ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIESWATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
27TH NOV, 2019.
180-185
________________________________
Tunani yayi ya kira Baba kulu,aiko yana kira ta dauka .cikin Sallama take dan zolayan shi da tsuntsayen dole.Dan smiling yayi ya gaishe ta.ko kafin ma ya tambayi Faa'eey
tasan ita yake nema .se tace .."Sedai Babyn bata nan taje makaranta.."Ajiyar zuciya ya sauke yace .."Tohm is sokay .amman da ta dawo Baba kice mata please ta kirani.noo kice nace wai Lallai ta kunna wayar ta kuma ta kira ni da ita.."
cewa Baba tayi .."Tohm insha Allah..."Godiya yayi mata yayi sallama ya kashe wayar sa.Mas'ud ne ya kalle sa yace .."Take komi easy,zatayi understand naka o.k?"
Dan nodding kan shi yayi shima cikin gamsuwa da hakan .yasan yana fada mata zata gane duk a wuce gun,dan ba karamin dauriya yayi na wannan fushin ba.Duk da ma tana da gaskiya
amman duk da haka ai uzuri ma wani abu ne ..haka ya samu ya shirya suka fita inda ya nufi gun aikin shi shi ma Mas'ud ya nufi gidan su akan cewa ma zashi Reading ya
dawo .Haka nan faa'eey da ta dawo Baba ta bata sakon se ta kunna wayar kuma ta kira shi,ko ba komai tayi missing din shi dan ita kadai tasan yadda ta rayu a wannan kwanakin
da suke fada.kullun ne se tayi kuka tace ya tafi ya barata yana kula wata ..tayi mai isarta sannan tayi bacci.shima baccin a sace yake daukar ta.A dai dai sanda ta kira shi shi kuma wayar shi a kashe ya hau jirgi abunsa.haka tayi ta gwadawa har ranar ta kare bata same shi ba.jiki a salube ta hakura tana yan hidin
dimun ta .Baba kulu kuwa a fakaice take ta bawa faa'eeyn shawara akan tabi komi a sannu.duk da ma bata san mene ne ya hadasu ba.amman faa'eeyn ta gaya mata cewa sunyi fada da Baby
A .Toh bari mu waiwaya Najariya muga abubuwan dake wakana .
__________________________________
Dawowar su Abbood da sati uku yau cif cif ,se ga Naadi ta fara laulayi laulayi.koda aka gwada aka ga shes pregnant for 3 weeks 2 days .nan fa hankalin ta ya tashi over
bori iri iri kala kala take ma Abbood ..wanda hakan ya sa shi fara gudun zaman gidan sa.se dare ya dawo ya kwanta sannan da safe in ya tashi da ta fara rigimar ta se
ya mata shiru yayi ta harkokin sa yayi wanka ya fice ya bar gidan.yama ki bari su zauna tare tayi magana baren tama ya kulata.sedai ya samu Ammi da maganan inda tace
masa cikin ke sata rigima ya bita a hankali har ta wuce wannan stage din.Har iyanzu da Abbood yayi aure ya haihu haihuwa biyu ma ga na 3 .hakanan yake da sanyi kamar dai da chan.nikam se naga kamar abun ma gaba yaci ba baya .shi dai kawai
bashi da kyuya ne kawai amman fa jikin sa baya son yama yama .jikin shi da shi kanshi ma butter cheese ne..kamar yanzu da yake tsaye a gaban mirror yana saka kayan sa
wanda ba shida niyyar zuwa ko ina yau tunda Ammi ta nuna masa ya runga bata time dinsa da kulawa ..A hankali yake komai wanda zaka rantse mace ne ..kama daga yadda yake
kokarin sanya pure cotton shirt da pants din ta .Mutuniyar kuma tana nan zaune ta kumbura fuska kamar wata pizza dough.a dole ita fushi take yi da shi.wai a cewar ta ma se tabe mata baki yake kuma ita ta lura ma har
kallon ta yake yi yana mata dariya.hmm Naadi! queen of paranoia kenan.kallon ta yake ta madubi yana dan fesa turare dan dai dai misali dan be cika fesa turaren nan ba
se kace wani wanda yayi wanka a swimming din turare ..yadda ta cika tayi dam ne yasa shi dan murmusa wa ya tabe baki kamar dai yadda yake a al'adar sa.aiko charaf ta dago ta kama shi yana wannan smiling din.ai kawai se
ta fara hawayen takaici da kullutun bakin ciki.nan fa ta hau diri tana mazurai ta shagwabe fuska ta hau kuka..cikin Kukan take cewa.."ni wai me yasa kake ta kallo na
kana mun dariya ne ,ni wai me nayi maka ne haka.kullun kenan ni se kayi ta mun dariya .."Wato tsabar rigiman zallah ke damun ta rasa fado wani reasonable reason se zagaye take a waje guda daya tana kame kame ..dfan dariya yayi da ya fahimce cewar drama
kawai take son masa..Hakuri ya fara bata bayan ya juyo yana duban ta ..cewa yayi .."Queen of Drama .." Nan fa ta fara wani sabon dirin .shi kuwa se ta wani birge shi
yaji ya kara nunkaya a cikin kogin soyayyar ta ..se kawai ya kamota ya rungume ta tsam a jikin sa yana patting back diinta cikin lallashi.shi yasan damuwar ta .kawai
yasan cikin ne take wa wannan rigiman.kuma haka ne kow da irin shi .shi ya dade da lura da cewar ita bame son yara bace ba .he can understand her kowa da irin shi amman
ya kamata ko kafin ta fara wannan rigiman ta samu koda yara uku ne se su fara planning dan shi Abbood bai ki ace yana da yara kamar 6 ba ko fi..niko nace da yake be san wahalar
daukan ciki da haihuwar shi ba ba.haka nan dai ya samu ya lallabata ya ziyar shi duniyar 10.sannan ya sake kimtsawa yayi ficewar shi. A lokacin ne kuma suka fara samun wani dan tangarda dangane da
aikin su .Abbood da Nabeel kenan wanda kawai wani Architect ya Bullo da karfin sa ya fara aikin wani tafatsetsen 5 star hotel dake garin Kano.A dai dai wannan lokaci
se hankalin kowa ya koma kanshi ,duba da cewayan kano daman basu iya samun abu ba.nan fa duk wani tudu da kwari ,media ko ina maganar wannan Gini ake da irin kayan da
ake ta shelar cewa za'a zuba.kan kace me se ga wannan sabon Arch wanda company name dinshi ya kama SSS & co. ya samu dunbun customers wanda har aiki ya mishi yawa .
