85-90

1.2K 101 1
                                    

ARCH.ABBOOD DAWOUD

       NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)

A K A AUNTY DIVAA

C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03

THURSDAY 4TH APRIL

85-90

_____________________________



Isar su gidan su naadi suka samu iso cikin parlour .a dai dai wannan lokacin naadi tana nan kwance an hada mata yan

abebadan da ake bata tana sha amma ta tasa su gaba tana kallo tana hawaye .hankalin ta sam baya jikin ta .damuwa karara

ta bayyana jikin ta.cikin haka mimi ta shigo dakin da sauri da sauri take cewa .."ke naadi ,mijin ki yazo yana parlour

wallahi.ki tashi ki shirya nasan yanzu zakiji mommy na neman ki.aiko kan ta karasa rufe bakin ta yussy ta shigo tana

cewa,"ya naadi,ya awesome yazo shida abokan shi.mommy tace wai kizo.."

tana fadin haka ta juya ta koma gun cousins dinsu da suka zo biki wanda wasu sun tafi amman wasu suna nan.koda yussy ta

fita Naadi ta kalli mimi tace .."ya zanyi?"

Mimi ta kalle ta tace .."i dont understand ya zakiyi ,mijin ki na kiran ki kam ai dole ki tashi ba maganan ya zakiyi.."

kallon mimi kawai naadi keyi a ranta kuma take ayyana mimi bata san ya take ji bane ba.A haka dai ta tashi tunda tasan

ba yadda zatayi ta saka wata atamfar ta holland exclusive made dinkin me kyau na gaske .mayafi ta yafa me kyau wanda

da ka ganta kasan Amarya ce.bata shafa komai ba.amman glowing da face dinta yake yi kadai is something else..

A parlour kuwa mommy ce take ta amsa gaisuwa cikin sakin fuska da surukan ta.bako shakka tana son Abbood sosai kamar

yadda shima ya yadda yana sonta da duk abun da ya shafi naadiyar sa wadda yake fushi da ita.amman yana arba da fuskar ta

yaji cewar kamar rabin laifin ta yana neman ya sauka daga cikin zuciyar shi.da sallama suka shigo itada mimi suna kallon

kasa kamar wasu munafukai ..suna shigowa mommy ta tashi ta shiga ciki abunta bayan sunyi sallama .A kasa suka samu suka

zauna suna kallon rug kamar masu gane ko shirin haddace zanen jikin rug din .Mimi ce ta fara cira murya ta gaishe su

.tare suka amsa suna kara musu ya gajiyar biki .A hankali naadi ta daga kai ta kalli Angon ta Abbood .ta gaishe shi cikin

ladabi da biyayya wanda ya kara tabbatar da nauyin shi da take ji a ranta.

Kallon ta daman yakeyi ya yi irin zaman nan nacin abinci gashi ya sarke hannun shi yana aika mata wani kallo na zallar

kauna da soyayya.ganin haka yasa mimi ta tashi ta shige ciki suma abokan sa suna ganin haka suka mike suma suka yi waje

.nan dai aka bari daga ango se amaryar sa.

Kasa kawai take kallo ta rasa inda zata saka kanta.dan ita bata so aka barsu su biyu ba .so tayi su gaisa kawai su tafi .

Amma se gashi mimi ce ta fara mata wannan iskancin...cikin wannan zancen zucin taji yace mata .."tohm ni na tafi se

anjima.."

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now