*UMMIN ABBATEE*😘
*135~140*
*WAHALAR RAYUWA*😪
Tafito waje ta samu saurayin bakowa bane face lawal saurayinta daya kacal wanda yakiyin zuciya yatafi saboda duk wanda yazo baya iya zama saboda cin mutunci da wulakanci da take ma samari amma shi haka kawai ya kasa daina zuwa saboda kullum kamar kara masa sonta akeyi azuciya.......ta karaso kusa da kujerun dayake zaune tayi tsaki....tare da zauna na adaya daga cikin kujerun....yace sannu da fitowa sarauniyar mata.....ko kallo kai ishetaba tafara danna iPad dinta tana chatting tana murmushi yace ranki shidade anwuni lafia ya gida yasu mama tace pls malam bana son surutu kayi magana kaga naki rankaka bai ishekaba sai ka saka min headache......yayi murmushin sa wanda baya daukewa daga kyakykyawan saurayin..........yace Allah yahuci xuciyar gimbiya shaheeda Allah yasamin sonki sosai wanda bansan tayaya zan miki bayanin saba wallahi jinake idan bansameki ba zan iya rasa rayuwata.......tatashi tsaye tace aykuwa kakusa rasa rayuwar ka kai kama rasa rayuwarka ka dan bazan taba son ka ba wallahi.......ni kaga tafiya ta idan kagama zaman shan iskan da kazo yi sai kayi waje .... ....tajuya zata bar wurin nan ta tsaya tsaye kamar wadda akaba umarnin rashin motsi ya karaso kusa da su lawal yamike tsaye yace barka da yamma baba alhaji idris yace yauwa yaro kana lafia yace lafia kalau yace ka zauna yaro........yace keee ta juyo a tsorace yace zoki zauna tadawo ta zauna bakamar yanda ta zauna dazu ba dan yanxu ta zauna ne tare da mika hankalin ta gaba daya agun dady yace kai yaro ya sunanka yace sunana lawal yace sakyau duk abunda yafaru tsakanin ka da shaheeda nagani kuma naji ke tadago kai bakya son shine?idan bakya sonshi meyasa zaki tsaya kina bata masa lokaci da bazaki fada masa gaskia ba?tace dady wallahi nafada masa yajuya gun lawal yace tafada maka malam lawal yace eh baba tafada min amma nine dai bancire rai ba. .....dady ya tsura mishi.idanu yana mai girgiza kai yace ikon Allah ke kuma shaheeda ba haka akeyima mai son ka ba da lallashi ake rabuwa karna kuskura nakara ganin ki kina wani ko bashi ba irin wannan dabiar ay dan mudai wallahi ba irin ta muka koya miki ba. .............tashi kishiga ciki........kai kuma kayi hakuri kaji tunda kace baka cire rai ba to nabaka izini kaci gaba da zuwa idan har ta amince to xan baka auren ta ta duka yana ta godia dady yace ba komai tashi katafi ........lawal yace awuni lafia baba ....... ...
