150-155

1.2K 139 17
                                    

ARCH.ABBOOD DAWOUD

       NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)

A K A AUNTY DIVAA

C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03

27TH JULY ,2019.

150-155



__________________________________________



Kallon su yayi cike da Kauna yace .."barka kadai yan yarana.ya kuke ya gidan,kallon faa'eey yayi yace ..Faa'eeyn papa,ya kike ya sabon guri,ince dai Malam Ashraf yana

baki abinci sosai kamar yadda yace ?"

cikin tsokana ya fadi aganar.shi kuwa Ash ya gane me papan yake nufi.wata rana da ya ganshi a gate yana leken faa'eeyn ne sukai maganar.so se Ash yayi smiling cikin

jin kunya ya dan shafa kan shi.tashi Faa'eey tayi tana cewa .."Papa wai ina Mamina,ya jikin ta ?"

"tana dakin ta .maza ma kira ta haka ake yi se ta tafi ta barni ni kadai.bayan wasu ma har yawo suke tare.."

Wuf faa'eey tayi ta shige.shiko Ash kasa ya sake yi da kan shi.kai kace nitse wa zeyi a cikin rug din. Dariya papa yayi ta manya yayi dan gyaran murya yace .."Malam Ashraf

ina fatan ba wata matsala dai ko?"  Daga kai yayi yana murmmushin shi me nuna kunyar da yake ji.shi ko Papa ba ruwan shi.suna haka faa'eey ta shigo tana cewa.."gata

nan zuwa papa.bacci ma take amman na tashe ta dan nayi missing din Mami na sosai sosai."  Cew Papa yayi .."Eh ita ma tana missing dinki.shi yasa ma tace gaskiya ita ta fasa bayar

ta fasa bayar wa.wai gwamma ki dawo gun ta kawai abinki.."

Wata iriyar razana da Ash yayi kai kace mugun labari aka bashi.A idon Papa wanda dariya taso kwace wa...se yaga Ash din ya kalli faaeey wanda hakan ya nuna so Ash

yake yaga yanda faa'eeyn nashi zata karbi maganar.se yaga ita ma shi take kallo da tsoro a idon ta.shi kuma papa ya sha kunu kamar ba shi yayi maganar ba.Ganin sun

shiga rudu ne yasa yace .."Ah lallai,da alama dai baza ki zauna ba.."

Kallon papa tayi tana tunanin in tace bazata zauna ba tayi rashin kunya.kar kuma tace zata zauna a rike ta Baby A ya tafi russia shi daya ya barta,shin in haka ta faru

wai ya zatayi da mugun son shi.Amman dai ta zabi tace zata zauna din.in yaso ko Umma se tasa Ash yayi wa magana.."  Kwatsam Ash yaji tace .."Ah ah papa zan zauna.

wato shi Ash ji yayi kamar an dalla mai mari.wannan amsar bata mai ba.yanzu kuma in aka ce ta zauna din se ta wai zauna,se ta barshi shi daya ya tafi.toh ya zaiyi da dakon

kaunar ta.ai wallahi tun wuri in dai ana so yayi karatu a hada shi da matar shi.toh kenan ma in har haka ne ba damuwa tayi da shi ba kenan? shi a halin da ake ciki

wallahi har in zama za tayi se dai su zauna tare..

Cikin tunanin shi yaji papa na cewa .."Mami shekenan kin daina missing faa'eeyn ki tunda ta yadda zata zauna dake din.."

Kallon shi tayi yayi saurin kashe mata ido haka ya tabbatar mata da cewa papan ya sako su gaba kenan .kallon su tayi taga duk sunyi tsuru tsuru.sunyi kalar tausayi



Aiko tausayin su taji se ta kalli Papa tace "Ah ah Papa,ka raba mutum da matar sa.indai dan nice na hakura abar masa kayan sa.."

Wata Ajiyar zuciya ya sauke wadda tasa duk suka kalle shi.se a sannan ya gane a fili ya sauke ta.se kunya ta kamashi.se kaunar Mami ta kama shi yaji ta shiga ransa more than da

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now