story of an orphan

120 0 0
                                    

UMMIN ABBATEE😘
     
          40~45

   WAHALAR RAYUWA 😪😪

Run daga ranar yafara jin ba wadda yakeso kamar zeezee komai tace yayi jiki na rawa yake aikatawa..................

Tayi shuru acikin mota tana zaune a Bayan mota driver na tukata dan yace basai drivern yadawo ba yatsaya tunda badade wa zatayi ba karyayi  wahalar dawowa.......tana ta tunanin ko lafia rabonta da sly tun washe garin ranar da ta iso birnin kebbi baikara waiwayar taba kuma ko ta kira baya pickin daga bayama tazo bata samu batasan meya sa ba tanata addua Allah dai yasa mijina yana lafia.............ta ciro  wayar ta daga cikin hand bag dinta tayi dialing numbern shi baya xuwa har tagaji ta mayar da wayar..........sun iso lafia koda mai gadi ya bude gate din ba karamin mamakin ganin motar sly agida tayi ba dan lokacin aiki ne.........tashiga ta bude side dinta bata damu da shiga tacema abokiyar zaman ta tadawo ba  dan da zata tafi tashiga tafada mata zata je ganin gida amma ko daga kai batayi ba balantana tasaran samun adduar Allah yaki yaye hanya........tashiga ta danyi gyare gyare tasa turaren wuta sai ta fada bandaki dan ta watsa ruwa bayan tafito ne ta shirya cikin wani purple silky material gown tagyara fuska da powder sai ta sa lipstick purple ta fesa turare sannan tanemi karamin gyale tayafa akanta batare da daura dankwali ba sai ta kulle side dinta tayi hanyar zuwa side din mijinta tashiga palourn abude ga takalmi  nace dakuma tagani abakin palourn haka kawai kishi ya dan tsirgo mata Amma  takawar da abun ay itama zainab din matar shice....... ta zauna  a palourn tare da sallama taji shuru takara yi taji shuru sai ta tashi tace wurin kofar shiga bedroom tayi knocking tare da yin sallama.......tadawo palourn ta zauna jiki asabule sai ga zeezee tafito daga ita sai wata arniyar riga jiki duk awaje tana wani girgiza gaba kallo daya fateema tayi mata ta yi saurin dauke kai tace nasame ku lafia nadawo ne shine fa nace bari nashigo naga motar maigidan awaje zeezee dake  tsaye  tana girgiza jiki tace to dakika yi sallama kikaji shuru  basai ki juyaba haba wannan wane irin naci ne mata da miji suna hutawa zaki damesu  fateema tarike baki tare da ce wa toh fa ayi hakuri ay bansa sai yanxu akecin amarcin ba  Bayan  wata 3 uku tayi mata gwalo tafita. ........tabar zeezee cike  da haushin abunda fateema tafada mata. ........takoma daki kamar tayi kuka kai namiji bashi da tabbas kuma bashi da kunya nan yake cewa bazai KO  shiga dakin zainab ba amma duba daga tafiya ta har an sake kamar ma baya maraba  da dawowa ta tunda yaji ni amma ko fitowa baiyi  ba yaganni amma bakomai tashare hawayen ta...................

Shuru shuru sly  yau kwana hudu da dawo warta amma bai shigo mata ba kuma ko da zata je dakin baya fitowa sai dai zainab tafito kuma daga baya bazai shigoba sai dai taji tashin motar sa.........abun tun baya damun ta har ya fara bata tsoro...........shur shuru ranar tanajin dawowar motar sa tayi sauri tafita ta tarosa  yana ganinta ya wani tsuke fuska yana kallon ta tace sannu da zuwa mijin wai lafia kuwa yau sati na  daya  da dawowa baka shigomin ba kuma konaje gefen ka baka fitowa lafia wani abun namaka yace to uwar mita agaban masu gadi zaki tsareni da tambayoyi wane zan amsa miki koni yaron kine bakaramin mamaki tayi ba da kalaman shi saboda irin haka bata taba shiga tsakanin su ba duk zamansu.......tace yi hakuri kawo jakan na rike maka ha kauce yace barshi kawai ya wuce fuuuu yabarta anan tsaye jikin ta a mace ...............taja duk bata jin gwarin jikin ba karamin rashin hankali tashiga ba da sauyin yanayin mijinta...........tana ta hakurin abun kusan wata daya kenan ba wanda ta fada ma dama gata marainiya agarin bata da kowa daga dangin mijinta sai mijinta dama su dangin miji ba dadin su take jiba dama mijinta ne gatan ta gashi shima ya juya mata baya ba ruwanshi da al amarinta..............

Ranar wata asabar tatashi da matsinacin ciwon ciki sai mirgina take akasa tana kuka tun asuba take fama da Abu daya ta samu talalubo numbern sly ta danna kira amma ko yashiga baa  dauka tana ta tayi can aka dauka menene wai ke baki da aiki sai na damuwar mutane tace mijin dan Allah kayi hakuri kazo wallahi bana jin dadi ne cikina keta damuna da ciwo yayi tsaki Toni ina ruwana bakida aiki sai na ci ba dole cikin ki yayi ciwo ba yakashe wayan sa can wuraren laasar ne tasamu ta lallaba tasaka kaya tafito wurin motar ta tace driver yazo yataimaka ya tukata yakaita asibiti................

by rukky 😘 *luv u all*

story of an orphanOù les histoires vivent. Découvrez maintenant