265-270

902 108 21
                                    

ARCH.ABBOOD DAWOUD

       NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03

2ND APRIL, 2020.

265-270

_______________________________________

Washe gari aka gama arrangements na daukan Amarya ,so bayan nan time din 4 ne na yamma daman ,se aka raba friends wasu suka dauko Amaryar Nabeel wasu kuma suka dauko ta
Abbood..haka aka kai ko wacce gidan ta a wannan yammacin ..

Naada ta shirya sosai tayi kwalliyar ta me kyau cikin kayan ta na alfarma ,haka aka fara kai faa'eey gun Naadi sannan aka wuce da ita dakin ta ,kafin ta koma gidan ta
duba da yadda bikin ya taho..

kowa ya watse aka bar faa'eey ita daya tana faman sake sake a ranta ..gurin 6 na yamma tayi alwala tayi sallah ,tana idar wa se ga Abbood ya shigo dakin da sallama,amsa
wa tayi sannan ta gaidashi .."a ranshi yace ,lallai yau an tuna kenan..'

ce mata yayi tazo suje palo zeyi magana dasu ita da matar sa,seda sunan nan ya bata haushi amman ya ta iya ,haka ta yafo mayafi ta fito palon ta zauna ,kiran sunan naadi
yayi sannan ya kira sunan faa'eey,ai maganar naadi da faa'eey taji ita ta bata damar bude fuskan ta tace .."kai ya naadi?"

kallon ta naadin tayi tace .."Na'am faa'eey ?"

kallon kasa faa'eey tayi tana mamakin yadda akai haka ta faru,wai yanzu da yar kawar ta zatayi kishi kenan?

zama tayi tana kallon gefe ,se taji kishin ta ya dan ragu a ranta,gaishe ta tayi ,ita kuma naadiyar ta amsa ba yabo ba fallasa ,saboda tana kishi da faa'eey sosai ,kuma
dalilin kishin da take da faa'eey ya samo asali ne ta sanin da tayi cewa shi Abbood da kanshi yake son ta ,se kuma ita ita tace tana son shi..katse mata tunani yayi da

fadin.." Yauwa ya naadi,kinga kece Babba,dole faa'eey zata biki yadda ya kamata ,amman kema zaki ruke girman ki yadda ya dace,bazan yadda da fada ba duk da nasan kowa
bata da tashin hankali,dan Allah ku hakura mu samu mu zauna lafiya tunda ita faa'eey ma few months zatayi anan ta koma gidan ta ..i hope duk kun gane me nake nufi ?"

cewa sukai .."eh .." yace toh maasha Allah.."Se maganar kwana ,zanyi 3 days a dakin Amarya sannan a cigaba da raba wa ,how many days kuke son a runga yi?"

Shiru dukkan su sukai ,ya sake tambayan su ,suka sake yin shiru se yace .."Yanzu nayi directing question dina to wifey naadi..how many days kike so a runga raba wa?"

Kallon shi tayi tace .."Duk yadda kace haka za'ai.."

Kallon faa'eey yayi yace .."Chinese how many days kike so ayi ?"

cewa tayi .."a zabar mana .."

Dariya yayi sannan yace .."Yau Allah ya hadani da mata masu kunya ,any ways shekenan ,i think ayi two days kamar yadda aka saba ko ,kamar zaifi?"

Ya fada da question yana kallon su ,gyada kai sukai sannan yace Alhamdulillah ..

Tashi yayi yayi hanyar dakin naadi,tana ganin haka se ta bishi ita ma.faa'eey kuwa bata sa komai a ranta ba ta tashi tayi hanyar ta ita ma ta shige daki ta tada sallar
isha'i.

Tana idar wa ta shiga wanka kuma har a lokacin be shigo ba.Bayan shigar ta ya leko dakin yaga bata ciki se ya fita waje ya karbo sako ya dawo ,har ta fito daga wankan
be shigo ba,se taji ta dan damu kadan.Amman se tayi Addu'a kawai tayi yan shafe shafen ta ,se ta saka kayan baccin ta riga da wando masu kyau da taushi ,ta shafa dan
turare sama sama ta koma gado tayi kwanciyar ta..

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now