195-200

888 93 7
                                    

ARCH.ABBOOD DAWOUD

NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03

5TH DEC, 2019

195-200

__________________________________

Gyaran muryan wanda yayi dai dai da dago idanun su suka kalle shi a tare,shi yayi dai dai da kallon junan su da sukai sannan suka sauke ido wanda yaya ishaq yake kallo
duk abunda suke yi.Da farko dai Ash ya fara wa Nasiha wadda ya nuna masa cewa dole ya san yadda ze runga controlling faa'eeyn tunda yarinya ce.shi kuma dole ya dau
girman tunda dole dai shine a gaba,ya nuna masa lallai ya daina bari yana irin wannan shirmen da ita komin runtsi.

Dawo wa kan faa'eey yayi yace .."Amman Faa'eeza ban taba sanin a yadda na sanki da kirki da ladabi ba zaki iya yi wa mijin ki haka.rashin kunya wa miji fa ba karamin abu
bane.kinsan Cewa In kika bata wa mijin ki rai kuwa har kafin ya sauko ana miki tsinuwa,kina son haka ne ?"

Girgiza kai tayi hawaye na sulmuyo mata daga idon ta,kai da gani kasan ba karamin damuwa ta shiga ba..kallon ta yayi yadda ta fara fidda shessheka a hankali wanda kukan
ke taba zuciyar Ash sosai Dan Allah ya san soyayyar faa'eey ce hala ajalin shi.shi da kansa ya san yana mata soyyayar da baya wa kanshi.kai a takaice ma daga Umman sa se
faa'eey duk duniyan nan kuwa.

Fada me kama da nasiha ya ishaq yayi wa dukkan su har yake cewa .."Ko so kuke yi ace anyi danasanin aurar da ku?,be jira ba ya cigaba da cewa ..Dan Allah ku rike kanku
kamar yadda kuka faro .sannan ku yi abunda za'a cigaba da alfahari da auranku .ku tuna Papa da granny da suka jajirce a kan auren ku.kuma se kawai ace kun fara samun
sabani sannan har baza kuyi settling issue din ba se ya dauki wasu watanni.Gaskiya hakan ya bata mun rai sannan banji dadi ba.Kuma sannan bana son na sake ji ko na sake
gani ko kusa ko alama!

Fada yake sosai dan yana so ya ja musu kunne sosai tunda gaskiya ba zasu fada wa su umma ba.kuma yana fatan wannan din ya zama na karshen karshe ..Kukan da take yi ne
yasa su tsaya wa kallon ta.A kuma suka kalli juna.shi yaya ishaq ya wa Ash kallon irin ka gani ko?"

Kallon ta ya sake yi yace .."FAa'eeza.."

bata dago ba amman tayi alamun ta amsa ..ce mata yayi .."akwai damuwa ne ?"

A hankali ta girgiza kai ..se kawai yayi wani tunani .nan ya kara masu nasiha me ratsa jiki a kan rayuwar aure wanda ya cire son kai yayi masu duk kuma ya ratsa su..nan yayi
masu sallama ya tafi akan zasu fita anjima wanda kuma saura 5 days su tafi..

Tare suka tafi da Ash inda ya samar masa taxi ya tafi sannan Ash ya dawo.A inda ya tafi ya barta a nan ya same ta tana kan kukan ta.A gaban ta yaje ya tsaya yana jin
yadda zuciyar shi take asalin karye wa..

Sama yake kallo yama rasa me zece mata ..kallon ta ya tsaya yi chan yayi gathering courage yace ,,"Babe,Baby.."

wallahi seda taji tsigar jikin ta ya tashi dan irin yanayin da ya kira sunan nata da shi.dan kadan ta kada kanta yayin da ya tsugunno ya kamo ta ta tashi tsaye .."kallon ta
yayi sannan yace .."Wait..wai nikam kukan me ma kike yi,ba ke kike yin fushi dani ba?"

Kallon shi tayi da wet face dinta ga idon ta da yayi ja sannan tace .."kaine kake fushi dani .." cikin sakarci da bare baki ta fada .se kawai ta bashi dariya ..amman
se ya gimtse yace .."Eh ni kam da gaske nake fushi da ke saboda kin nuna baki yadda dani ba sannan kuma kina zargi na..wallahi it pains my heart to hear that from you.
faa'eeza ke kike tunanin ni mijin ki ina neman mata ..this sucks and hurts you know..but its a past thou..sedai zan miki rantsuwa guda daya in kin yarda tohm ..Wallahi
ban taba wani abu da wata ba wallahi..

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now