Part 1-5

9.2K 403 4
                                    

ARCH. ABBOOD DAWOUD

NA
UMMKULTHUM AHMAD
(@divaa_doveysdiaries)on wattpad and instagram. Please follow, like, vote, comment and share

The beginning of ABOOD DAWOUD..

EPISODE (1)

1St September,2017.. Inspired.. At a sallah BBQ..

Zaune take a gun da kidan yake tashi, yana ratsa duk wata zuciya tare da nutsuwa.. kowa ka gani yana ta harkar sa a BBQ din,saboda duk yan uwane yara da manya se yan abokai da kawaye da ba'a rasa ba.

Gida ne Wanda ya gaji da haduwa da tsaruwa,ga shukoki ko ta ina sun kawata gidan hadi da gardens na flowers da kuma na fruits .

Ga wata kwanttacciyar grass carpet dake a walk ways na gidan,a bayan gidan ake party din. fitulu sun wadatu a gun amman saboda party din ya fi dadi se aka kashe wasu.Dan hasken kadan ne, Wanda in basu yan uwa ba,da suka San Juna ba lallai ka gane mutum ba kai tsaye saboda karancin haske a gurin ....
Tables ne Marasa yawa aka saka tare da kujeru..

Mutane na zaune a kujeru wasu suna kasa amman  kowa da abun da yake.

Lebanese ko kuma nace white's sun fi yawa a gun, hakan ne yasa atmospheren ya cika da smoke din cigarette..

Ga dan kamshin Suya kuma da yake ta fitowa daga dan gurin  da aka zagaye da bamboo sticks...aci gaba da gashi suya se yau sallah ..

Guy din da yafi daukar hankalinta, yana zaune daga gaban speakers, akan irin shaped woods dinnan da ake deco dasu,sanye da wata raw sholey wadda baka gane colourn ta saboda duhu,saidai kyallinta kawai..ga wata hula da ya sha me kyau akan kyakkyawan gashin shi da yadan taru kadan,kai daganin hulan kasan se Dan Alhaji da hajiya..

Kafan shi daya  kan daya,Wanda takalmin kafar shi kadai ya isa ya nuna ma mutum tsadar shi ko daga nesa.

Dadin sautin na Dan daukar shi ,haka ne ma yasa yake ta girgiza kai a hankali.tare da kora kwalbar ruwa na nestle dake  Hannunshi.

Cousins ne yara da manya,aunties da uncles da parents dinsu mata..

Hakan ne yasa dakwai dai daikun mutane a tsaye a inda aka bari ya zama dancing ground.. inda wasu hira kawai suke wasu kuma rawa

Zaune nake da walk way a tsakiya, shikuma yana daga right  side a kasa a gaban DJ. Kallon shi take sosai Wanda har yasa  aka zo da tray da drinks akai dan ta dauka amman bata kula ba.

"Oh my.. "
Tace sanda wani ya tsaya a  gaban shi suke magana.. Mutane ne kuma suka fara zuwa kan grass carpet suna rawa, a hankali ta daina ganin shi saboda mutane sun rufe shi..


Hankalin Naadi ya Kara tashi sanda take ta mike dan dogon wuyan ta tana leke leke Dan ganin ana ta watse wa amman bata ga awesome ba. Sunan da tasa mashi kenan..

Itakam tana fatan sake ganin shi ko da kuwa a mafarkin ta..
Mutum ne ko ba mutum ba ita dai tana son  sake ganin shi..
 
*********
Late Alhaji Abdulhameed lawan,dan asalin garin Katsina ne tsohon attajiri Wanda zama ya kawo shi garin kano,shine mahaifin su naadi.

Mu'aaz Dan shekaru (29) shine 'da na farko gurin Alhaji abdulhameed yana da degree dinsa a fannin public Administration Wanda ya hada a jami'ar Oxford university dake london sannan yana aikin shi a NNPC.

Sai muhammad (24) yana kokarin hada degree dinshi na biyu akan international relations a university  of middle sex. dake Dubai.sai Naadiyya (22) tana nan a baze university dake Abuja a final year inta. sannan Kanwarsu yusra yar shekaru (13) ita ma tana prime college anan kano.

Abban su naadi ya rasu tun yussy na da shekaru 6 a duniya.

Mahaifiyarsu mommy zainaba macen kwarai, mace me kamar maza ita ta cigaba da rike yaran ta. tare da musu duk wata dawainiyar su da kuma sauran abubuwan bukata. Ga tarbiyar da suka samu me inganci a gareta.

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now