210-215

1K 88 7
                                    

ARCH.ABBOOD DAWOUD

       NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03

10TH JANUARY,2020

210-215
___________________________________

Kallon matar tayi sannan ta zauna da tana gaisar da mutanen dake cikin saloon din.duk da ma mutum uku ne cikin saloon din as clients se its ta hudu.sauran Matan su biyar
duk mata ne masu aikin saloon din..Tana zama aka fara attending dinta ..nan tace washing kawai zatayi ..Matar tana zaune ne ana shafa mata relaxer ..wanda ita kuma faa'eey
tana facing dinta ne ..

Faa'eey na cikin farin ciki wanda ya kasa boyuwa haka ne yasa kusan duk matan cikin saloon din suke ta kallon ta suna mata smiling,ciki kuwa harda matar wadda take dan
shafa cikin ta a hankali.ko da yake ma duk sunwa faa'eeyn kallon Budurwa,se da take waya da ,Mami ne ma sannan suka gane cewa matar Aure ce ..Anan ne ma sukaji cewa ciki
gareta inda har suke mata congrats,ko da ma ahankali take maganar .Amman hair attendant din ce ta fara cewa .."Woww,congratulations .."  Hakan yaja hankalin sauran suma
suke taya ta murna ,A hankali a hankali suke dan hira ,duk da ma faa'eey nata kokarin kiran Ash a waya amman ta kasa samun shi..cikin wannan halin ne se Matar take ce mata

.."kuma cikin ya kai how many months ?"  shiru faa'eeey tayi da farko se kuma tace .."Wai 4 months 3 weeks .."  "Ikon Allah .." Matar ta fada tana mamakin hakan ,ko dama
itan ma bata taba gane tana da ciki ba .Amman se taga kamar da mamaki ace mutum nada cikin kusan 5 months a jikin sa be sani ba..  Kallon faa'eey tayi tana cewa .."Tab
kinga kuwa nima ban taba gane ina da ciki ba .amman kuma naki dai da mamaki ace har cikin 5 months baki sani ba.."  faa'eey cewa tayi .."wallahi kam.." Daga nan bata
sake cewa komai ba tayi shiru wa hirar ma duka dan ita daman bata cika hakan ba,wai daga haduwa da mata a guri ka kma hira dasu har hirar ta gangaro ta taho inda yake
sirrin ka..

Ganin haka ne yasa ita ma matar tayi shiru tana ta danna wayar ta ..wayar faa'eey ce tayi ringing se tayi saurin kallon wayar ta tashi tana wani smiling me kashe zuciyar
ko wane ya ke kallon ta..ita kuwa wannan matar aga irin wannan murmushi da faa'eey ta tashi tana yi ..bata fita daga cikin saloon din ba.Amman tayi nisa dasu yadda basu
jinta tunda saloon din babba ne sosai,har ma ya kunshi parts parts..

Da yake faa'eey ta cire Abayar ta ta sama,se yayi sauran wata yar riga simple doguwa a jikin ta.wadda ta fidda sirrin jikin faa'eeyn kuma badan ta matse ta ba.da yake irin
cotton yard din nan ce.shi yasa har in ka ganta cikin rigar zaka ga yadda ta wadadtu da kira me kyau..A zuciyar wannan matar take cewa lallai faa'eey nada jiki me kyau
toh kunsan mata daman ,basu cika son suga wadda ta fisu ba.Nan take se taji kishin faa'eey ya kamata ..Hakan ne yasa ta bita da kallo bako kyaftawa ..Ita kuwa faa'eey
se ta yanke shawarar kawai bari ta fita ta zauna a mota tayi wayar ta ta gama ...

A ciki kuwa wannan matar tana ta faman tunanin cewa duk mijin da ya mallaki faa'eey ya haye,wai a cewar ta duk wanda ya samu faa'eey bazeyi bakin ciki ba.har ma take
auno yadda mijin faa'eeyn ze kasance ,dan ta tabbatar faa'eey bazata taba aurar mijin da be hadu ba..niko nace aiko Ash haddeden gaye ne ba wasa ..

A bangaren Ash yana kwance yake kiran faa'eey a waya ..da sanyin murya ta dauka wanda seda ya tsinci shauki a voice dinta,se yace "Babe murnan me kike haka ?"

Dariya tayi tace masa .."Im pregnant Baby,im pregnant and we are going to have a baby.."

cikin sanyin jiki da kasala yace mata .."Allah da gaske ?"  dalili kuwa shine Umma na gefen sa.dan tashin shi kenan su Umma suka zo,so shi kuma se ya farakiran faa'eey
kodan yaji ya akai a asibiti.dan ta mai text tace zata asibiti..shine yaji wannan labarin.Amma ga mamakin sa se ya kasa gaya wa Umman sa.duk kuwa da irin sakewar da suke
da ita na cewar su kadaine yaran ta kuma masa,so they are so close to each other amman se ya kasa gaya mata wannan good news din..

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now