ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES
WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
6/12/2019
125-130
_________________________
Assalamu alaikum dear lovelies,ya muke gaba dayan mu ,ya ibada ,Anyi sallah lafiya ?.Allah muna rokan ka da ka karbi dukkan
ibadun mu da mukayi.rokan mu da kukan mu.Ka amshi du"ain mu na Alkhairi ,Zunuban mu,kurakuran mu ka yafe mana su ya Allah..
Da wannan zanyi amfani da damar yiwa dukkan musulmin duniya barka da sallah .Allah ya maimaita mana Ameen.
___________________________
kamar yadda alkawari ya tashi ,an daura auren Assadiq da Rasheeda wanda ya samu halartar daruruwan mutane da manyan mutane
.daurin aure ne wanda aka yi shi cikin son rai da neman suna.dan Baaba Aminuddeen ya kashe kudi kan bikin nan sosai.
shiko Ango gashi nan ne kawai.ana daura aure yana gwada numbern Najwan sa.sedai taki dauka .a karshe ma kashe wayar
tayi a kokarin ta na ganin ta bashi damar tsaida hankalin sa wuri daya,sedai bata san cewa sake tunziro shi tayi ya
rasa natsuwar sa ba da sukuni.Dada wanda dashi da Nabeel sun halarci daurin Auren ba karamin dadi Assadiq yaji ba.kuma
ko ba komai ganin su yasa shi natsuwa aka daura auren su da Amaryar sa .
Ana gama daura Aure Assadiq ya kama hanya se gidan su Najwa wadda a safiyar ranar aka dawo da ita gida.tana daki ya isa
gidan.se Ammi ya gani ita kadai kuma itan ma kamar tana cikin damuwa.hakan ne kuwa dan tunda su Dada suka fita daurin
auren suka kasa natsuwa.da Ammin ma tana dakin Najwan tana ta kara bata Addu'oi ta karanta ko ta kara samun saukin
zuciyar ta .Daga haka ta fito parlor ta zauna tana kallon hanyar da su Dada zasu shigo.kwatsam se ga Angon da kanshi.
Shi kuma yana ganin Ammi ya fashe da kuka .ya gaji ya gaji ya gaji da dauriya .gwamma kawai yayi kukan shi ko yaji dadi.
izuwa yanzu ya tabbatar ya rasa Najwa a matsayin 1st and last wive dinsa.ga wata iriyar nasiha da Maaman shi ta mai
wadda tun safen yau take dawainiya da shi.to yama zeyi in beyi kukan ba,bayan yana ji yana gani an rusa mafarkin shi
wanda ya kawo matakin linta,kuma in dai yana so ya koma ga Allah lafiya dole yaji maganar da mahaifiyar shi ta gaya
mashi wanda itama ba fadin ta bane fadin Allah ne ? ita kuma ta dora da nata wanda ta kira shi da sunan umarni ?,ya zeyi
ne?
Kuka sosai yake yi wanda ya bashi damar cire Hular shi ya yar a kasa .Ammi kuwa zuwa tayi ta ruko hannun shi ta jawo
shi ta zaunar kan kujera .kma wa tayi ta zauna a gefen shi tana bubbuga kafadar shi alamar rarrashi wanda kuma hakan
sake karo gudun kukan nashi yake yi.Ammi ji take kamar ta rungume shi ko yaji sauki amman hakan baze yiyu ba.he surely
need a shoulder to lean and cry on.yana cikin wani hali wanda dauriyar da yayi ce ta jawo mashi.shi yasa daya ga abun
YOU ARE READING
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...