ARCH.ABBOOD DAWOUD
NA
UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIESWATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03
9TH MARCH,2020
225-230
__________________________________
Go Nabood,Go Nabood Go nabood..ihun yara ne ya cika stadium din ,sakamakon inter school sport da ake yi wanda ciki harda Nabood private school inda daliban Nabood suka
nuna cewa suma zakaru ne ta ko wanne fanni,Anyi foot ball sunyi second ,anyi quiz sunyi first,anyi debate sunyi first yanzu result aka fada wanda su suka cinye a tsakanin
schoolsuku da aka yi wannan program din..wannan shine dalilin da yasa ake ta jin ihun yara wanda murna ta cikasu ,ko su Nabeel ba karamin dadi sukaji ba sunyi murna sosai,gashi next month ma suna da wani program
din wanda su suka hada shi ,program ne akan drawing ,suna so su ga yadda skill din yaran su yakai akan zane zane ..da murna da farin ciki yan Nabood suka karbi cup suka
shigo Bus dinsu suka dawo school ..***********************************
Daga school ma gaba daya su najwa ne meena ,naadi duk gidan Dada aka wuto,nan aka zauna ana sake hiran abunda ya faru ,Tabbas duk wanda ya raina mutum yayi babban kuskure
saboda lokacin da aka fara kafa Nabood mutane nata suka ,wasu suna cewa ya za'ayi ace wai almajirai aka diba ake wani daukar nauyin su,a cewar masu fada ,wai salon se an tashi
daga school din ma su wuce suna barace barace da school uniform din,wannan wai zeyi tarnishing image din school din.se gashi abun ba haka bane ,kaf yaran sun maida hankali
suna karatun su,kuma yanzu suna yin turanci sosai ,wanda kuma aka ga sunki gane karatun se a maidasu business class ,suna koyon sana'a suna dan aikin da ba'a rasa wa ,
gashi yanzu school ta girmama ta habaka ,school food din su ma kawai abun kallo ne wanda daga foundation ake kawo abinci.sannan yanzu set din da zasuyi graduating za'a
debi yara uku a kaisa kasashen duniya su cigaba da karatu,wai wannan inba'a gode musu ba ai ba'a tsine masu ba..Dada ya kara tsufa Maasha Allah,gashi ya rame sakamakon ciwon sugar da yake da shi ,duk da ma yana kiyaye wa sosai amman ciwo da girma basu cika kawance ba.tare da iyalinsa
ana ta shan hira ana dariya ,ko da ma najwa nada tsohon ciki.shine ake ta tsokanar Assadiq wanda ya koma bawan Najwa ,komai shike mata masu aikin ma jansu suna mamakin
irin wannan soyyaya.ga yan yaran su gwanin sha'awa Hana da Hanan ..haka rayuwa ta cigaba da tafiya har najwa ta haihu danta namiji wanda yaci sunan Abbood .aiko yaro ya
kwashi arziki ba kadan ba yaro ya samu gata ga soyayyar da iyayen ke nuna msa ,sedai watan shi uku ya koma ga Allah..sun sha kukan su saboda yaran wanda ake kira da A
junior ya shiga ran kowa sedai ya zasuyi,daman chan ba dabarar su ce ba ta basu ..Meenan Nabeel ma tsohon ciki gare ta wanda take nan tana tura wa da kyar ,Naadi ma ta haihu tsiran haihuwar su kadan da najwa ..
Bari muyi gaba muga kuma me zamu tarar?
__________________________________
US ,new york ..Ash manyan maza kenan ake gaya muku wanda yanzu yake nan zaune da matar sa Jaab cikin son juna da kwanciyar hankali.sedai fa a cikin ransa in akwai abunda
yake kwana yake tashi da shi be fi matar sa ba wadda ya tabbatar yayi wa kansa babbar asara,wadda har abada baze taba maye gurbin wannan matar ba,tabbas yasan soyayyar
su da faa'eey daga Allah ne ,kamar yadda yasan cewa Allah ne ya daura masa soyayar Jaab wanda a yanzu take tafiyar da rayuwar ta da tsarin Addinin musulunci na gaske ,
kamar yadda duk wata shigar ta ma kamar hausawa take yi se kadan ne take sirka wa da india ko kuma nace english..Ba irin biyayyar da batayi wa Ash ,inaga shiyasa har yanzu
baya irin mugun maraicin nan.amman yasan yana son faa'eey ,yasan cewa soyayyar ta da ita ze mutu .kuma har yanzu be cire ran inta hakura zata koma masa ba.
YOU ARE READING
ABBOOD DAWOUD ✅
RomanceLabarin soyayya me dauke da sarkakiya ta rashin abunda wani ke so ,labarin me cike da soyyayya me kyau da tsafta da taba zuciya,labari me ban tausayi da dadawa rai..Labarin Abbood da Nabeel,Abbood da Naadi sannan Ashraf da faa'eey,se kuma Abbood da...