200-205

959 81 18
                                    

ARCH.ABBOOD DAWOUD

       NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)
A K A AUNTY DIVAA
C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03

22ND DEC, 2019

200-205

________________________________________

Haushin kanta ma ta fara ji dan se yanzu ta dawo hankalin ta ta yadda da bayanin nan da yaya ishaq yayi mata .shi da yake ma Ash din nada kyankyami,ko da haka kawai akai
la'akari ansan zeyi wahala ya iya neman mata..Aman kuma duba da haka ita ma ai ya kamata a mata uziri a matsayin ta na me son mijin ta da kishin shi sannan a gefe guda kuma
itama tana fama da matsananciyar bukata ai..shiru tayi tana sake auno abubuwa da dama .amman duk ciki da na sani wanda ta kasance keya ne yafi tsaya mata da damunta ..sam
yanzu kunyar Ash take yi tasan bata kyauta masa ba ko kadan..Amman kawai se ta sa a ranta kaddara ce kawai wadda ta riga fata .

Shi ko yaya da ya tabbatar ta gamsu se yayi mata sallama ya tafi.da daddaren ranar Ash ya dawo gidan ya sameta .fuskar sa ba yabo ba fallasa ya nufi daki inda take kwance
a gadon wanda bashi da girma sosai.kallon ta yayi yadda tayi saurin firgita ta taso ta zauna..

Sauka tayi daga kan gadon ta nufi gun shi bata jira komai ba ta rungume shi da karfin ta ta fara masa kuka me kashe jiki tana bashi hakuri ..shima kama ta yayi sosai ya
matse ta ajikin shi yana kukan shima.wani irin yanayi suka shiga na da na sani da tsantsar nadaman me suka aikata wa junan su.sun samu kamar 3 minutes suna wannan drama din
sannan ya jata suka zauna a bakin gadon ..kasa kallon shi tayi se kawai ta sake rungume shi tana sake ce mashi mistake ne da misunderstanding din junan su da sukayi,
shima ya yadda da haka kam sosai ma.Nan suka sake tabbatar wa da kansu sunyi na farko sunyi na karshe Insha ALLh.Dan sun shiga seventh month din su kenan da samun breakup din
da suka samu .

Sake rungume juna sukai suna sake jaddawa juna yadda sukai missing junan su..basu dau dogon lokaci ba suka fada wanka duk dama Faa'eey nata nokewa amman dai sun shana
son ransu sannan suka fito kowa ranshi yayi fari kal.A wannan dare seda suka faranta ran junan su.ji suka runga yi kamar wasu sabbin Amare.nidai da haka na yago jiki
na nayi tafiya ta dan cigaba da kawa rahoto.

___________________________________________

Ammi wadda taji dadin yadda aka hada mata suprise birthday din nan ya wuce misali.ta tabbatar da yadda iyalinta suke son ta .haka kuma sosai yayi mata dadi sannan ga
yadda akayi ciyar wa din nan yayi dadi.Video din event din ya watsu a kafafen yada labarai na social media wanda sarkin kano ya gani yaji dadi sosai ..haka ne yasa aka bi
tags din wanda aka yi se sunan Nabeel ya zama shi akai wa magana har dai kawo inda sarki ya sa aka sanar dasu cewa yana so suyi organising wani na 1000 people ..Abun
ya qayatar wanda shi kuma Nabeel yazo ya samu Dada da Najwa da Nabeel da Ammi da batun ..Aiko zunzurutun kudi Sarkin kano na wannan lokacin ya bayar aka kuwa hada shi
aka samo almajirai daga gurare suka samu cin Abinci .wanda kowa yaci ya koshi sosai.ko da ma be kai na Ammi varities ba saboda yawan yaran .Amman kam sunci ta tsoste sannan
kuma sun shi kaza da kifi ga salad ga lemo harma da ruwan roba.

sarki yaji dadin abun sosai duk dama ya ce a boye wanda yayi abun shi dan Allah yayi amman fa ya sha Addu'a sosai sosai.Kai se gashi wani me kudi ma ya sake tuntuba
nan ma se aka sake bawa su Nabeel kwangila sukai.Abunda suke shine ko na sarki ma seda suka saka kudin su ciki suma su samu ladan .Wannan ma hakan sukai seda duk suka
saka kudi masu yawa suma tunda ko wanne suna dinki wa yaran sannan da bukatun yau da kullum.kamar dai yanzu da ya kama lokacin sanyi ne ..Abbood da Nabeel da Najwa da
Assadiq se sukai ordern rigunan sanyi da huluna .kan kace me kaya sunzo riga guda 1000 hula ma haka da socks ..Nan fa sukai Abincin again Amman wannan karon a wani
fili sukai wai Abacha .katon fili ne mecin mutum ba adadi .nan suka runga raba wannan kayan sanyin da sauransu.

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now