🏵🏵🏵
Alhamdulillah dady na kammala exams dina insha Allah gobe kamar haka ina Nigeria dady yace masha Allah afaf m proud of u wallahi Allah dai yasa ka mori karatun yace amin dady wallahi na matsu na dawo na ganku......dady yace bakomai goben nan kuwa insha Allah yace dady.....dan Allah ya dady Na kuwa yace karka damu jikin dadyn ka da sauki zakaZo ka ganshi......afaf yace nayi missing nashi sosai wallahi shekaru hudu kenan batare da naji koda muryan saba..........yace karka damu son ga mahmahn naku ku gaisa yace to......Helo afaf congrats yace tnk u mama ya gida yace yasu ahlam tace komai lafia wallahi ahlam dake gefen ta tace mahmah bani yaya afaf mugaisa tace ke goben nan zai dawo basai kin karar masa da credit ba afaf dake jin su cikin waya yanata murmushi yace mahmah kibata kawai tace to zoki karba kanwar yaya da sauri ta cafke wayar tace yaya afaf wai gobene zaka dawo yace kwarai kuwa yar kanwas tace kayimin tsarabar da nace kayimin yace ay duk tsarabar kusan takice ma kawai tace yeeeeh nagode bros bye ta mikama mahmah wayar shaheeda dake jin su bata damu da anata ba dan ita dama bawai ma murnan dawowan sa takeyi ba............shiyasa mom bata ma yi tunanin bata ba sukayi sallama tamika ma dady wayar sa ya mike yace bari nashiga ciki tace ok ganinan shigowa nima ...... ..mahmah tace toh gobe muna da bako.....karfe daya zasu sauka yacemin dan haka shaheeda gobe ba shegen baccin nan naki na safe kinaji nako? shaheeda tace meyasa mahmah tace bakiji afaf zai dawo gobe bane tace toh mahmah ni ina ruwana dashi me zan masa tace keko zaki masa komai dan kece zaki gyara masa dakin sa.........ta juya taci gaba da kallon ta Mahmah tace ko bakiji nibane tace Allah yakaimu mahmah kamar zatayi kuka mahmah tace amin ahlam tace mahmah ni mezanyi gobe tace karki damu autana ke tare zamu shiga kitchen idan mungama muci wanka muje tarbon yaya afaf ahlam tace yees mahmah na..........nima bazaa barni abaya ba zan je tarbo kanina kuma abokina shaheed kenan wanda shigowar sa kenan yau friday yashigo weekend mahma tace ahto duk gidan nan waye zaice afaf bai shiga ranshi ba ay sai dai yan adawa.......ya zauna yace ina wuni mahma tace lafia kalau ya hanyar yace nasha hanya mahmah ga yunwa su shaheeda suka gaishe shi ya amsa yace shaheeda taimako da abinci wallahi har jiri jiri nakeji tace ayya sowie bros yace bari na watsa ruwa da sauri kafin ki hado...............
Bayan ya gama cin abinci ya huta wuraren karfe takwas na dare ya fito yasa jins da wata t-shirt yasamu ahlam kawai a palour yace ina mahmah tace mahmah tana side din dady yace ok barta kawai shaheeda fa tace gani anan naje kitchen ne hado lipton shaheed yace aikin kenan anzauna agida ayi aure ankiyin aure sai cinyema dady kayan dady akeyi shine dan samun wuri harda zuwa wani hada Lipton tayi dariya tace kai yaya yau kuma chapter ta kabudo haka karka damu nakusa aure dama ina jira har kayine tukunna yace mtsw yaushe kika bar samarin balantana ma har ki tsayar da wani.....ni kinga tafiya ta zanje naga mata ta tace iyye yaya wannan daukan wanka haka na zata ma mukayi ma yace keee waye saan ki da zai miki kwalliya ya juya yafara tafiya yace idan mahmah tafi to ki fada mata pls....ahlam tace yaya agaishe da anty maryam yace yauwa kanwas shaheeda tace angon mai kyau angon mai kyau yace Allah yabiyaki kema.......sukayi dariya yakoma yazauna tana shan Lipton abunta ......
🏵🏵🏵
WASHE GARI. .........
Bayan sun gama aikin abinci ne da gyaran dakin afaf mahmat tatasa keyar kowa tace atafi tarbo afaf................Helo mutumin kana inane yace ganinan a kofar rini nazo wurin daurin aurene yace albishirin ka yace goro kazo kasamemu a air port yanxun nan .........alhaji sulaiman yace kai idi mekake yi a airport kuma yace kazo dai kayi sauri karka bari 1 tayi batare da ka iso bafa.............(mahaifin afaf bai san da dawowar dan nasa ba... saboda alhaji idris yace ma afaf karya fada ma alhaji kaka zai dawo saboda yana so suyi surprising din alhaji sulaiman dan dama can ba waya sukeyi da afaf ba)............
by rukky😘 *luv u all*
