai, ba tare da yace uffan ba.
***
BAKORI"Ammah ba za ki bar kukan nan ba? Tun ɗazu kin ƙi ki saurari kowa".
"Haba Gwaggo yanzu kamar ni za a yi ma aure?". Ta sake rushewa da kuka.
Gwaggo ta rungumeta, tana bata baki.
"Ki bar kukan nan kin ji? In Allah ya yarda zanyi bakin kokarina inga Innani ta janye maganar auren nan".
"Dan Allah Gwaggota ki taimake ni kar ki bari a mun aure".
"Kar ki damu kin ji, share hawayenki". Abdullahi ya shigo ɗakin Gwaggo, hannunshi riƙe da ledar Malteser.
"Yaya ki zo".
"Kai Abdullahi minene a hannunka?".
"Ba ni aka yi ".
" Waye ya ba ka?".
Da gudu ya fita daga ɗakin yana ƙara jadadda ma Ammah kiranta da ake.
" je ki ji wake kiranki".
"Toh Gwaggo". Dama izinin Gwaggo take jira, jikinta ba karfi duk ya yi sanyi tasa hijabinta, ta fita kofar gida.
Baki buɗe, idanunta kamar za su zazzago,ta murza idanunta tare da furta "Ya Mmm Keee?".
Ya kasa dauke idanushi akanta,zuciyarshi na bugawa da ƙarfi, wani irin abu ke fizgarshi kamar magnet ya haɗu da ƙarfe.
Cikin maƙoshi ya furta "Halimatuu".
Kwarmin idanunta sun cika taf! Da hawaye za ta yi magana su ka idasa gangarowa.
"Ya MK shi ne ka tafi ka bar ni koh? Ga Innani ta ce aure za ta min".
Ya kasa cire idanunshi daga kallonta, harshenshi ya gaza furta kalma ɗaya. A hankali ya karaso gabanta.Double double sorry for not updating MADUBI yesterday. Smile and forgive me. ILYS
Keep voting and commenting, for any correction or suggestion please holla me ayeeshasadeeq2010@gmail.com
Thanks a million.www.chuchungaye.wordpress.com
www.nagarta.com
Wattpad @ayeesh_chuchu
YOU ARE READING
MADUBI
General Fiction#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta...