part 10-15

1.8K 144 0
                                    

ABBOOD DAWOUD
           
            NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS). AKA
DIVAA

@divaa_doveysdiaries. On wattpad and instagram. Please follow, like, vote, comment and share

EPISODE (3)

12TH NOV. 2017
12TH NOV.2018

My birthday.. ❤🎂

Thanks all for the birthday wishes. Thou I didn't start posting the book.

(Doveys, lovely readers and ghost readers..the spelling of "abood ",is now "abbood"..this is the  correct spelling of the name. "ABBOOD "..Meaning."devoted worshipper of Allah)

Sorry readers na manta na saka Episode 1-5,2-10.

Now episode 3-15

Let's go..

Su fa'eiy ne suka saka masu kaya mota.nabeel ya basu 1k sabuwa kar kowaccen su. Anan ne take Kara cewa..

"Papa.. Yanzu kuma su ina zasu tafi, badai garin su zasu ba ko?.. "

Girgida kai yayi yace..
"Fa'eiyyy.. Kinsan su ne?.. "

A lokacin jidderh ta bashi labarin yadda akai a cikin gida..

Nabeel ne yace mata..

"Fa'eiyn papa. Kano zamu yanzu sannan mu wuce garin mu "

Ko Kafin ya dire ta fara dariya tana fadin..
"Aishatu (gezawah) ai na gaya maki irin su ne.. "

Kallon abbood tayi tace mashi..
"Kai amman kana kama kuma da irin mutanen cikin su jumong.. "

Murmushi yayi yace "shidin kuma waye?"..

Kallon jidderh tayi tana fadin..
"Maama gaya mashi su kilan ya sansu inkin gaya mashi ko?.. "

Papa da yaga abun baze kare ba yace "Aishatu maza kuje ciki zasu tafi kar suyi dare.. "

Bye bye suka masu tare da godiya suka koma cikin gida suna tafiya tubur tubur suna zancen su abunsu..

Su kuma su nabeel suka kama hanya . Abbood zuciyar shi tunani fal.

To 5:00 suka baro kazaure. Wannan Karon kuma nabeel ke tuki. Dan kuwa abbood bashi da karfin yin tuki.. Shi kanshi nabeel ya lura da mutumin nashi amman yafi badawa a ranshi cewa gajiya ce tare da hayaniyar da suka shiga..

Gudu suke ba na wasa ba..

*****-----*****

ABUJA

Su su'ad ba sauran zama ana ta hidima
Su deezah ma kowa ka gani ana ta shige da fice ana Kara hada komai ..

Abu biyu ne suka hadin ma najwa. Rashin isowan cake dinsu da kuma su bee h da har yanzu basu dawo ba..

Nabeel ta kira. Yana daga wa yace mata "muna kusa da airport".. Lokacin 6:20..
Nan ta ke gaya mashi cake insu bai Iso ba har yanzu.. Tambayan ta yayi da waye zai kawo

" Su Babyzee ne  "..ta gaya mashi.. Tare da gaya mai flight din su 5:40 ne amman sun sama delay. Wai yanzu se 6:45..

Che mata yayi jirgi daya zasu shigo..

Okay tace tare da Addu'an Allah ya kawo su lafiya..

Abbood dake gefe bai ko damu da wayar nabeel ba. Haka kuma bai gane me wayan ke nufi ba..

Sannu a hankali se gasu a airport. Masallaci suka nufa bayan sunyi parking. Sallah sukayi sannan suka fito ko sannan 6:38 tayi.

Nan kuma aka fara rigiman barin dambu da sauran su.. A karshe dai sun hakura zasu bari a mota tunda za'azo daukan motan. Haka nan suka hakura. Sai suka nemi wani gaye Anas yana saida ticket na parking a nan airport din kano. Ya sansu da kyau saboda haka suka gaya mashi za'a zo a dauki motan anjima..

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now