WAHALAR RAYUWA

35 1 0
                                    

*UMMIN ABBATEE*😘

         *100~105*

*WAHALAR RAYUWA*😪

shuru shuru afaf baije ya kai ma yaron littafan saba sai yatafi gidan abokin afaf habu......bayan Habu ya fito ne yace ah ya karatu yace wane karatu kuma bayan katona min asiri kunxo kun karba littafaina amma shuru baku kawo ba gashi saura kwana biyar afara jaraba wa.........sai a sannan habu yarike kai yace innalillahi dan Allah kayi hakuri ina zuwa bari naje gidan nasu nakarbo maka kwana biyu ban  hadu da afaf ba nazata ma yakawo maka fa.....yace ina kuwa yakawo min wallahi muje tare dan banason kwana kwana suka wuce gidan tare da isar su.......suka samu hajiya abakin gate din gidan zata shiga ciki tadawo daga unguwa.......suka gaisheta ta amsa a wulakance saboda tasan habu abokin afaf ne sosai.......yawuce ciki zasu shigo suma ta dakatar dasu me kuke bukata zaku shigomin gida kai tsaye nabaku izinin shigowa ne???habu daya San halinta sai yace yi hakuri hajiya munxo ganin afaf ne tace nezaku masa yace bakomai caraf makocin su habu yace karya yakeh yi littafaina afaf ya karba tun wancan satin bai kawo min ba gashi yau saura kwana biyar afara exams tatafa hannuwan fa tace lallai biri yayi kama da mutun.....wato dan banzan yaron nan baidai na  halin gadon nan ba kenan to kai yaro kayi ma kanka baka San bakin ciki yake maka ba zaka rubuta exams shine yakarbo maka littafai ina kallon sa yana kinada kurumus sukayi.............azuciye yaron yace wllhi sai na kira masa police idan bai fitomin da littafaina  daga nan zuwa yamma ba......fuuuu ya wuce habu yafisa abayansa yana kiran sunan shi yaki tsayawa.....kai tsaye wurin police yanufa..........Alokacin afaf nacan wurin aikin ginin gidan da alhaji ya sakashi dinga ba flowers ruwa sannan yazuba ma siminti da akayi ruwa...... yanxu kwanan sa shidda kenan dafara wa dan kawai yanason yasamu kudi yasiya ma fahad  littafansa dan yasan yaron akwai gadara da wulakanci......wuraren karfe hudu na yamma ne yana shirin wuce wa gida alhaji kawai yake jira saboda kullum idan yagama aikin  yake bashi kudin sa........ ......sai ji yayi ana cewa yauwa gashinan eh shine ku kamashi Ya  juyo da sauri yaga meke faruwa sai ganin fahad yayi hankalinsa ba karamin tashi yayi ba...........ashe sunje gida da police din shine hajiya tace musu ay baya nan yana can wurin yaron banzan shi amma dai  bazai wuce wannan unguwar ba kuje aiki yaganku nidai ba ruwana kar akara zuwamin bakin gida ..........shine fa suna cikin tafiya kadan kadan acikin mota  suna kalle kalle sai fahad ya hango sa........haka yadinga rokonsu suyi hakuri amma fahad  yace shi baisan wannan na littafansa zai biyasa idan yanason akyaleshi ahaka suka jashi sauran ma aikata na kallo bawanda yayi tinanin taimaka masa dama yaron haushi yake basu saboda yanda suka ga Algaji na ji dashi................motar police na dagawa sai ga motan Alhaji suka taso suka gaishe shi yace ina afaf ko ya wuce gida sukace eh yayi shuru yace toh fa Allah yasa lafia naga kullum sai nazo yake wuce wa gida............

           🏵🏵🏵

Tunda suka gaishi cell kullum dukan sa sukeyi akan yakawo littafan yaron mutane amma sai hakuri yake basu yana cewa wallahi yagasu akayi  shine ni nake kokarin yin aiki dan nasamu kudi naje nasiya masa Na biya shi...........abu kamar wasa dan kawai baida gata  duk sun farfasa masa jikin sa....................habu yaji labarin cewa abokin sa afaf yana cell da sauri yaje gidan su fahad yace meyasa zakayi haka haba fahad yaron nan maraya ne wllhi badan rashin lafian babansa ba baka isa ka wulakanta shiba banza kawai fahad yace kai bakaga abunda yayi min bane duk dadai na nariga na siya wasu amma so nake nayi maganin dan matsita yayi tsaki zai koma cikin gida habu ya jawo rigarsa yace zo nan wllhi sai ka fadamin wane police station kakai shi batare da ya juyoba yafada masa habu  yace kadai ji kunya mara wayo kawai Allah sai ya sakama afaf wllhi..............fahad yace kuma sai yasha wahala zanje asake shi saboda gobe bazai kara yima kowa irin hakan dayayi min ba....

