ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIESWATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
7TH APRIL, 2020.
285-290
___________________________________________________________
An daura aure anyi reception na masu kudi da wadata.izuwa yanzu mutane da yawa sun gane cewa su Daddy A da N taimakon ayin Allah suka saka a gaba,dan wannan recption
din ma da akayi sun buda shi ta yadda ko ta hanyar ka biyo aka ganka za'a miko maka pack,su kuwa bakin daurin aure ma se ka zabi me kake so,in kuk=wa kace komai ne toh haka
za a zubo maka tunda dai Allah ya hore.Ran da aka daura auren akayi dinner da daddare,diner da ba'a kai ta ko ina ba,A cikin gidan akwai wani zabgegen hall da sukai musamman dan taro..duk da a cikin gidan
yake amman bangare daban,Yan dinner zasu zo dinners su kuma ba ruwan su da main house,sedai duk mesn ya bulla main house ze iya,akwai wata yar kofa daga bayan Hall din,wanda
tanan ne yan gidan suke shigowa cikin gun..Wannan dinner gidan maza ce ,dan Haka Umaima da soffy suka ci gayun su suka zo akayi dinner,duk da ma Umaima tana jin kunya ta kasa sake wa a gun dinner din,toh in akayi
la'akari da yadda Maaman ta take aure a gidan,se kuma gashi itama aure ya kawo ta gida daya da maman ta.Hakan yasa tayi ta nuku nuku ,har aka tashi daga dinner din,gashi tunda aka daura aure basu dan kebe da Ango ba,hidima tayi masa yawa ne sosai.Ana ta hidimar reception
ana gama ta kuma aka hau hidimar Dinner.baya ga cewa Ango Ameer shine babba a gidan ,daman kuma duk wani babban Namiji a gida shi ake bari da duk wani hidima da ya taso,
seda irin wayyannan dinnan da basu cika magana ba,dariyar ma basayi,su miskilaye ne,in an gaishe su ma basa amsawa ..Amman shi Ameer daban yake ,ba ruwan shi abun sa
ya gado Daddy A.Dan ko Daddy Nabeel ma yana da yar kyuya ,shiko Abbood ba ruwan sa.daman tun zamanin samrtakar su ma shike musu dahuwar Indomie,shike hado su coffee ne sannan
shi yake gyara masu kayan su,amman badai Nabeel ba.Shi yasa ko yanzu yaran in suna son Abu sedai Daddy A,wani lokacin ma Haka Daddy Nabeel ze hana,dole a hakura.Rayuwar su gwanin dadi..
_____________________________
Dinner wadda ta kayatar sosai Maasha Allah,Hall din wanda yasha decoration se ka rantse wani tangamemen Marque ka shiga,anci uban naira a wannan biki,kuma duk da
wannan kashe kudin fa ,ba wai sunyi Almubazzaranci bane,Ah ah ,sunyi iya karfin su.amman fa kunsan iya karfin sun kuma ba magana bace ake ta wasa..YawwaYadda dinner ta kasance ,yanzu zamani ya karo wulakamci,an samu sauyin abubuwa da dama,ba kamar zamanin su Daddy ba.Da aka tashi an ware bangaren kakannin su wanda suke nan
har yau ana dama wa da su tunda ba wani turkushe wa sukai ba.har yanzu da lafiyar su da dan sauran karfin su.Duk ciki ma Dada ne yafi tsufa,tunda daman Dada ya girmi
Ammi nesa ba kusa ba,so shi ga shekaru sannan ciwon Suga wato diabeties da suka taimako wajen nuna tsufar shi ..Bangaren iyayen su ma Daban..Su Dadday A ne da Daddy N,Ga Maama Naadi,fa maama faa'eey,ga Maama Ameena,se Mommy Hafsatu (please im sorry na manta sunan Amaryar Nabeel
da na bata tun farko,sesa ma nayi ta regarding din ta as Amarya,amman an bata hafsat yanzu..) se Papa da Mamy Da wasu Aunties din su faa'eey din se kuma ta bangaren
Baban Umaima ,Marigayi Daddy Ashraf..wato su mommy Hibba ,mommy Jaab ne da yawan su dai daga dangin baban ta wanda aka ruga aka zama daya..ko da yake daman anyi auren
Yar wajen Daddy ishaq shima batayi 5 months ba ma,duk da a 15 ma akai mata aure tunda ta nuna shi take so..Haka bangaren sisters da brothers ,cousins da friends din su ..
Amarya da Ango suka tako suka shigo an saka musu kida ,Amarya da kawayen ta haka ma ango,isarsu mazaunin su MC din mu da ta kasance Mace a wannan karon se ta tsayar
dasu ta sa su yin game,haka sukai ta game abun dariya .Dan tace wai Abokan ango su nemo hair brush Guda 20 a Hall din.suka rude suna ta guje guje,su kuwa Yammatan Amarya
powder brush aka sa su su nemo,suma sun rude din,amman da class suke tafiya suna tambayan yan matan gurin,koda a cikin bridesmaid din an samu kusan 8 brushes a gun su
ESTÁS LEYENDO
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...