ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIESWATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
19TH NOV, 2019.
165-170
___________________________________
Assalaam lovelies ya kuke duka ,kuyi hakuri jina shiru da kukai.Exams ne ya sakoni gaba,na gama amman har yanzu banji na huta ba.i hope ana mun uziri har ila yau?
.Na gode.__________________________________
Kwanci tashi ba wuya se gashi har Ash ya samu one year yana flying,cikin wannan one year din abubuwa da yawa na alheri sun faru dashi wanda yayi mugun suna cikin
dan kankanin lokaci.hakan kuma yayi dai dai da faa'eey wadda keda sauran shekara daya cif ta kammala nata karatun.ita ma ta dage ta daga hankalin ta.hakan ne yasa
da ka ganta zaka ga kamar wadda bata samun hutu kwata kwata,har fada mammy taka mata akan ta rage wannan zafafawar akan karatu.Ita kuwa faa'eey gani take ya za'ai ace tana mace mijin ta yafi ta dagiya,ai yadda kowa ke alfahari da shi haka ita kuma take so yayi alfahari da ita.wannan ne yasa
tace she will never give up.so kullun cikin karatu taka tana making researches kan duk wani abu da ya shafi karatun ta na Law.A bangare guda kuma kewar mijin ta ta fara mata yawa saboda yanayin aikin shi kullum baya nan .tun tana dannewa tana hakuri har yakai ya kawo ta fara masa kuka in suna
waya.dan bata iya jurewa ,faa'eey irin matan nan ne masu zafin bukata,gashi kuma irin sune basu ma kawowa da wuri ,ko da ma shi Ash yasan halin abarsa kuma hakan be
taba damun sa ba.saboda tun be san yadda zeyi da ita ba har ya kai ya kawo ya gane kanta ya kuma san duk wata hanya da zebi da ita akai har inda ake so akai.Shima akan kan shi yana tausayin ta,amma aikin shi ne ya takure shi,kullun cikin yawo yake a sama kamar wani tsuntsu ko direban adaidaita sahu.ita kanta faa'eey tana
masa uziri kuma tana tausayin sa ,amman rai da jiki da tsoka da jini,dole tana bukatar kulawar mijin ta.kuma tun kafin ma suyi aure tasan it was his dream na ya zama
pilot,gashi ya zama amma ta lura hakan na neman kawo mata cikas.Ana wata ga wata ,dan se gashi Ash ya samu wani contract wanda ya maida shi chan yankin su K9 .Nan fa hankalin faa'eey ya tashi ta runga kuka tana cewa bazata iya ba.wai
a cewar ta sedai in tabar karatun ta bishi dan wallahi bazata iya ba,cewa tayi toh yana nan kusa ma ya aka kare baran tama yayi mata nisa,ita gaskiya bata yadda ba.A wannan lokacin shiru yayi mata saboda yasan ma wasa take tace zata bar karatun ta ta bishi ,duka duka saura how manay months ta kare ,be fi saura 8 months ba yanzu,
se kawai ta bar karatun da ta kwashi shekaru tana yi dan ita tafi kowa .A wnnan lokacin saura 2 weeks ya bar kasar Russia ya nufi su K9 ne .so harkoki kadan ne suke
sa shi fita daga gida,ita kuwa Faa'eey tayi wani irin fushi.A cewar ta baby A baya son ta kamar yadda take son shi,kuma wai be damu da ita ba kamar dai yadda ita ta
damu dashi.ta kara da fadin da ace ya damu da ita da bazai taba yadda ya tafi ya barta ita kadai saboda tana karatu ba.Wasa wasa se faa'eey ta fara dena kula shi,ta share shi bata wasa da shi kamar dai yadda suka saba.
Yau ta kama Saturday faa'eey ta tashi tayi musu Veges stir fry da chicken biryani.tayi wankan ta tayi kwalliyar ta cikin wata gown so simple me kyau,ko kalar kawai
ta karbi jikin ta.gashi ta fidda duk wata suffa da sura ta jikin ta.sedai fuskar ta kawai zaka kalla kasan cewa bata cikin sukuni.Haka nan taje daki ta same shi yana
waya ya fito ma daga wanka.ruwa ne a warwatse a bayan shi wanda yake kamar tudu da kwari.ga wani kwanji nan ya wani ya murde .Kamar yadda yake a aladar ta tsugunna wa har kasa in zata mai magana,haka tayi cikin ladabi da sunkui da kai tace .."Baby A breakfast is ready.."
Ta cikin Madubi yaka kare mata kallo,ba karamin kyau ta mashi ba.kai shi tun daga shan kunun ma nata yayi masifan kara mata kyau.Dan shi ze iya kirga sau nawa yagan ta
a irin yanayin shan kunu.Faa'eey wata irin yarin ya ce me hankali da natsuwa.gashi taiya bawa babba girman shi.bare Mammy da kullum cikin tuna mata take tabi mijin ta,
ta bi mijin ta.so wannan abun kullun yaki fita daga kanta.se akayi sa'a shima Ash baya cika yin abunda ze sa har tayi wani rashin kunya ko wani haukan,sanyin hali gare
shi.kuma ma dai Soyayyar faa'eeyn is his weak point.duk Abunda ya hado da faa'eey ji yake kamar an kashe mai jiki da shi.
YOU ARE READING
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...