WAHALAR RAYUWA

51 1 0
                                        

*UMMIN ABBATEE*😘

         *115~120*

*WAHALAR RAYUWA*😪

Bayan tafiyar afaf kullum baa kwana biyu alhaji idris  baije ya duba jikin sly ba.........kusan shekarar afaf biyu kenan da tafiya wanda saura shekaru biyu cif ya kammala karatunsa..... haka ma yau kamar yanda yasa ba wato alhaji idris yaje gidan dan duba sly yana zaune a dakin da sly yake kwance....yajuyo ya kalli mahaifin sly yace baba yakamata afita da  sly kasar waje dan abun nan ba alaman sauki kullum Abu ba ci  gaba......yace banki ta taka ba idris amma wallahi munyi yawon asibiti sosai amma ba nasara gashi shi kanshi abubuwan daya mallaka da yawa haka muka siyar danawa din amma duk dai ba nasara  ikon Allah wannan Abu dai sai addua gashi ni ba aikin nakeyi ba business ne ake dan juyawa dama shine mai kokarin neman. ... yafara zubda hawaye .......idris yace aa baba ai bazaa gaji ba.....kayi hakuri  insha Allah zan bincika wace kasace sukafi kwarewa akan irin wannan ciwon sai nashirya tafiyan baba yace ayi haka idris wahalar sai tayi yawa ay idris yace  haba baba wallahi sulaiman yafi karfin komai aguna Allah Dai yasa mu dace baba yace ameen
.......
          🏵🏵🏵

Haka dai idris yadinga shiga da fice wurin neman kwararren asibiti akowane kasa ne dan yafitar da abokinsa ta.......yayi dace kuwa aka fada masa cewa suje paris da taimakon wani abokin sa doctor akayi musu booking komai na asibiti aka basu date suje nan da wata 3uku...............
        🏵🏵🏵

haba zik so kake kasamin ciwon zuciya kullum ina nuna maka ka dena abun nan da kakeyi amma kamar ina kara zugaka kaci gaba?yace mtsw tare da mikewa tsaye gaskia nifa kina takura min haba ke haka iyayen ki suka yi miki kullum sai kidinga hanani more rayuwa.......tana matsar kwallah tace kai kadai ne dani zik idan yan san da suka kama ka wallahi bansan Ya zanyi da rayuwa bata.....yace to ina ruwan ki...........Assalamu alaikum wata yarinya ce aka yaso gaba wani saurayi nabinta abaya da alama kamar  yayan tane ...... ....zainab(zeezee) ta juyo da kallon ta gare su tare da ansa sallama zik daya gane yarinyan sai yajuya da kansa yana kallon wani gefe.......zeezee yace lafia bawan Allah bangane kaba yace bazaki gane ni ba ay amma muna fukin danki zai gane kan wana dayayi ma fade tadafa kirji  tana salati ta juyo da fuskar zik tace hakane zik?yaushe zaka dena jawo min magana tana girgiza shi ya kwace kansa yace nayi mata fyade ko dai tamin fyade yayan yarinyar ya wankesa da mari ......sai ga wata tsohuwa tafito daga dakin ta tana yamutse fuska tace nifa nafara gajiya da wannan halin naki dana yaronki ace nagama da ke sannan nazo ina fama da danki wannan wane irin balai ne wallahi nagaji.....yayan yarinyar yace au ashe ko kuma kun gaji  dashi amma da alama uwarsa bata gashi da halin saba. ....officer ku shigo sai fa police suka shigo suka daure masa hannu wa suka tasashi agaba........tana ta kuka tana rokon su amma fir sukaki kulata. .....yakoma kusa da Mama ta tace mami dan Allah kisa baki su kyalemin shi.....tace ke ni kyaleni dan Allah nagaji da halinku daga ke har dan naki kullum shida hakamata yafara nemo abunda zamuci amma sai dai nasamo  kuci .........ba zaman dakika zabar muku kenan ba keda danki ba to bismillah duniya ce zata koya muku hankali ay....... .......da azama ta fada dakin ta takira numbern talatu bayan ta dauka ne take fada mata abun da yafaru akan ta ara mata kudi tace tafito dashi zata biyata daga  baya......talatu tace kinsan fa ba kudine dake ba balantana ki biyani daga baya ba...... haka dai zeezee tadinga rokon ta dakyar  tace zata bata 15k dai.....zeezee tace to ganinan zuwa na karba da karfi  talatu tace aaaa karki zo ki bari zan  kawo miki.............abunda akayi tun karfe 10 na safe shine har karfe 3 uku na rana da zeezee taji shuru ta dauki gyalenta ta yafa tafita tatari mai adaidaita ta isa gidan kawar ta talatu .....da isar ta bakin gidan ba karamin mamaki tayi ba saboda ganin motar bazawarin ta da suke shirin yin aure ba da dadewa ba haka dai ta kawar as komai tasaka cikin gidan daidai kofar palour taji murya kamar nishi nishi gashi kuma ana kyalkyalar dariya ga kuma kofa abude gabanta ta faduwa tatura kofar palourn suka zabura suka Mike dan tsorata da ganinta da sukayi ta kurma ihu ta zube nan tana kuka.......talatu ta Mike tana gyara bra dinta tace lafia zaki shigo min gida  ba sallama ba izini dallah malama  tashi kifitar min .........zeezee tamike tace no zakici amana talatu duk amincin da ke tsakanina dake?talatu tayi dariya irin dasu ta yan duniya tace wane aminci kuma ke  har zakiyi magana akan aminci duk yanda mijinki yayarda dake kikaci amanar sa ay bakisan aminci ba....ohhh ko kin manta cin amanata da kikayi kika kwacemin alhaji lawal kin zata  banji haushi bane ay tun lokacin ne na qudira rabaki da duk wani farin cikin ki.....ganinki da nakeyi agidan sulaiman bakin ciki nakeji kamar ya kasheni shiyasa nayi hanyar da kika bar gidan........fita ki bani wuri malama ko kai yah alhaj  akwai abunda zaka yi da ita? wannan da kake gani zata iya kashe ka dan taci gado  karamin aikin tane wannan ba babba ba......yana balla  buturan rigarsa yacire ya ajiye agefe yace ba abunda zanyi da ita kifita da ita nifa a matse nake. .......tace basai na fitar da  itaba idan zata iya zama tagani ay bismillah ganin da tayi da gaske sukeyi zasu aikata iskancin agaban ta shine yasa yafita daga palourn dagudu tana may gunjin kuka...........ahaka ta wuce police station aji gace ta isa tanemi ganin zik fir suka hanata ......takuwa ki tafiya tana ta musu kuka tausayin yanda fateyin kukan ne yasa suka taimaka suka fito dashi taganshi suka basu  5mns .........shikam ba digon damuwa ko kadan a fuskar sa ya zauna yawani  daure fuska yace haka zaki barni zakayi beli na ba tace zik kudin naje nema amma ban samu ba wllhi......ya busar da iska yace tashi kitafi................

by rukky 😘 *luv u all*

story of an orphanOnde histórias criam vida. Descubra agora