*UMMIN ABBATEE* 😘
*105~110*
*WAHALAR RAYUWA*😪
Yace ai ba damuwa alhaji zan kaika ko yaushe kashirya yace to kabari gobe idan Allah yakaimu...... yanxu ya maganan exam din yaushe zaa fara rubutawa?afaf yace alhaji gobe da karfe biyun rana akace min alhaji yace to madallah ya zakayi da takaddunka da kace sunacan gidan naku yayi shuru yana tunanin mafita yace wallahi alhaji tunda safe abun da nake tunani kenan dole zanje ne na dauko......alhaji yace karka damu anjima kazo kasameni da karfe uku daidai sai muje ka dauko daga can sai mu wuce naga baban maka...... sai ga matar gidan ta shigo da sallama hajiya amina kenan mata daya tak agun alhaji idris.........suna zama a kebbi state daga baya aka tura shi kasar France daga wurin aikin su bayan shekara biyar ne aka dawo dashi Nigeria amma sai suka kaishi sokoto state suna da yara uku shaheed shaheeda sai ahlam itace auta shaheed yana da shekara 22 yanxu yana kasar Sudan inda yake karanta medicine ita kuma shaheed shekarunta goma sha tara inda take 100 level a usmanu danfodio university of sokoto state sai auta ahlam tana da shekaru koma sha hudu tana jss3........ta zauna tare da fara arta tace kai da dan naka ne ake tattaunawa alhaji yace hmmm akan matsalar dayake cikine nakeso Na kaishi ya dauko exam card dinshi daga can naje naga mahaifinsa ...ya gaida hajiya sai yamike yace nagoda sosai alhaji...... yabude labule zai bar palourn ashe mutum na zuwa da sauri sukayi karo yabuge mata hanci ta kurma kara wayyo mahma help me tana kokarin cire labulen daya rufe mata fuska shi kuma sai cewa yake am very sowie pls am sowie tace dallah matsa ni nawuce so kake ka kasheni abunda na tsana bai wuce a taba min dogon hancin nan nawaba dan dabaka da shi da sai nace kana bakin ciki dashine hajiya amina ta daka mata tsawa ke uwar marasa kunya zonan bakiga ba da gangan bane haba kidinga hakuri mana dallah zoki wuce ki wuce kiba mutane wuri.....sumsum ta wuce da sauri tana gunguni......alhajibyace yi hakuri afaf kaji jeka huta kafin anjima din hajiya amina tace alhaji yakamata kan kaje kaga baban yaron nan dan gaskia kamar tayi yawa kama yake min da mutane biyu dana sani alhaji yace hmm kedai bari ay namtasu naga baban nashi ko hankalina zai kwanta
🏵🏵🏵
Sun isa gidan abakin gate alhaji yayi parking yafito ya jingina da motan afaf ya zagayo wurinsa alhaji yace kashiga ina nan ina jiranka ba abunda zai faru insha Allah yace to yasa kai cikin gidan bakowa a tsakar gida ya wuce kawai cikin dakin nasa awatse yaga kayan sa dakin ya hargitse daga gani wani ya shigo dakin ne........yaduba takaddunsa sama ko kasa babu baigani ba dama dakin bawani tarkace ke ciki ba katifa ce sai akwatinsa guda biyu........yafita ranshi abace yana tunanin shiga cikin gidan amma yaga ba amfani gara yafara fadama alhaji yaji mezaice kawai sai ya fito alhajin yadago kai ya kalle sa yace afaf ya akayine lafia daiko? naga ka dade ne yace alhaji wallahi nanema na rasa koda nashiga dakin daga gani wani yashigane ya dauka saboda duk an hargitsa dakin............ya girgiza kai yadafa kafadar afaf yace yi hakuri kaji sunyima kansu Allah zai saka maka karka damu zansan yanda zaayi shiga motan muje wurin mahaifin naka. ........
🏵🏵🏵
Assalamu alaikum baba tsoho kana ina da sauri kakan nasa yafito daga daki wato mahaifin sly shidai alhaji idris yana bin wurin da kallo ne kawai yana mamaki meke shirin faruwa ne tabbas duk da yafada rabonsa da gidan nan bazai taba manta gidan ba dama kai kansa gidan ne kawai bazai iya yiba.........fuskar tsohon ya tsura ma ido wanda yasan ba ganeshi zaiyi ba saboda yanayin tsufa sai ga wata tsohuwa itama tafito tana cewa to yaron kirki sannu da zuwa kwana biyu kaki zuwana duba mu.....afaf yadawo kusa da kofar yace alhaji bismillah sai a sannan tsofaffin suka kula dashi tace au kaji ka da shirmen naka kazo da bako kabar shi Anakin kofa tace maraba zauna......ya tsugunna ya gaidasu suka amsa cikin faraa tsohon yace bangane kaba bawan Allah afaf wanene afaf yace alhaji tsoho gajen hakurine dakai ba yace kaji ni da yaro to nayi shuru yace bari nafada zuwa naga babana yace baban naka da harira tace kace kagaji da zuwa duba shi.....yace hmm bari indubashi ina zuwa.......can sagashi yadauko baban nasa acikin wheelchair innalillahi!!!abunda alhaji ya mike tsaye yadin ga maimai tawa kenan suka dago kowa yazuba mishi ido da gudu ya kara sa kusa da sulaiman dake zaune kai a dangwabe yace sly kaine haka yafara kuka yana cewa meya sameka abokina me nake shirin gani.......
Sai da ya nutsu yadena kukannne sannan yabasu labarin abokan takansu da sly har baban sly din ma yagane shi daga baya......yakuma basu labarin dalilin zuwan shi gidan saboda halin da yaron wahalar rayuwan da yaron ke ciki.......jikin su ba karamin sanyi yayi ba saboda yaron baitaba fadamusu ba shidai sly dama yasan komai.........alhaji idris yace amma baba ya aka bar sulaiman agida batare da ankaishi asibiti ba?baban yace anyi anyi abun yakici yaki cinyewa ne sai muka barma Allah..............
🏵🏵🏵
Tun daga lokacin alhaji isdri yace day dauki nauyin komai na afaf har karatunsa shine dalilin dawowar afaf gidan nashi dake unguwar alkilla road.......tunda yadawo gidan yake jin dadi abunsa sai dai matsala daya tak itace shaheeda bata son shi dan Allah yayi ta mutum mai kishi gani takeyi kamar yanxu mahaifan nata sundena ji dasu sai afaf..........ta fito daga dakinta zata fita sai ta hango afaf a palour yana buga game shida ahlam sai dariya suketa kyalkyala azuciye ta shigo palourn tace keeee bakida hankaline kin zauna tare da namiji kina ta wani washe baki dallah tashi kishiya ciki ahlam ta wuce tana buga kafa akasa yana cewa gaskia nifa ana takuramin ina ruwan ki dani wallahi sai na fadama mahmah taruga da gudu......shaheeda ta juyo tana kallon afaf tace kai kuma banason shishshigi dan talakawa kawai daga zuwa kasani zaqe sai kaudi kake ma mutane dan antaimaka andauko ka daga cikin wahalar rayuwan danake ciki mtsw nakama kanka fuuuu ta wuce tafita ....... ...ya zauna yayi shuru nidai narasa menayi ma yarinyar nan take tsanata haka.......
BY RUKKY😘 *luv u all*
