275-280

847 88 4
                                    

ARCH.ABBOOD DAWOUD

       NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03

4TH APRIL, 2020.

275-280

_______________________________________________

Abunda ya hada faa'eey da Abbood shine faa'eey bata son gyara kayanta da kanta ,daman chan ta saba Baba kulu ne ke mata ,shi kuma Abbood in kun tuna baya daukar masu
aiki,so in that case Abubuwa sukayi wa faa'eeyn yawa ,Ga aikin gida ga aikin ta ,tunda ta cigaba da aiki,hakan ne yasa tayi fushi akan maganar gyaran kayan da ya mata
domin har ce mata yayi kazama akan hakan,wannan abun ya mata ciwo sabida ita bata da kazanta kuma bata son ta,shima kuma ya sani,amman ya mata wannan sharrin na kazanta
kuma duk da rashin gyara kayan ta ,bata taba tara undies din ta,da tayi wanka da ta cilla ciki machine tas abunta..Gashi yaki barin me aiki,sannan kuma har yanzu yaki
bar ta ta tashi daga gidan,wai tunda tana zuwa aiki gwamma su zauna da Naadi ko ba komai in ya shigo gidan ya samu abinci..

Wannan shi ya haddasa samun sabani a tsakanin su,ta tuna sadda take auren Ash ,kayan ma wani lokaci shi yake gyara mata,dan kai tsaye take gaya masa tace ,,"Baby A wlh
na tsani gyaran kaya ,haushi abun yake ban.."  Se yayi dariya yace mata .."Kin tuno sadda in muna waya kan auren mu kike kuka kina gaya mun cewa Mamy ta saki gyaran
kaya kuma ke bakya so?"

Ita kadai take dariya tana hawaye ,Tabbas tana missing Ash din ta sosai ,Tana masa mugun so,tasan harta mutu yana ranta,he was her first love ,duk da ga Abbood kuma
tana son shi,amman fa maganar Ash daban take a ranta,Ash is a no go area..

Haka sukai ta wannan fushin kuma har bayan ta daure ta gyara kayan nata ,wanda ba wani gyaran arziki ba ma,kayan guga ne in aka kawo ,haka zata lafta su cikin wordrobe
din ta,wani lokacin ma yadda aka shigo mata dasu haka zata barsu a inda suke ,se suyi kwana biyu a hakan bata taba ba,se kuma gun ciro kayan a wordrobe din ,duk yadda
ta samu haka kawai ake zaro su,shi kuma Abbood baya son haka,wordrobe in shi kullum tas take a gyare kamar ta mace ,shine ai kullum se yace mata .."Wannan wordrobe din
taki ni ya kamata ace tawa ce ,tawa kuma taki,um um amman abun ba haka yake ba,kullum wordrobe dinki a hargitse kamar ana yaki cikin ta,"

Se wani abu da yake alfahari da faa'eey na cewa duk fushin da zatayi dashi in sunyi normal fadan ma'aurata,kome ze ce mata bata taba musawa ba ko ta daga masa murya.so
a hakan se yake gane cewa Allah baya hada wa mutum daya komai,misali ,ita naadi na gaya masa magana ,amman tana gyara kayan ta ,sannan ita faa'eey bazata taba gaya masa
magana ba,kayan kuma bazata gyara ba,haka ta bangarori da dama kowa da arzikin sa kuma kowa da rashin arzikin sa..

Abunda nake so mata su gane ko dan zamanin da muke ciki yanzu shine .Misali ,kece kike da aure ,kuma kike da kawa matar aure,kullun in tazo miki,ko kika je mata se kiga tana
cikin wadata fiye dake ,se ki runga jin ina kece hakan.amman baki sani ba,duk da wadatar da take ciki,tayiwu mijin ta baya mutunta ta,ke kuma naki mijin ba wadatar
sosai,amman yana ganin mutumcin ki.

Sannan se kiga mijin ta na mata wanki da guga ,ke kuwa naki mijin ba yayi ,misali .Amman ke baki san me take masa ba da har yasa yake mata gugar,kamar yadda ke kuma
mijin ki a bashi da kudi ze kaiki ko ina a yar motar sa ,ita kuwa ga kudin da motocin amman se dai tayi ta yawo a Keke napep.Little knowledge shared ,kuyi nazari a
kan hakan ,kuma ki daina dora ido akan abunda kika gani a gun wata ko wani,tsaya iya naki,kita Gode wa Allah..

*******

Wannan fadan ya dauke su har one week,meaning ko kwanan ta ne se dai suyi bacci kawai ,in ta tashi tayi breakfast din ta sannan ta wuce aikin ta ..Ran da abun ya isheta
ta duba taga ai itace Mace,kenan gwamma ta lallabashi su shirya tunda ko ba komai Al'jannar tace take tangal tangal..(Note,mata da yawa suna manta cewa aure ibada ce,sannan
duk abun tsiyar da miji ze miki in kika maida komai ba komai ba se kiga kin samu al'jannar ki,sannan komai kike a gidan ki ki runga tuna cewa dan Al'jannar ki kike yi,
dan maza da yawa in banda wannan dalilin basu isa su runga wulakanta mata ba,Amman da yake Allah yana gani.Allah ya gyara ya daidaita mana Al'amuran wannan zamanin ..

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now