*UMMIN ABBATEE*😘
*225~230**WAHALAR RAYUWA*😪
ko ajikin afaf dan kuwa kwantawa yayi asaman gado yana kare mata kallo jawo towel din tayi ta ta daura.......haba malam menene haka zaka fadamin daki ba izini.....au shigowa dakin mata ta sai da izini bakida hankali......ta turo baki wai bama kafita ba me yadawo dakai toh? ohhh murna kike da fitan tawa ashe shiyasa ina fita harkin bude kofa ya miko daga saman gadon yazo daf da ita,dataga da gaskene yanason riko tane sai ta juya zata fada toilet damka daya yayi mata ya kamo ta tare da manna ta akirjin sa yafara shafo cinyoyinta yace daga zan taimaka miki.....tace wallahi banaso karabu dani...............kai bakya son me banason gulma wannan irin cinyoyi haka dakika bude haka bari dai na taimaka miki.......kwace jikin ta tayi tare da cewa wallahi banaso sai kanacin amana ta kanason Abu kana fakewa da wai nike so toh banaso ko kai din ma nadena Son naka dan haka kafita min adaki malam. .....tsaye yayi yana mamakin ta ohh lallai ay tunda kikace kinji kingani toh ay shikenan wannan auren shi aka ce ma mutu karaba takalmin kaza. .......dan haka garama kici gaba da son nan da kikemin yan mata yakoma takwanta zo dan Allah karki bata min lokaci taho na taimaka miki na wuce wata........dallah malam kafita kabani wuri nace maka banaso anayin dolene nice nafada maka cewa ina so?fitamin adaki dan Allah...........duk ranar dakaji kai keso dakanka kazo bazan hanaka ba....amma yanxu tafi nayafe............mikeya yayi tsaye yace nine kika daina so? to shikenan dama can nasan ba dagaske kike yiba kuma insha Allah bazan kara shiga tsabgar kiba...........bude kofar yayi ya bugo ta da karfi. .........fitar da baiyi ba kenan ya koma sama ya kwanta yana ta huci saboda bakin cikin kalmar da tafada masa wai bata son nasa..............
🏵🏵🏵
tayi data zanin fada masa wannan kalmar saboda yanda taga yahau fushi da ita ko kulata bayayi. ... ..ko girki tayi baka kulawa balantana yaci.....sai dai ma yasiyo nashi ya hau sama yaci sai idan tashiga gyara masa wannan ta ga robobin take away............
bayan tafito daga dakine wuraren karfe tara tana tunanin ya wuce gun aiki sai tahau sama dan tagyara gado da dakunam kafin ta dauko tsintsiya.....tana cikin dakin ne sai gashi ya shigo shi mamakin ganin ta yayi dan kwana biyu kenan ranonshi da yasaka ta a ido. ..........tsaya wa yayi abakin kofan.......lafia meya kawo ki dakina?ummm tare da kauda kai ina gyara maka ne.....nasakine?meye amfanin kyautata ma wanda baka so zo dan Allah kema kibarmin dakina........banaso zan kawo wadda take sona zata gyaramin karki damu fita da Allah nagode kin fita tayi ta tsaya kawai ta tsura mishi idanu yace ok idan bazaki fitaba ni bari nabaki wuri............
Anyi haka da Sati biyu ne afaf yasamu ahlam da zik yana neman shawaran su yanda zai shawo kan shaheeda anan suka bashi shawara wadda naga yanata kada kai yana murmushi................
🏵🏵🏵
shigowa yayi cikin palourn dawowa sa saga gidan babansa kenan ya ajiye wata leda yanda abunda ke ciki zai iya fitowa wake ya zauna
yana cewa washh kai auren soyayya da dadi yake Allah yakawo min halimatu saadiya ko nasamu mai min tausa idan nadawo gida............Dakar fi yake maganan yanda shaheeda yaji burontun ta a kitchn zata iya jiyoshi..........da gudu ta fito tare da zaro idanu tace wat aure zaka sakeyi afaf. yace oh sowie. wai ba wanda yafada miki ne?kiyi hakuri fa manta wa nayi abubuwa sunmin yawa ga cards nan ki diba mai isanki wadanda zakiba mutanen ki.........yadago ledan yace gashi ledan ta kwabe duka katinan suka fado iv cards ne masu manne da pic din afaf da wata kyakykyawan budurwa...........shaheeda ihu tasaka tare da xubewa akasa ta riqe kafar sa dan Allah karufamin asiri wallahi bazan iya hada miji dakai ba afaf ina son ka fiye dakai na wallahi yace kai haba banason salo na yaidara meye haka harda kuka me zakiyi da wanda bakyaso yazaayi kiyi kishina kuma kinga niyanxu yanda nakeji na ko tafiyan ki kikayi bazan damuba..........ga hanya nan. ..........kuka takeyi mai tsuma zuciya yanaji har aransa yamatsu su ahlam da zik so fito daga wurin da suka boya saboda ya rungimo matarsa ya lallasheta.......yace to dama kina sona meyasa kikace bakya sona?tace wallahi wasa nake maka bazan taba dena sonka ba saboda yanda kake nunamin ne abun yabani haushi kuma bayan nafada maka nayi danasani wallahi dan Allah kayafemin ka hanya maganan auren nan yace inaaaa aure ba fashi yakike so nace ma amaryan tawa dan ubanta wallahi mijina yayi karfin ta kabani numbern ta up address yanxu ma zanje mu muna da ita me tafini da zakace kana sonta yace kinsan meta fiki tace aa sona ta fiki kuma ita basa tamin ruwan komai ba balantana na kanta.............mikewa tayi tace wallahi nima bazan maka rowa ba dan Allah muje kome zakayi kayi amma dan Allah kafasa.........dariya suka jiyo ana kyalkyalewa da ita daga gun kofa shaheeda ta waiga sai ganin su ahlam tayi shima afaf ya mike yana dariya kallon su tashiga yi hade da mamaki ahlam ta karaso ta dafa shaheeda tace zauna sis dina kin baki tausayi ashe haka kikeson bro kai Allah yakara so da kauna tace kaman yaya bangane ba sis aure fa zai kara ki tagani rokon sa wane irin kiyayya yakeyimin haka😢ahlam tace ay duk duniya bayan iyayen shi ba wadda yakeso sai ke tsaya ma kiji..........nan ta kwashe duk labarin plan din da suka hada ta fada mata.......aykuwa daga kuka shaheeda sai gata ta koma dariya tana kunyan hada fuska da afaf ma. .....
mikewa afaf yayi tsaye tare da bude hannayen sa alaman tazo kunya takasa mikewa sai yajuya baya yace ahlam muje gidan su Sadiya muce ba tun auren nan yananan ba fashi da gudu shaheeda ta karaso ta rungume shi ta baya tace nooo sahibul shaheeda adena wadan nan kai na shaheeda ne ita kadai insha Allah juyowa yayi da ita ya rungume ta sosai da kyau..............zik yace honey Mike kigani mu wuce gidan mu ko kuwa yamxu musha mamaki ahlam tace aykuwa bako karamin mamaki ba dan amarene......
by RUKKY😘 *luv u all*