            🏵🏵🏵

kwanan afaf biyu kenan a cell wanda kullum sai habu yaje yakai masa abinci.......shuru shuru alhaji baiga afaf ba sannan idan. ya tambaya masu sauran aikin kullum ansa dayane basu sani ba.......akwana na ukune  daya tambayesu sukace haryanxu shuru ba labarinsa gashi bawanda yasan gidan su.....bayan alhaji zai wuce yashiga mota ne sai daya daga cikin yabi alhaji har gun motarsa yake shirin shiga ya tayar........yace alhaji gaskia naga bazan iya munafurtan kaba  anan wurin kowa haushin yaron nan afaf yake ji amma gaskia yanxu nidai banajin haushin sa sai ma tausayin sa tunda naga tsanar da muke masa zai iya sakawa ya mutu batare da ansan ina gawar sa take ma.....alhaji yace mekake nufi ne kafada min ka dena wannan kwana kwanan...yayi shuru alhaji yace kafada min mana.. yace to alhaji yaron nan dai police sunzo sunkama shi yana ta basu hakuri amma abanza dan kuwa sai da suka tafi dashi to tin daga ranar bamu kara ganin shiba......alhaji yayi salati yace da girman  ku kukeyin irin wannan dabiyar yamxu dai banma da time dinku awane police station ne yace toh alhaji nadai ga kamar antubuta gwiwa lowcost shine nake tunanin kila shine nakusa da mangwara road ne alhaji yashiga mota kawai ya tayar ya wuce dan yagane kwatancen............yashiga yace yana son ganin ogan su kai tsaye suka mishi izini shiga bayan ogan yayi  umarni dasu shigo dashi  yashiga sai ganin nayi sun taba suna gaisawa tare da yima juna dariya alhaji yace nazone akan case din wani yaro mai suna afaf......inspectr yace afaf? zauna dai tukunna bari nakira nace su duba ko anan ne......bayan ya kira waya minti biyu sai ga srngent   ya shigo tare  da sarama ogan shi sai ya bashi umarni da yaduba sunan wani yaro afaf  a list din wadanda ke cikin cell........after 5mns da fitar sa sai gashin ya dawo.....yace akwai sir kwanan sa kusa hudu kenan alhaji yace shine fa ogan yace je kakawo shi.........aka turo kofar afaf ne jiki duk a fashe sai  kace wanda yayi sata duk sun fara masa jiki bakyan gani alhaji ya mike  yakamo hannunsa yace afaf me ka aikata haka hawaye nabin fuskarsa yace bakomai alhaji kaddara ce alhaji yace wace irin kaddara sata kayi kome afaf yace aa alhaji nan dai yafada masa komai shi kansa inspctr saida jikin sa yayi balain sanyi saboda yaga ba. wani abu yaro yayi ba amma anyi masa irin wannan horo haka......alhaji ya juyo sai fara masifa yace kayi hakuri alhaji wllhi basu kyau  taba amma dan Allah afuwan yanxu me wuce da yaron kawai kai kuma sgent kaje kakira wanda yakarbi yaron nan yasaka who a cell sannan da wanda yayi masa wa nan illar
........

           🏵🏵🏵

Alhaji ne  zaune a palourn sa yajira a kira masa afaf wanda tin da yafito dashi daga cell yawuto dashi gidan sa yanaso yaji tarihin  yaron..........sai can sai gashi ya shigo da sallama shidai yaron nabashi mamaki kamar sa tayi yawa DA abokin sa shidai yaron yashiga ranshi sosai har yakaraso kusa da alhajin yazauna yace ina kwana alhaji maganan da takatse ma alhaji daga tunanin daya lula kenan......yace yauwa afaf ya gajiya yace Alhamdulillah Alhaji nagode sosai da karamcin ka Allah ubangiji yasaka maka da alkhairi Allah yasa kagama da duniya lafia.....alhaji ya dafa kansa yace ameen afaf kasan me nakeso dakai yagirgiza kai alhaji yace yauwa  so nake naji tarihinka ina iyayen ka suke meyasa kana cell amma basu samu dasu neme kaba???ya share Sudan fuskar sa batare da bata lokaci ba yaba alhaji  labarin komai tindaga wanda haihuwarsa da babansa yabashi labari har wadan da yata fuskanta da girman sa........ ....alhaji ya shiga girgiza kai tausayin yaron yashige shi ainun .....alhajin yadago kai yace maman ya sunan ta yace sunan ta fateema babana kuma sulaiman wasu na kiransa da sly!alhaji ya zabura  yace zaka iya kaini wurin babanka naganshi?yace ay baduwa alhaji zan kaika..

......
BY RUKKY 😘 *luv u all*

story of an orphanTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang