UMMIN ABBATEE😘
35~40
WAHALAR RAYUWA😪😪
Shigan ta kitchen keda wuya talatu ya daga kai tana ta kallon palourn tana tabe baki.......sai ga zee zee tafito sai talatu tayi saurin washe fuska tana dariya...... talatu tace kince akwai labari ince dai ko lafia tace lafiar kenan kedai kifara shan ruwa dai kedai talatu ta dauki apple tafara gutsira tace ina jinki nafa kagu ki sanar dani nan zee ta ce kedai ina cikin matsala wallahi saboda mijina tun da akakwoni ba abunda yashiga tsakanin mu na rayuwar aure ko kwana bayayi agefe na wannan tsinanniyar matar tashi bata barinshi talatu tayi tsuru tana kallon ta zee zee tace menene kike kallo na haka kiyi magana mana talatu tace ay dole nayi shuru ashe wata biyu kenan aure wannan kice min bakisan mijin kiba anya zan yarda to idan halin naki ya motsa yakike yi ko kina fita ne kisamu.......😜 zee zee tace kinji ki ni fa balain son mijina nakeyi ay yanxu bawanda nake muradu kamar sulaiman talatu tace to kuwa dole kimike tsaye idan ba haka ba ko abincin dayake baki nan gaba zata hanashi baki zee tace tabb ay bazai yuyuwa yanxu dai yakike ganin zaayi talatu......talatu tayi shuru tace zo kiji. ................................
Kai fatee na wannan miya tayi dadi haka shiyasa ko ina naje bana iya cin abinci sai na dawo gunki shiyasa wata rana kike horani kiki bani dan kinsan zan wahala tatashi tsaye ta dauko trow pillow ta jingina masa a bayan sa yace meke nan tace santin naka ne yayi yawa mijin wannan irin surutu haka yaciro pillown ya jeho mata ta goce suka kyalkyale da dariya yace amma fa kin samoni da yawa Allah ba santi bane gaskia ne ya daga mata gira tace to nayarda tamiko masa ruwa adan bowl tace wanke hannunka bayan ya wanke ne. .........ta dawo tazauna kisa dashi tace dan Allah mijin inaso naje naga su mama kwanaki tace min baba baiji dadi ba yace haka fa amma kibari muje tare mana tace aaa kaida aiki yayi maka yawa a office kabari kawai naje bazan dade sosai ba ko kwana biyar na samu yace anya kuwa fateema zan iya hakurin rashin ki akusa har Na kwana biyar kaii gaskia da sake ta kwanto a cinyar sa tace haba nawan ay ba nikadai kake daba ga zaynab idan kabini ay munshiga hakkin ta yayi tsaki tamike zauna tace nifa ina nunama yin adalci ne saboda gudun fushin Allah banaso gobe kiyama katashi da shanyayyen rabon jiki nafiso akullum kazamo mai adalci kaji nawan jikin sa yayi sanyi yace naji amma gaskia kwana biyu zakiyi tafara shafa masa gashin gemun sa tace kayi hakuri kabari nayi kwana hudu to yayi kissing kumatun ta yace kin ganki akwai iya kashema mutum jiki wallahi suka tuntsire da dariya.....................
Bayan tafiyar fateema da biyu ne yashiga gefen zeezee dan yabata kudin cefane alokacin ita kuma tagama yin duk abubuwan da suka samo awurin malamin tsubbun da talatu takaita gunsa.........ta burne na murne wa ta kuma shafa na shafawa ta yi wanka da wanda ya bata ba karamin dadin tafiyar fateema tajiba...........yashigo da sallama yazauna palourn sai gata tafito da ga daki kamar wadda aka biyo ...... ita kuma tafitone dasauri saboda kar yaga bata palour yakoma dan bakaramin aikin sa bane.........shikam har mamakin yayi yanda tafito kamar anjehota tafara kwarkwasa tana sannu da shigo wa ango na ya turnuke fuska tamatso kusa dashi wani Abu yaji ya bogoshi shiba kanshi ba shi kuma ba wari ba shidai baikara sanin inda kanshi yake ba.........sai farkawa yayi yana ganin bushi bushi ita kuma zeezee alokacin tafito daga toilet tana daure da towel ga kuma karamin towel a hannun ta tana tsantsame gashin kanta.......ta iso kusa da bakin gadon ruwan kashinta ya digo masa a fuska ya zabura ya tashi tace koma kahuta gwarzon mijina ay kayi aiki dayawa shidai yarasa gane kansa yadaiga yabi umarnin ta kawai............
By rukky😘 *luv u all*
