190-195

784 86 4
                                    

ARCH.ABBOOD DAWOUD

       NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03

30TH NOV, 2019.

190-195

_________________________________

Wannan abun da ya ya ishaq yayi masu ya dagula mata lissafi kwata kwata ..a zaune take a kan yar couch a nan sit room din.shi kuma yana tsaye a kofar daki yana kallon
yadda ta ke ta kallon kasa kamar wata muna
fuka.ita kuma harda kunyar rashin arzikin da tayi masa.yanzu kwarjinin sa ya mamaye gidan ma baki daya ta kasa tabuka komi..gashi safiya har yanzu ..cikin isa da kasaita
ya tsura mata ido wanda jikin ta ya bata itan yake kallo..

Zamo wa kasa tayi ta tsugunna sannan tace .."Ina kwana.." A hankali ta furta amman yaji ..se kawai yace mata .."Lafiya .."  Juya wa yayi daki .me yayi Allah masani.sannan
ya fito daga gidan ma gaba ki daya ya barta ita kadai ..Zama tayi ta hada tagumi.tun tana jiran sa ya dawo har ta gaji ta tashi ta fara gyara sit room din.chan tayi kitchnet
dinsa tana dan dubawa.shima ta gyara ta wanke cups wanda sune suka fi yawa da tea spoon wanda yake shan warm water da lemon se kuma na coffee ko tea..

cups din da lemon din yake da yawa take kallo.wanda ta kwana da sanin cewa ko a gida in tana period da yawa yana shan wannan lemon din..ga ma kwallayen nan a cups din
wannan ya nuna mata yawan shan lemon da yake yi kuma shi lemon yana karya tasirin sha'awa ne ..Nan jikin ta ya mutu kwarai.fridge din shi ta duba taga lemon da yawa a
ciki..hawaye ne ya silmo mata daga idanun ta .amman nan da nan shaidan ya sake zuwa ya tuna mata cewa kefa kinji ance Baby fone is ringing..Nan ta cire ko wani tunanin
ta gyara mai kitchen din tana kara hawa kan bakan ta na yadda da abunda tai.

tana gamawa da nan se tayi zamanta da wayar ta tana danne danne..Chan se gashi ya shigo da leda biyu a hannun shi ya siyo mata abinci .se yan chops haka ya kawo mata
a gaban ta ya ajje sannan yace mata .."Eat.." .yana fadar haka ya juya ya sake fita.nan ma be dade ba ya dawo inda ya same ta taci dan snack kadan ta sha coffee din.

Daki ya nuna mata in tana son wani abu duk ta birkita zata samu.ai kuwa nan ta shiga ciki ta tafi toilet.shima toilet din ba tsari dakin ma haka.da haka dai ta samu
tayi kurari wanda daman ya dame ta.sannan ta nemi detrgents ta wanke toilet din sannan ta fito.Thank God ma bata sallah.

dakin ta dan kimtsa sama sama wanda daga nan ta bude dan karamin trolley din ta ta shirya kanta .a lokaci irin na yanzu daman ingila sanyi ake.so ta saka sweater ta samu
ta kwanta tana jiran shi ya shigo.amman shiru kake ji .shi kuwa daman da dare yake flying amman se yayi tafiyar shi tun lokacin kusan 3pm.

haka ta karaci jiran shi har tayi bacci ta tashi tana jiran shi be dawo ba.dare ya fara yi haka taji tsoro ya fara kamata ..amman dai ta daure ta share .wasa wasa
har washe gari dai bai zo ba ..se chan wajen 10 da safe se gashi shi da Ya ishaq din sun shigo.ba yabo ba fallasa ta gaida su.wanda tsabar fargaba ke cin ta .

Zama sukai inda shi kuma Ash ya wuce kitchent din da yake gano su suma suke gano shi daga ciki..Ya Ishaq ne yace taje ta hado musu suyi breakfast duk da ma shi ya ruga ya
yi nasa .

Tashi tayi kamar mara laka ta isa kitchnet din tana kokarin taya shi me yake yi..Kasa ta tsugunna tace masa .."Ina kwana .."

A hankali ya amsa dai dai kunnen ta kamar yadda ita ma tayi gaisuwan dai dai kunnen shi ..tashi tayi ta rasa me zata ce masa.kawai se yaga kwalla a idon ta kadan..
for the first time yaji ta bashi tausayi tunda sukai fadan nasu..Amman se yayi kamar be gani ba ya wuce ya bar mata ta karasa ,A hankali hawayen ya samu damar gangarowa
ya sauka kan fuskar ta.

A nan ma kuma se ta shiga tunanin inda ya tafi ya kwana.kenan daman haka yake yi baya kwanan a gidan ,ko dan tazo ne ..Nan brain dinta ta sake juya wa..se kawai ta sake
juya wa kan tunanin cewa mijin ta na neman mata ya baro ta chan tana fama da kewa da bukatu iri iri.se kawai ta sake daure fuska .Ko da ta gama ta fito wa da kowa cup
of coffee da tray inda ta zubo already banana baked chocolate chip bread wanda yaji honey sannan kuma doughnot ta ajje musu .

Sha sukai duk shiru .shi kuma Yaya yana kallon su yana observing dinsu .yana kuma lura da duk abunda yake wakana tsakanin su.ya lura dai duk suna kan dokin zuciya duk
da ma shi Ash ne ya fidda maganan saboda yana neman gyara a lamarin,amman duk da haka ya wani sha kunu ya daure fuska .sedai fa duk da wannan mazuran da yake yi kama
kallon cikin idon shi zaka fahimci tsantsar soyayyar matar tashi a kwance luf luf a idanun shi..

Shi dai yaya coffee kawai ya sha sannan yayi gyaran murya ..

Ko me ze ce masu ? se mu hadu a next page .kuyi hakuri da short pages dina .naga inna ce se nayi 5000 words dinnan bana samun dama sosai ne .dan se na dade ina typing
saboda yananyin aikace aikace na.

TBC........................

ABBOOD DAWOUD ✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora