ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIESWATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
26TH NOV, 2019.
175-180
______________________________________
for shiz naji dadin comments dinku,especially yan Divaa doveys parlour..I dey do you fa..
_______________________________________
Bacci tayi me cike da munanan mafarkai da tunanika iri iri duk akan abun da ta sa a ranta ta kwanta dashi .haka tai ta tashi tana addu'a tana koma wa bacci.chan kusan
5:40 am ta farka wanda tayi saurin tashi ta shige toilet tayo wanka wanda yake a al'adar ta sannan ta fito da alwalarta ta tada sallah.Sallah tayi me cike da ihsani da
ikhlaasi.sannan ta kai kukan ta gurin Allah akan Allah ya warware mata wannan matsalar da ta tunkaro mata (A tunanin ta kenan )..sannan tayi sauran Addu'oi dangane da
karatun ta da ma al'umma baki daya ta shafa ta tashi.Koda ta tashi se taji sha'awar kiran baby A.hakan ne yasa ta dau wayar ta jiki ba kwari tana ayyana cewar kullun Baby A ke kiran ta da Asuba ta tashi tayi sallah sannan
bayan ssunyi sallah suyi hirar su ta soyayya sannan suyi sallama kuma su shiga hidimar su ta yau da kullum.se gashi yau da yasan bashi da gaskiya be ko kira ta ba,cewa
tayi .."Toh ni me yasa zan kira sa tnda ma shi yaki kirana ?"Wata zuciyar ce tace "Ai gwamma ki kira ko ya maki bayanin abunda kika ji jiya.."
Dialing numbern tayi zuciyan ta na kara bugu .ai kuwa har ta katse Baby A be dauka ba.A wannan lokacin kuwa shi yana toilet ma yana ta mitar yau be kira Babyn sa ba kuma
gashi shima har to 7 be yi sallah ba.da hanzari ya fito inda ya sake tsintar kukan wayar shi .cewa yayi se yayi sallah sannan yazo ya dau wayar duk dama be sa a ransa
Baby F bane saboda su Umma irin wannan time din suke kiran sa tun kan ya fita aiki,duk da ma ya danganta da tsarin timing din nashi.Amman a yanzu da yake tafiyar rana
da dare da safe ne ake samun sa.Da wannan ya kabbarta sallah bayan jero Istighfaar mara adadi.ko da ya Idar ya dade a zaune yana Addu'oi sannan ya tashi ya nufi kitchnet dinsa .dan Coffee ya samu ya
hado sannan ya zauna ya latsa kiran sunan Baby da ya gani yana ayyana irin mitar da ze sha ya sa sun makara sallah.dan a tunanin shi lokacin ta tashi ganin be kirata
ba yasa ta kirashi.wani lallausan murmushi me sauti ya sake ganin yadda numbern tayi saurin shiga.Ita kuwa Faa'eey ta kule ranta ya baci .zama ma ta kasa se ayyano abubuwa take tayi game da rashin kiran ta da daukar nata kiran.cikin wannan sintirin taji wayar ta
na kara.da sauri ta nauka har wani diri taake zata fara korafi.se taji ya fara mata waka yana fadin .."you are my life and my love you are the secret of every air i breath
.."Cewa take lallai ma ya raina mun hankali ,ba dole ya fara waka ba yasan yayi ba dai dai ba.jin shirun ta yasa yace .."Hello bae..are yo there.."
Ji tayi wani mololon bakin ciki ya taso mata.ita fa so take tayi fada da shi.so take tasan dalilin da yasa shi zuwa ko kuma kiran mace.har tana wani kiranshi da baby.
kawai tuna haka da tayi se taji hawaye ya gangaro mata..da kyar tace masa.."ina kwana .." Daga yadda tayi gaisuwan ma yasan ba lafiya .se yayi saurin cewa .."Babe ,Babe
whats wrong baki da lafiya ne ?"Cewa tayi a ranta "Anzo dai dai wajen.."
cewa ta sake yi .."ni lafiya ta kalau ..kawai dai kaine kasa na kasa walwala kuma nake ciwon kai.."
shiru yayi sannan yace .."NI,ni kuma ,me nayi miki haka,ko dan ban kiraki ba jiya ..wallah baby bani da lafiya ne sji yasa ,baki ga har na makara sallah ba yau ko kiranki
banyi ba ,ai kinsan is so unusual of me .."cewatayi .."Shi yasa kuma naji wata tana ce maka baby ko?"
Gaban sa ne ya fadi dan wallahi be san anyi haka ba.yo a ina wata zata ce masa baby .se kawai yace a ransa hala ma mafarki ne tayi zata daga masa hankali da farar
safiyar nan .cewa yayi .."Huh baby just say kinyi mafarki ne ,enough with this your drama.har kin daga man hankali wallah..so ya kike ,i kinda missed you fa,jiya
bakiga yadda na sha wahala ba.like ciwon ciki i tot i was going to die ma .."Ayyanawa take ya ma raina mata hankali ..se kawai ta fashe da kuka .yama za'ai yace ba haka bane bayan da kunnen ta taji abun da taji,har kofa aka bude aka rufe fa
kuma duk taji ,yaushe ze ce ba haka ba .kuka take sosai inda ta ajje wayar yana ta magana ta na jin sa amman shiru shiru bata kula ba.kashe wa yayi ya sake kira
nan ma stll bata dauka ba.nan fa hankalin shi ya tashi ,dan yasan yanzu she is serious .but what happened ?Tambaya kenan da yake ta yiwa kansa amma ba amsa.gashi baya son ya kira Baba kulu tun yanzu.kawai se ya shiga typing Apology text messages yana tura mata .har yayi mata
uku sannan ya hakura haka ya tashi ya shirya dan zeyi flying.haka yake ta aiki sukuku.wannan abun se da ya dauke su 3 days faa'eey be gane kanta ba.shi kuma ya rantse
ba wata mace da ta kira shi da bay jar faa'eeyn taji kamar yadda take fada.A karshe fushin se ya zamto nasu duka dan shi ya lura faa'eeyn kawai bata yadda dashi bane
in banda haka ya zata ce wai taji shi da mace ,Mace fa,toh me take nufi yana yi da ita ?Wani fada ya rufe faa'eey dashi a wata waya da suke yi tana mai halaye.sosai ya mata fada kuma yace kar ta sake masa wannan maganar .kuma ya hanata kukan .nan fa ita
kuma taga ita ce me gaskiya se kawai ta fita harkar shi.duk da suna fada kullun yana kira da asuba ya tashe ta su gaisa kowa yana baasar wa.se ta kashe wayar tata ma
kullum in ya kira shiru,koda ya ga haka hankalin shi ya tashi dan dama daurewa yake yi sosai yake jin fushin ta ya ishe shi.wai mene haka ne shi kam.sun samu akalla 2 weeks abun ba kanta .se a yau ne da aka cika two weeks sannan Mas'ud ya dawo inda yake bawa Ash hakurin rashin kiran shi da beyi ba.ashe daman next day
zeje gida .so daze tafi ma yabar line dinshi na London yayi gida abun shi.A jiya ya dawo sannan a yau yazo gun Ash yana ta tambayar shi ya jikin shi..Shi dai ASh se a lokacin ma ya tuno da faruwan hakan .se yake ta amsa shi da Lafiya Alhamdulillah.Nan ne Mas'ud ya sako serious face yana kallon Ashraf.ko shi Ashraf seda
kallon yasa shi shan jinin jikin shi.dan Gyaran murya Mas'ud yayi yace .."bruh ,i want to ask you something ,and im sorry if its your personal life but uhm as a Muslim
bruh zan baka shawara .but before then ina son na san meye hadinka da chronic erections din da har suke saka a irin wanchan condition din as young as you are?"Kallon shi Ash yayi yace .."uhm,uhm its ,uhm i actually have a wife,im married .."
Wani irin zabura Mas'ud yayi ko shi ashraf seda ya gani kuma seda abun ya basa dariya ..Dariya sukai tare mas'ud na sake mamakin yiyuwar haka.duk da ma Ash din yayi
jiki sannan kuma shi Mas'ud yasan irin auren da ake kenan na yan yara.abun ya daure mashi kai.nan ne yace .."daman i tot kana kula setual workers ne .."Dan shafa kai Ash yayi ya danyi murmushi sannan ya girgiza kai yace .."I dont do that sesa ma na shiga wanchan condition din.."
Kallon shi Mas'ud yayi sannan yace .."im sorry Bruh,but ina wife dinka take ..shiru yayi sannan yace .." tana gidan mu.Russia ,tana russia.."
ko daga nan Mas'ud be sake tambayar Ash komi ba .tunda ma al'adar sa kamar bature haka yake ,koda ma ya ruga yayi kutse,amman wannan bisa mamaki ne da tausayi.
so daganan suka ci gaba da yar hira haka mostly ma akan aikin Ash dinne.cikin hirar ne ma Mas'ud yaji fadan ash da faa'eey.A nan ne fa Mas'ud ya tuno da time din
da summy ta kira shi ta bashi fone din amman ai bata daga wayar ba .A nashi tunanin kenan fa .Wata ajiyar zuciya Ash yayi yayin da yaji wani nauyi ya sauka a zuciyar shi.dialing numbrn ta yayi amman a kashe.nan ya yanke shawarar zuwa ya same ta koda one day ne..
tohm doveys ko yaya za'a kare ?
Sorry for the short chapter ..yafi babu ..
TBC..........................
YOU ARE READING
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...