ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
19TH JULY,2019
135-140
________________________________
A bangaren Amarya rasheeda tana nan abun duniya ya isheta ,ace anyi auren ka a sati daya anyi maka kishiya,shin wannan
wace irin kaddara ce ta sameta.ace daga aure anyo mata amarya bayan itama amaryar ce .kuma wadda aka auro din itace
wadda ake so,ko wana irin zama zasuyi wannan ?
Bari mudan koma baya kadan zuwa Ranar da rasheeda ta tare mugano yaya Ango Assadiq yayi..koda mutane suka watse ya zama
saura ita daya,dan dama bata wani tara yan siyen baki dan tasan bama ta isa da hakan ba.
Dakakkiyar shadda ce a jikin sa irin light yello dinnan me daukar ido.se wani malakwai malakwai take duk inda ya motsa
ga wani uban kamshin Dior sauvage da yake zabga wa.Duk fa wannad Maaman sa ce tayi masa nasihar da ta ratsa jiki da jijiyar sa
hadi da umarni wanda tace indai yayi wasa da auren sa bashi ba ita.dan bazata saka ido dan ta ya halaka ba a kan so
kawai.Allah sarki uwa me adalci kenan.gashi tasan yadda komai ya faru .amman tana kokarin ganin hakkin rasheeda da Allah
ya daura Assadiq din ya sauke shi..
da sallama ya shigo dakin cikin muryar sa me sanyi wanda hakan ya bala'in bata mamaki.dan ko a shirmen mafarkin ta bata
taba tunanin ma ze shigo ba dakin ba.se gashi ya bata mugun mamaki.A gefen ta ya samu ya zauna yana dan kokarin yi mata
murmushi.cewa yayi.."Sannun ki da zuwa Amarya.."
Kallon shi tayi tace mashi.."sannu da zuwa,ina yini.."
amsa wa yayi da .."Lafiya lau ya hidiman biki?"
tace .."lafiya Alhamdullilah.." duk cikin mamakin yadda yake fitarda wani murmushin da yake kayatar da ita take ..cewa ya
sake yi.."tohm rasheeda,ki tashi muyi sallah muyi godiya ga Allah da ya hada mu wanda bamusan meye rabon dake tsakanin mu
ba.sannan kar kiga naki yadda da auren da kizata ko kinki nake ,kawai kinsan yanayin yan adam haka muke ,se muyita rokar
Alherin mu in Allah ya kawo shi kuma se mu runga gududwa muna yiwa kanmu zabi da kanmu.so se kiga daga mutum ya dawo kuma
yana regretting .here i want to say i accepted our marriage whole heartedly sedai ina baki hakurin duk wani abu da zaki gani
ba dai dai ba.sannan next week saturday za'a kara daura wani auren da kanwarki.i hope zaki karbi shortness dina ki dauka
hakan ba yana nufin cin fuska bane a gareki?,sannan zaki bani hadin kai ki zauna da second amarya lafiya?"
Tabbas zuciyar ta na kuna.amman me maganar da yayi mata cikin hikima da dabara shi ya chanji zuciyar tata daga kuna ya
sauya ta ta koma zafi takeyi wanda wannan dole ne.amman duk da haka ai sedai ta gode wa Allah.inda wani ne ma baze kulata
YOU ARE READING
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...