ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
9TH MARCH.2019
PLEASE VOTE AND SHARE..
_______________________
Rana bata karya sedai uwar diya taji kunya.haka ne kam tunda yau ta kasance ranar bikin farko wanda bridal shower aka
fara yi inda kawayen amarya suka ci suka sha kowa ka gani yasha kwalliya .kai kun dai san bikin kano yanzu yadda kawayn
amarya suke kwalliya har ka zata amare ne suma.hakan ce ta kasance sedai fa rigar amarya naadi ba kamarta .dan wani
yadi ne me sirrin azabar kyau wanda bashi da hayaniya aka dinka mata shi black ne dinkin slim floor lenght dress tabi
jikin ta se walainiya take yi.dake naadin bata cika jiki ba.haka kuma komai nata dan dai dai dashi.
washe gari ya kama ranar kamun Ango wanda za'a yishi a meena event center an shirya mai gurin zaman su na su biyu wanda
ya kayatu da kayan zamani na gargajiya.inda daga gefe kuma aka yi wata yar bukka aka rufe ta ruf.koda aka fara taro
iyaye ne zalla ba amarya ba ango da abokan su.
Amarya tana gida ana mata shiri me kyau wanda Atampha tasa dinkin zani da rigar saki.tayi kyau maasha Allah.Ango kuwa
shadda yasa wadda ta dace da kalar atamphan naadi.yayi kyau sosai haka aka suka iso kofar hall suka tsaya kamar dai
yadda aka saba.sedai fa Amarya da tawaggar ta daban suka shiga suna rawa suna yanga suka samu guri suka tsattsaya a layi.
syn kawata wajen yayin da ango yake waje abokan sa nata tsokanar sa ya sha kunu.nabeel se masifa yake akan lallai dole
se shi Abbood yayi abunda yake so wanda a ganin nabeel dasu khalil su hadi su affan su Arab ,muhsin kai da dai sauransu
da yawa.
koda Mc ya gayyaci su ango se suka fara takowa cikin gayu da kasaita .layi daya sukai dogo wanda a gaban layin Nabeel da
Abood ke tsaye inda nabeel yake saitin layin angwayen shi kuma Abbood shi kadai ke gefen ,cikin wani salo na taku iri
daya suke tafiya kidin wakar (a one ode,a 2 odede,a 3 odedede..eeeh yeba).dont mind me divaa. har suka isa dai dai
amaren suke sannan suka tsaya suma suna rawar su me abun dariya dan yawancin su basu iya rawa ba.karma da khalil yaji
labari.dan wallahi nabel ne yace duk wanda yaki rawa se sun rama ta hanyar da basuyi zato ba.toh koma ba haka dukkan
su suna son Abbood suna ji dashi saboda dai gaskiya bashi da abokin fada toh shi ko hayaniya baya so bare wani fada.
sedai fa akwai zuciya in aka tabosa.daman kuma kunsan face dinsa ma bata kama da ta wasa.kwarjinin sa ma kadai abun mamaki
ne.
Haka dai akai ta musu dariya sannan yan matan amarya da abokan ango suka tafi a layi zuwa left side da right side
suka zauna inda gurin zamansu yake.akabar ango da amarya a tsakiya zo ka ga fadin maasha Allah .kai kawai sun hadu ne
YOU ARE READING
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...