ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
19TH APRIL.2019
105-110
_________________________________
Hello lovelies ..ya kuke ,sorry kun jini shiru .abune ya sameni wallahi shiyasa...but today the 18th of April 2018 became
a day to be added to my Diary.its just an unforgettable day in my life ..thats why i decided to give this and wil give
another one so long happiness is concern..(MY HAPPINESS) (03) #ifyouknowyouknow
__________________________________
Dan ko a lokacin ma kallon junan su suke a sace .dayake dai babba babba ne Papa yana lura da su.A ranshi yake tunanin
yadda za'ai a raba su.nan take ya kudire a ransa dole su san ydada zasuyi tun kafin abun yafi karfin su a gaba.sallamar
faa'eey yayi ta tafi taje ta kwanta dan har a lokacin jikin ta bashi da karfi ko kadan.tana kallon Ash ta wuce ciki
Shigar ta daki yayi dai dai da sallamar Ash shima ya tafi gida cike da kewar babyn shi.koda ya isa gida seda ya fadawa ya
ishaq yadda komai ya wakana.shidai yaya dadin shi daya ba wanda ya taba lafiyar kanin nasa.sannan kuma zasu jira suga
yadda Papa zeyi tunda har ya karbi numbern Abban su ..Allah dai yasa alkhairi ya biyo baya.
__________________________________
A dakin turaren ta ya addabe shi ,kamshin ta ya isheshi.wani irin sanyi ne da turaren me saka natsuwa da kwantar da
hakali.amman a wani bangaren tada hankali yake kamar dai yadda ya tabbatar koma mene za'a yita ta kare.bari dai ta dawo
hanyar da shari'ah ta yarje mai.
kwance yake sanda wayar shi ta kada .dubawar shi yaga nabeel ke kiran shi.dauka yayi da murmushi a fuskar shi sannan
ya fita daga dakin ya koma dakin da naadi take.da dariya Nabeel ya fara yana fadin.."ya zama ya zama ya zama.."
Dariya Abbood ma yayi yana cewa .."bud mana,se kace wata mace?"
cewa Nabeel yayi .."ah ah ba mace bane ,amman ai ka zama na macen..hope komai went smoothly?"
kallon Naadi nabeel tayi wadda ya lurata kasa kallo shi da ya shigo.kuyan kanta take yadda ta zaqe tayi kissing dinshi
.oh ita kam yanzu da wani ido zata kalle shi..
Fita yayi daga dakin yana girgiza kai sannan yace wa Nabeel.."nothing happened munafuki.se kace ni na maka irin wannan
binciken ,shine zaka bi ka isheni.." Dariya duk sukai abunsu sannan Nabeel yace .."base ka zage ni ba fa,nima ina da
mata .remember?,so abunda kake so ka boye man na dade a system din kaine farin shiga ..lastly kazo ka karba breakfast
dinku a waje,zan ajiye gun guardman na juya.."
Jin hakan da Abbood yayi ne yasa yace.."Ah ..please wait mana ,ka shigo let me talk to you.."
.."okay.." Nabeel yace shortly ya kashe wayan.
YOU ARE READING
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...