WAHALAR RAYUWA

56 0 0
                                    

*UMMIN ABBATEE*😘

           *95~100*

*WAHALAR RAYUWA*😪

  AFaf ne zaune ya gama diban ruwa yakai cikin toilet........ya koma tsakar gida ya zauna ya mikar  da kafaffun sa yana jin matsinan ciyar yunwa gashi su maryam sunyi tafiya sunje buki garin yabo ....... ...anas ne yazo wuce wa wanda kwanan sa uku kenan agidan.....yace Anas akwai abinci kuwa?anas yace eh dazu nagani da yawa a kitchen bari naje na zubo maka yafara tafiya .....afaf yace aa anas dawo nariga naduba babu yace bari natambaya  maka hajiya yana kiran anas din amma yariga yaruga da gudu cikin gida............yananan zaune wurin yayi tagumi yana tunanin baban sa kusan sati biyar kenan baije ya ganshi ba da kuma kakan nin shi mahaifan mamansa fateema suma tun da yaje gida yayi waya dasu da phone din kakan sa bai...........sai ji yayi an rankwashe sa a akan sa tace to sannu cikakke rikakke wato kai wuyanka  yayi kwari KO  wato har zaka iya tambaya ta abinci basai kaje kaciba idan uwarka ce tataso tadafa dakanta  to wallahi kayi nafarko kayi  nakarshe karkaga ka girma  tsawo da tashin balaga na dibanga wallahi baruwa Na sai na maka shegen duka ba uban da ya isa yarama maka kuma..........................

         🏵🏵🏵

Afaf wai kai so kake ko this year ka kara missing waec da neco ne? wani abokin sa ne ke tambaya sa wanda shi yanxu Hathaway admission yana 300level..........afaf yace ba haka bane habu kai ma kasan bada san raina nake rasa rubuta jarabawar nan ba kasan matsalar da nake ciki..... gashi banason fadama alhaji kaka kaga hawan jini ne dashi dama mijin hajiya ke biya yanxu kuma bana tunanin tafada masa.....gashi itace ke jamin rashin rubutawa amma kuma taki karba min kudinn....but nayi alqawarin wannan shekarar insha Allah ba abunda zai hanani rubutawa..............habu yace amma kana ganin bazaka roki head master ba yataimaka maka yace kana ganin zai yarda?yace kadai gwada kagani ............yace gobe da safe zaoshirya sai naje habu yace dadai zaifi maka ...... ....

         🏵🏵🏵

Bayan ya agama aikin gidane ya duba yaga ba kowa a tsakar gida yafito daga dakinsa da gudu yafita daga gate din dan bayaso agansa da school uniform ajikinsa.......Ya isa school Din kai tsaye is wuce office din head master....yay knocking yace yess shigo bayan yashiga ne......Ya gaishe shi  sannan yafada masa bukatar shi na yataimaka masa baida kudin biyan kudin registration ya kalle shi  sama da kasa yace get out of my office!ya tsugunna gwiwowinsa akasa yana kuka yace kataimaka min banason rasa exam din nan sir kataimaka min malamin yace baka da   hankaline dubu ishirin wasa ne ay koni nasamesu inaso wllhi baka san inada nawa iyalinba da kuma nawa Matsalan ba tashi tashi kafita konasa azane min kai anan...........

tun da yafita daga school din yake hawaye yana sharewa sannan yayi alqawarin insha Allah sai he nemo kudin yin exams.........yana cikin tafiya sai yaga wani katon sabon gida kato ana  ginin sa ga ma aikata nan sai kai da kawowa suke tayi. ......yace  ya samu daya daga cikin su yasiya shinkafa da wake yana ci yayi masa sallama suka gaisa mutumin ya kawar da kansa yana cin abincin sa sai afaf ya duka yace bawan Allah dan Allah aiki nake nema wllhi koda kwasan kasa ne komeye ma inaso mutumin da yacika baki da abinci yadago yana kallon sa sai da ya hadiye abincin sai yace kai wuce kabani wuri koso kake kasa abincin yashakeni?......dallah wuce  na ce maka yamike yana shirin ma din afaf sai ga wani mutum mai kakkaurin jiki mai tsawo ga yabude mota yafito yace kai kai meyasa zaka maresa meyayi maka bayan ina kallon ku tun dazu da alama ma rokon ka yakeyi wani abun........yace eh mai gida wai aiki yake nema sai kace yaga nan yayi kama da office mutumin yace to ay sai kace basa baa dauka bawai ka mike zaka mare saba.........kai yaro zonan ya matsa kusa da alhajin yce aikin me kake so yace alhaji wallahi kome kabani inaso zan iya nidai fatana na biya kudin waec dina.......Alhajin takura masa ido yace waec zaka rubuta yace eh alhaji yace ya sunan ka yace sunana AFAF  mutumin ya tsaya ya tsura masa ido yace afaf hmm sunan babanka fa ya ce sulaiman alhajin yace sulaiman anan garin babanka yake? yace eh  Maman kafa?  sai yadukar da kansa yace mamana sunan ta fateema koda nagirma bansan taba ance tana haifana ta rasu ......alhajinn jikin sa ba karamin sanyi yayi ba yace ga card dina ka duba akwai address dina duk lokacin  da kasamu tym kazo. ..yace to alhaji nagode yace nawane kudin waec din?yashiga mota ya zauna sai afaf yace alhaji har dubu ashirin ne alhajin yagado kai ya kalleshi tare da girgiza kai sai yaciro kudi daga cikin aljihunsa yana qirgawa sannan yamiko ma  afaf wasu yace gashi dubu ishirin da biyar ne kaje kabiya kudin jarabawar daga baya kasame ni agida ba kudi  sosai ajiki nane yanxu.......afaf ya tsugunna yafara hawaye yana ta godia mutumin yace tashi kaje kaji kawuce direct kabiya fa dan idan ka rubuta inason ganin result........
 
          🏵🏵🏵

Da murnan sa yakoma school ya biya malamin bakaramin mamakin yaron is bashi ba amma afaf ko kallon arziki bai masa ba daya gama da biyan kudin ne yaje wuriin da ake siyar da waec text books biyu kawai yasamu yasiya.......sai ya wuce mai tsaye gidan su abokinsa habu ya labarta masa komai yata ya abokin nasa murna sosai..... sannan afaf yaroke sa da yataimaka masa suje gidan wasu makotansu ya ara sauran text books din da bai siya yaje ya rubuta sai yadawo masa dasu habu yace kasan hakin usama bai da kirki banaso littafansa su samu matsala gaskia zai iya mana rashin mutunci afaf yace insha Allah ba abunda zai faru zan kula dasu..........haka fa usama kafin yabayar sai da ya ja ma afaf kunne akan ba ruwan shi idan aka bata masa tabbas sai anbiyasa  afaf yace yayarda shidai burin sa yayi karatun jarabawar nan..........sun karba yayi godia yakama hanyar komawa gida sai  yafara jin kiran sallah sai alokacin hankalinsa ya tuna masa  da hajiya da kuma  dadewan dayayi awaje yau Allah kadai zai taimakesa amma yasan sai yasha zagi idan ma bata doke saba kenan. ....yana ta tunanin ne yashiga masallaci yayi sallah yana idar wa yaje wurin wani maishayi abakin titi kusa da M asallacin yace adafa masa indomie ita yake marmari sai dai asakashi yadafa ko kuma adafa yana jin kanshi amma ahanasa ko dan danawa........isar sa gidan   keda wiya  yasamu su hajiya zaune a tsakar gida suna shan iska saboda andauke wutan nepa ...... .....yayi sallama yasa kai  zai wuce cikin gida ta ce kai zonan dan iska daga ina haka rikakke?tashin farko ta wanke shi da mari wato ni zaka mayar mahaukaciya kabarni ina jiran ka ka hada mana abun kari ashe kasa kafa kabar gidan ma to gidan ubanwa kaje yayi shuru kawai yana ta ajiyar zuciya saboda zafin marin da yaji amma saboda taurin zuciya irin na shi  ko kwalla  babu a idanunshi......bada kai nake magana ba takara kai masa wani dukan yace school naje sai alokacin idanunka  suka kai kan littafan hannunsa tace ohhh ahhh lallai  toh fa yaro yagirma ina kasamu kudin makarantar da kuma Na siyan littafan? kafada min ko halin ne ya motsa data kayi ?ta rankwasheshi akai bakajine nizakama taurin kai to bari kagani taja do littafan yana kallo yana rokon ta da tabashi banashi bane  amma haka taya gasu daya bayan daya yarda Hadiza na gefe tana taya ta......itama tayi aure amma  kamar batayi ba kullum tana gida saboda mijin korota yakeyi yace tazo gida ta koyi tarbiyya sai ta koma. .............kukan da baitaba yin irin saba shi afaf yakeyi kamar ransa zai fita jijiyoyin kansa suka fito yakoma daki ya kwanta ya kulle dakin ........................

by rukky😘 *luv u all*

story of an orphanTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang