220-225

853 92 8
                                    

ARCH.ABBOOD DAWOUD

       NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03

8TH MARCH,2020

220-225

_______________________________________

Bayan dogon hutu da nasha a yau na dawo wanda nake saka ran kammala wannan littafi insha Allah..hope you missed me ?

_______________________________________

Koda faa'eey ta tashi daga bacci da draman ta ta tashi.wai acewar ta lallai sedai in a cire kidney in Bunjaab a maida mata kayan ta,se kuma a cire tata a saka wa Ash..
lallai soyayya ,Ash ya zama dan gata.da rigimar ta tayi yawa se aka ce an yadda inda aka je akayi mata test kuma batayi fitting abun ba.daman Bunjaab ma seda aka gwada
nata sannan akayi.Se a nan ne ma faa'eeyn tadan ji sauki atleast tasan dan nata yaki yi ne ba'a saka masa ba.

A bangaren Ash kuma yanzu abun har ya fara bashi tsoro,dan wallahi be taba zaton akwai macen da ze iya sake jin ta a jinin sa ba,se gashi Bunjaab tana nema ta zame masa
karfen kafa..koda ma ita bata da niyyar yin soyayya da shi,amman ita kanta tasan tana jin shi a jikin ta ,tana ganin mutumcin shi...

Forward ,3 weeks later ..

A yanzu da Ash ya samu sauki se jiran healing din ciwo from aikin da aka masa ,har hira yake da Jaab kamar yadda yake kiran ta dashi,da yake su Umma basa kwana a hosp
din sedai suzo su tafi ,se wata alaka me karfi ta shiga tsakanin Ash da Jaab..ko da ma Faa'eey ta lura da hakan ,Amman se batayi saurin yanke hukunci ba.

se yau da suka zo asibitin ne da Umaima ta dau wayar baban ta tana ta danne danne tana game ,shine har ta shiga camera tana ta shirmen ta ..se ga pic din Jaab guda daya
wanda ma Ash ne ya dauke ta da kansa,kamar ma bata san ya dauke ta ba,gashi tayi kyau sosai gashin nan yayi wani kyau dashi.

Hankalin faa'eey ba karamin tashi yayi ba ,saboda daman tana zargin kamar sun shaku morethan yadda ya kamata,se gashi taga wannan pic din.maida wa Umaima wayar tayi
bayan ta fita daga camera din ta maida mata ita game .kwalla ce take ta kokarin fitowa daga idon ta saboda zata iya tuna tun da aka masu wannn aikin Ash ya dan chanja
da ta zata saboda rashin lafiya ne ,amman yanzu ta lura ba wata rashin lafiya ,kawai dai hankalin shi ne ya rabu.

Ta masa uziri saboda bata masa magana ba kuma bata nuna ta gan komai ba,se ma jan shi a jiki da ta kara sosai dan kam tana son mijin ta ..sedai abunda bata sani ba
shine a ranar bayan tafiyar su yayi propisng ma Jaab ta kuma amince zata aure shi .Amman tace sedai su zauna A US dan haka tayi alkawari da Baban ta,cewa yayi shi ya
yadda ,daga baya se susan yadda zasu tsara tunda tasan yana da mata.

Ita kanta Jaab tasan sedai ta nuna wa faa'eey gashi da haske amman wallahi bata isa tace tafi faa'eey kyau ba..Kuma tana son Faa'eey har zuciyan ta ga ma Umaima tana
sonta sosai.

The next day

Umma ce ta fara zuwa Asibiti kafin su faa'eey suzo saboda se umaima ta tashi da fever ,hakan ne yasa Umma ta ruga zuwa .Kafin zuwan Umma kuwa har Ash ya kira Yaya Ishaq
yana gaya mashi maganar son Jaab da Auren ta.toh gaskiya Yaya ya goyi bayan Ash dan shima a wannan lokacin yana son ya sake aure ne,ko da yake shi ba damuwa dan ya
sake aure saboda gaskiya matar sa Hibba irin matan nan ne da basu iya like ma miji ba ,kuma tasan da hakan .ko zama zeyi bata zuwa jikin sa,duk kuwa da cewa haihuwar su
daya kenan.

Sunyi akan shi yaya ne ze fada wa su Umma.hakan kuwa akai ,dan Yaya ya kira Umma ya fada mata ,sedai ita ta dauki maganar ne ma wasa kawai,dan bazata taba bari Ash ya
sake aure ba a yan shekarun shi,ace yana da mata biyu.Kai tun Asali ma ita ta tsani kishiya ,kuma ba wani danta daze yi mata biyu sedai in bata raye .

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now