ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIESWATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
10TH MARCH, 2020.
230-235
____________________________________
A kwana a tashi ba wuya gurin Allah ,se gashi Ash yayi 2 years da auren shi da Jaab ,sedai kuma har yanzu basu haihu ba,ko da yake ma daman ko auren shi na farko seda
suka dade sannan suka samu ciki,so hakan ne yake kokarin faruwa da Ash again,gashi kuma daman ita ma Jaab din ita kadai maman ta Aurmi ta haifa .Wai shin ina Umma take ,shin ta yadda da Jaab a matsayin suruka ?
Toh Umma dai bata yarda da Jaab ba,sedai ba wanda ze fito ya fada ko yace ya gane,saboda itan ma bata nuna wa ,amman har ranta tasan bata son Jaab,sedai kuma kullum tana
cikin yi musu Addu'a sannan har yau tana fatan Faa'eey ta dawo ma Ash dan tasan Faa'eey matar arziki ce,matar rufin asiri,takai duk inda ake son duk wata macen aure takai
,amman ya ta iya ,dole se fata na gari take mata a duk halin da ta samu kanta.______________________________________
6 months later
tsaye yake jikin wani fence da ya kasance fili ne na training din sojoji wanda ya zama saura one week su kammala ..a dai dai wannan lokaci kuma guy din wanda shi ke tsaye
daga jikin fence din naga yana ta waya,ko da yake ban san waye shi ba ,sannan kuma ban san wayar me yake ba,nadai ga ya natsu wanda a nan ne na tabbatar wannan wayar tana
da muhimmanci a gare shi ..Ko da ma a tsayen da yake kuma Hannun sa na makale ne da POP wanda hakan ke nuna alamun cewa hannun guy din a tsaye yake ,da haka ya gama
waya inda na ganshi yana tako wa cikin takama da kasaita ,ga wata isa da yake nuna wa ,Guy din wanda haduwar sa ta kai haduwa kyaun sa ya kai kyau,kasaitar sa takai
kasaita ne naga ya matso yana magana da wasu guys din wanda suma sojojin ne ..*****************************************
6 days later
Su Dada ne da Ammi,Najwa da Assadiq,se Hana da Hanan ,meena da Amir da Samy (second baby din Nabeel) se Naadi da Yasmin da Amani itama (3rd bbyn Abbood) ,su na gani
ana ta sauri a kama hanya,ni ban san inda suka nufa ,sedai nasan cewa Drivern su Abbood na office ne yake jan su Ammi da dada da yan jikokin su,se Nabeel wanda shi ke
jan su Meena da Naadi da Najwa ,se Assadiq a gaba ,sun kama hanya bayan Addu'oi da aka sha ..sudai duk sun san cewa zasu Abuja ne dubiya,sedai bayan doguwar tafiya
se gashi kuma sun dire a wani gari ..ko wana gari ne wannan ? se munyi gaba sannan****************************************
Sojoji ne gawurtattun maza wanda da ka gansu kaga haddadu yan hutu ma wasunsu ga zubin naira ..A tsaye suke sun jeru wanda yau ya kasance yau ce ranar passing out parade
,su Dada da suka iso duk murna ce ta cika masu fuska da zuciyar su..Su Nabeel kuwa sudai kawai sun zubawa sarautar Allah ido suna kallon ikon Allah,kamar da wasa Najwa
tace .."Dada,ya naga wani kamar BH?" kai wallah shine ..Nan fa sauran ahalin ma suka fara hange suna so su tantance ,ba shaka kuwa Abbood ne ,wanda ya gaji da gorin da
Nabeel yake masa na cewa komai nashi kamar na mace ne,wannan dalilin yasa Abood yayi zuciya ,tun sun UK ya fara neman hanyar da ze shiga yayi short service,ko da yake ma
ya boye ,amman ya boye ne saboda kar su hana shi ko su soki batun,yanzu kuwa gashi a randa ya gama ne suka sani duk da Ammi da Dada sun sani,sedai ko su be fadawa ya
balle ba..An dau lokaci ana program din,seda suka gama sannan ko wa ya fara hangen dangin shi,Naadi kam se kuka kawai take kamar me ,ita ciwon Hannun shi ne ma yafi damun ta ,sannan
wallahi da ta sani tun farko bazata bar shi yayi ba,da sauri Najwa ta tafi ta ruko shi itama tana hawaye ,shi ko Nabeel tsabar Haushi ma Mota kawai ya juya ya shiga abunsa
,sannu a hankali Abbood ya tako ya nufo su da murmushi a fuskar sa ,farin ciki sosai yake yi,yama rasa gun wanda zeje ,yayi missing Amir,da yasmin da Ammi da Dada upon all
kuma yayi missing matar shi ,se kawai ya tsaya yana kallon su da farinciki,su Amir suka zo gun shi da gudu har su hanan ma suna ta murnar ganin Daddy Abbood,bayan ya
cikasu ya matso gun su Ammi ,aiko da sauri ta yi mashi side hug tana sanya mashi albarka.Dada dai dariya ma yake tayi irin ta manya dinnan ga murna shima a fuskar shi..
YOU ARE READING
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...