Hankalin su Nabeel ya Tashi dan kuwa sun dade suna lissafin samun wannan project din,se gashi kawai wani ya fito out of nowhere ya samu .gashi har yanzu sun kasa gane
kan abun.haka dai suka fawwala wa Allah sannan suka dage akan cewa fa Rabon kwado baya ..oho wallahi na manta karshen maganan amman dai abunda nake nufi anan shine duk
abunda yake naka ne baya taba wuce ka se yazo ya sameka ko kuwa kai kaje ka same shi..A Yau da ta kama 29th nov 2019 ne yayi dai dsai da zagayowar ranar haihuwan Ammi wanda ta samu cika shekaru 50 cif cif a duniya,su Ammi fa an tafi kuma an raba 100.se
kuma Addu'ar karo shekarun masu dubun albarka (i love you Ummana )..A nan gefen kuma karku mata cewa 12th nov ne birthdate din Abbood..Amman beyi komi ba.daman shi manatwa
ma yake da date din.mostly bank ke tuna mai ko su Nabeel suyi masa suprise..Haka ne ya bawa Najwa,Assadiq baban yan biyu da Nabeel baban Ameer suka hada kai wajen hadawa Ammin tasu Grand party..A garin na kano me dumbin Albarkar event centrs
suka zago suka zaga suka samo wani event center me suna FABS suka kama wannan marque din shafcece ko jin kudin basuyi ba..duk da ma Nabeel ya karbe ATM card din Abbood
din ba tare da ya gaya masa me zeyi da shi ba.shi dai Abbood da ya runga ganin wasu mahaukatan debit alerts se ya kira Nabeel yace .."Bud what the hell do you mean,
halan ma ka shirya talauta ni ne dare daya kam ban sani ba.." Dariya Nabeel yayi yana cewa wo wo wo wo brufh ..take it easy fa ..ni ban shirya haka ba..Amman dai to
let you know that more alerts are coming ,i swear se inda karfi na ya kare .."Haba Abbood ze sake magana Nabeel ya kashe wayar shi yana dariya ..Ko a lokacin wata 900,000 k ce ta fita daga account din Abbood..Amman really wasa Abbood yake masa
da ma ya tambaye sa din .kawai yana so yasan ko wani project suka samu Nabeel be fada masa ba..Chan kuma Najwa taga lallai se sun jawo Dada cikin wannan game din dan komi yafi tafiya dai dai..hakan kuwa akai Najwa tazo har gida ta same shi sukai magana ba tare da
sun bari Ammi taji ba.yaji dadin hakan sedai cewa yayi shi fa a matsayin shi na Dada mijin celebrant din yana da shawara .koda ta tambayi shi meye shawaran se yace .."
toh gaskiya na yarda da shawarar ku sedai nafi ganin cewa ayi mata sadaka se tafi son haka.kunga daman ita bata fiya son wannan bidi'oin ba .amman intaji sadaka za'a
mata zata fi yarda .."Tabbas Naajwan ma ta yarda da haka ..cewa tayi toh taya za'ai sadakan .."Nan ya mata bayani wanda bana jin me dame suke cewa..Gani nai kawai tana ta girgida kai fuskar
ta kalar tausayi.a karshe ma har kuka tayi ta share hawaye kafin Ammi ta dawo parloun ..koda ta dawo sunyi shiru da waccan maganar sun sako sabuwa inda Hanan take hannun
najwa tana noke .ita kuwa Hana tana gun Dada tana dan kamo gemun shi..da haka ta tafi sannan kuma tayi wa Abbood magana kamar yadda Dada ya sata .ta fadawa Nabeel ma
sannan ta fadawa Assadiq.gaba dayan su sunyi na'am da shawarar ..nan suka shiga shirye shirye ka'in da na'in..Bari mu dakata kadan anan muga yadda abun ze kasance a gaba ..doveys da divaa's watpaddians can any body guess what is about to happen ? ???
sorry again i know that its a short chapter but its better short than babu abi my sissy's i love yall..
TBC.....
YOU ARE READING
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...