ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIESWATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
16TH MARCH, 2020.
255-260
____________________________________
Daurin Auren na Faa'eey da Angon ta dan yaro sabon jini tear leda wato Abdullah ya hada mutane masu dumbin yawa,Daurin auren wanda ya gayyato malluma da sarakai da
masu kudi da yan kasuwa,sakamakon Gayya ce ta me martaba sarkin kazaure na wannan lokaci..Daurin auren wanda aka saka shi za'a daura a ranar Friday na watan da ake ciki
na wannan lokacin...Nabeel wanda ya isa gun Abbood ya same shi ba yadda yake ne ya kira Khalil yana shaida musu cewar yayi hakuri ,they cant make it ,Anan Nabeel yake cewa tunda an hanamu
ma har sau uku munyi fushi mu ..Sedai maganar da Papa yayi ne ta bawa Nabeel mamaki hadi da tsoro ,me hakan yake nufi kenan ?Shidai ya amsa shi da eh kawai komai eh ko tohm,da haka aka gama wannan waya ..
Abbood kuwa koda Nabeel ya dawo cikin dakin lokacin yana zaune yace shi lallai yau se yayi kuka ,ganin Nabeel ne yana bashi hakuri na daukan kaddara tasa ya fashe da
kuka,kukan me cike da hargagi wanda yace daga shi kuma ya rufe babin chinese har abada,amman for just wannan time din he wants to act like a 3 year old child yayi kuka,yayi
ihu yayi birgima ko ko an bashi hakuri yaki ji se sanda yaga dama,in ya tashi insha Alah he will focus and move on..Koda Nabeel yaga haka se ya fito daga dakin dan ya bashi guri,yasan yadda yake ji ,yasan da ciwo kuma yasan Abbood yayi enduring alot,so its high time ya barshi yayi
kururuwan shi yayi hargagin shi snnan su taru su healing,But God knows that Nabeel baya jin dadin abunda ke faruwa ..______________________________________
Nabeel a waje yayi waya kamar guda uku wadda ban san me yake cewa ba.sedai nasan wayar tana da amfani sosai sosai a rayuwar mutane da yawa,sannan tana da ciwo a rayuwar
akalla mutum biyu zuwa uku,sedai ya za'ai tunda yadda Allah yake so haka yake yi,kuma ba wanda ya isa ya hana faruwar duka abunda Allah yayi se ya faru .************************************
Ina Ango kuwa ,chan na gano shi shima ya na ta shan kuka,kukan wanda na kasa gane na farin ciki ne ko na bakin ciki,dan dai gashi yasha kwalliya kai da ganin sa kaga
angon da ya samu damar auren wadda yake so..da haka na baro shi zuwa later se naji me yake faruwa ..me makon ango ya ruga dariya se kuma ya ringa kuka?ko da na yi kano zuwa gidan su ango se naga kowa yayi jugum jugum ,wai ashe shi be gaya musu bazawara bace ,ita kuma Uwar shi tace wallahi bata yadda ba .Danta daya
raka a duniya na miji ya rasa da wacce ze fara aure se wadda tayi aure biyu shine na uku ,sannan kuma ma sa'ar sa..da wannan magana aka iske fadar sarki wanda hakan ya
jawo tozarci ga fada,Amman da yake Allah me hikima ne se gashi aure dai an daura shi amman da wani akasin Abdullah,Tabbas an daura auren faa'eey da Angon ta Abbood dawoud
Daurin auren da yayi wa Nabeel dadi kai kace nashi aka daura..Toh da yake a zahiri shima nashi saura one month dan Yan Buk dai sun tafi strike , so se kawai akai shawaan matso da bikin nasu kusa dan da akan bayan Sallah ne ,yanzu kuwa
ya koma kafin ma azumi ..Abbood kuwa ya gama kukan sa ya tashi ya yi wanka ya shirya cikin doguwar rigar shadda me kyau da maiko ga kyalli,kasancewar rana ce ta friday,daman kuma be ci komai
ba se kawai ya zarce da Azumi abunsa ,a ransa yana Addu'ar Allah ya kawo masa mafita..Nabeel wanda yake jiran Abbood su tashi suyi gida sakamakon kiran da Dada yake masa ne ya tsaya kallon Abbood,ga namiji har namiji amman wannan nature din nashi na
sanyin jiki na tare dashi,kai wallahi kallon fuskar sa a lokacin ma ze bawa mutum dariya dan gaba daya ya tabe fuska kamar yarinyar da take son zuwa birthday din besty
din ta kuma maman ta ta hana ta..
BINABASA MO ANG
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...