95-100

1.2K 84 0
                                    

ARCH.ABBOOD DAWOUD

       NA

UMMKULTHUM AHMAD (MRS)

A K A AUNTY DIVAA

C.E.O DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @DIVAADOVEYSDIARIES03

10TH APRIL.2019

95-100



_________________________________

A safiyar ranar sunday Mami hauwa ta kira faa'eey dakin ta kafin kowa ma ya tashi.Gaban faa'eey na faduwa ta isa dakin

dan tasan zancen na gizo baze wuce na koki ba.ilai kuwa hakan ne tunanin faa'eey ya zama gaskiya.Mami ce ta tambayeta

kamar haka.."faa'eey wannan wayar wace ?"

Ta fada tana daga wayar dake aje gefen ta tare da kallon faa'eeyn cikin kallo me sanyi.

Shiru faa'eey tayi tana kallon kasa .A ranta kuma tana wasi wasin yadda zata bada amsar tambayar Mami.Muryar mami ce

ta kara karade kunnen faa'eey da sabuwar tambaya..."Da wa kike waya jiya ?"

Innalillahi wa'inna ilaihi raaji'un..faa'eey ce take ta faman mai maita wa a ranta..Mami ce ta sake cewa .."faa'eey dake

nake magana fa.."

tiryan tiryan kwalla ta fara gangarowa a fuskar faa'eey.still kuma bata yi magana ba.wani mugun tsoro ne ya cika mata ranta

ita ya zatayi ne kam?.

mika mata wayar Mami tayi tace .."bude wayan ki bani"..ba musu faa'eey ta karba ta bude tana rawar hannu da komai ta mika

wa mami wayar.call history ta bude ta duba .number ta gani daya har tayi scroling ta gama bata ga wata number ba bayan ita

Kallon Faa'eey tayi tace .."Numbern waye wannan kuma wannan wayan waye ,this is th last time da zan tambayeki .."

Kuka faa'eeyn ta fara tana bawa Mami hakuri.mami tace "ni ba hakuri nace kiban ba.tambayan ki nayi wayan waye kuma dawa

kike waya jiya?"

kai da ganin fuskar Mami kasan ba mutumci a kan ta.hakan kuma shi ya hana faa'eey magana.tsoro take ji kar ta fada .

bata san ya Mamin zatayi ba.

Wata tsawa Mami ta daka mata wanda ya tilastawa faa'eey fadin.."waya ta ce Mami.dan Allah kiyi hakuri Mami bazan kara ba

mami .."

Tana kuka take magiyan Mami tayi hakuri..Amman kam inaa .Mami na zargin yarinyan ta ta fada wata hanya wadda ta tabbatar

bata nuna mata ita ba.Se Mami tace .."waya baki ?" ta fada cikin zare ido.nan faa'eey ta kara tsorata.kukan ta ya dadu.

wannan hayaniyan ne yasa papa fitowa daga dakin shi ya iso dakin Mami.

Tambayan ta ya fara abunda yake faruwa.ce mai tayi ba komai.kawai lefi faa'eeyn tayi mata .yaje kawai ba wani abu.

shi kuma papa yasan cewa faa'eeyn na laifi .amman be taba jin hauwa na hayaniya irin haka ba.zama yayi a gefen Mami yace

.."faa'eeyza zo nan,me kika yiwa mamin ki take fushi irin haka ?"    Mami ce tace .."gatanan na tambaye ta taki fada

amman ni da kene ai.."

share hawaye tayi tace .."papa dan Allah kayi hakuri wallahi bazan kara ba .."

kallon mami yayi yace.."mami please jeki hada mun breakfast yunwa nake ji.." Ba musu ta tashi ta fita abunta .amma da wayar

ABBOOD DAWOUD ✅Where stories live. Discover now