WAHALAR RAYUWA

45 2 0
                                        

*UMMIN ABBATEE*😘

          *120~125*

*WAHALAR RAYUWA*😪

Mai gadi ne ya isa kofar gate din zai bude saboda buga kofar da ake tayi yana banda ki.......bakuwar fuska yagani yace sannu da zuwa hajiya wakike nema tace sannu kadai ina neman masu gidan ne.....yace wake nan daga ciki tayi shuru tana tunanin wazata ce sai tace um sulaiman yace hajiya baya nan tace dan Allah yaushe kake ganin zai dawo sai najira shi yace tab yana mai rike haba yace ay yana kasar paris watan su biyu kenan da tafiya.........ta zaro idanu  tare da dafe kirji tace baban shifa yace yafita amma bazai dade ba zai dawo saboda lokacin  dawowar sa ya kusa tace to nagode bakowa acikin gidan ne zanshiga sai najira shi yace to ina zuwa bari naje na sanar sa H ajiyan wa zance ta ce kace zainab yace to yashiga yayi sallama aka ansa yafada mata tace wace zainab kuma jekace wace zainab yanda duniya ta lalace karka shigomin da mutum gashi nikadai acikin gida tace to rankishi dade....yakoma yace tace wace zainab wai tace kace zainab  tsohuwar matar sulaiman ya tsura mata ido yana mamakin ashe itace zainab shidai fuskar ta masa kamar yataba gani......ya juya yafada tace toh fa dame tazo bari nafito  je ka ce ina zuwa.........fitowan sa daga cikin gidan keda wuya akayi horn maigidan ne yadawo yaje ya bude yana mai karema matar da yagania tsaye kallo yayi parking   sai yafito tazo da sauri ta tsugunna tana gaishe shi ya amsa sai ga hajiya yafito wato kanwar mahaifiyar sly sake zama tare dasu tace baban sulaiman ashe ka iso yace eh fa bakuwa kika yi tace mukayi dai dan nima fitowa ta kenan  ance tana nemana......yace wacece tace baka gane taba baban sulaiman yace ina zan gane ta aini ban taba ganin taba zainab tarike kafar sa tana kuka dan Allah baba kayi hakuri ka yafemin.....yace da kikamin me?ay ni bakimin komai ba kawai kitashi kitafi tace baba Alhakin kune ke bina shiyasa bana ganin daidai nida dana dan Allah kayi hakuri yace malam salihu yace naam alhaji yace idan tafita ka kulle min kofar gida ke wuce mutafi haka suka shiga suka Barta  tagama kukan ta sannan tafito............

         🏵🏵🏵

Gidan agyare yake sai tashin kanshin turare wuta da kuma Na girke girke yakeyi......ke shaheeda wai bazakiyi maza ba ki  karasa hada salad din ba lokacin saukar jirgin su sai karaso wa yakeyi fa tace mahmah kije kiyi wanka kawai tunda kune zakuje tarbo su dady ni ay tarbo  yaya shaheed zanje yi  mahmah.........afilin  jirgine su mahmah na karasowa sai ga jirgin su dad da sly ya sauko abokanan biyu ne ke saukowa daga matattakalar banen  jirgin sly dan gaye tafiyar nan da yasabayi ta kasaita sak kamar afaf itadin ce yakeyi ko yanxu tsufan sa baisa ya canja ba sai wani fresh ma dayayi yayi haske sun gama saukowa kenan sai ga motar mahaifin sly tare da yan uwan sa barira dakuma kanwar mahaifiyar su.......suka rungume juna shida da mahaifinsa suna ta kukan murna mai hade da dariya.........suka runguma zasu shiga motan baban sly su wuce gida sai idris yace Sam bazaayi haka ba madam tariga tamana girki dan haka dan Allah kuxo mu wuce gidan gaba daya idan anci abinci sai ku wuce....baban sly yace ayi haka aa mu bari mu wuce gida dai idan kin gama sai ka kawo shi idris yace baba kayi hakuri fa dama baka taba zuwa ba dan Allah muje................sunci din sha sunyi kat sukayi hamdala sannan suka koma sittingroom suka zauna....... nan baba yayi gyaran murya tabude taron da addua yace ba abunda zance maka kai  idris sai addua Allah yayi maka albarka Allah yarufa asiri ya shirya maka zuria Allah yakuma kara budi  na alkhairi.....suka amsa as amin dukan su yace sulaimanu kaga aboki na kwarai nan tabbas idris yacika dan halak  yayi maka abunda ko yar uwar ka dakuka  fito ciki daya bata maka ba yace baba nasan komai yace ya akayi ka sani yace kullum idan afaf yazo sai ya fada min halin da yake ciki idan zaka lura duk ranar da AFAF yazo to ranar sai na dinga kuka.........amma bakomai duk wanda yayi mai kyau kansa yayi ma kai kuma idris nagode da halaccin da kamin bazan taba biyan kaba da irin taimaka min da kayi dakuma dana kajawo shi daga halin kunci da wahalar rayuwa kasashi a rayuwa ta hutu da jin dadi Allah yabiyaka aboki na Allah yabarmu tare.......idris yace amina wai ina shaheeda ne ko shaheed din bai iso  bane?tace aa  munyi waya sun sauka yanxu zaka gansu.....suka juya saboda bude kofar palour da akayi alhaji idris yamike tsaye yace I 're welcome son suka rungume juna sly ya tsura musu ido sai a sannan yaji missing din afaf sosai shi kawai yake marmarin gani. .........sly yace to aydai dan ba naka bane idris yasake shi yace ga babanka sulaiman danake baka labarin shi yace oh sannu uncle ina wuni yace bazan ansaba nima rungumeni zakayi aka kyalkyale da dariya yaje ya   rungume shi sannan ya duka Ya  gaida baban sly sai yakoma kusa da mahaifiyarsa yagaisheta ta amsa tace kaje ciki kayi wanka kazo kaci abinci yace ok mahmah. ....shaheeda tabi bayan sa dauke da trolly dinsa.........suka shiga dakin tace sannu bros yace yauwa tace bros me kakawo min ne yace ke  banason shishshigi daga zuwana zaki fara min surutun ki ba abunda nazo miki dashi daga ahlam sai mahmah da daddy sai kuwa afaf tayi mtsw wane afaf kuma tayaya kasan shi yace bansani ba niko nasan afaf tun muna yara.....tace hmm ni ay haushi yaron ke bani ga shegen girman kai sai ka ganshi ko ya zan bata masa rai baya ko  kallona  balantana ya tanka shaheed yace kekam Allah yashiryeki ni fita ki bani wuri zanshiga wanka......

by rukky😘 *luv u all*
 

           🏵🏵🏵

Duk cikin yan uwan sulaiman bawanda baba yafada ma akan jin saukin jikin sly basu ma san cewa  ankai shi Paris ba tunda ko gidan ba wani zuwa sukeyi ba......

story of an orphanOù les histoires vivent. Découvrez maintenant