01

2.6K 157 3
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*

*Bismillahir rahmanir raheem*
*Dukkan godiya sun tabbata ga Allah mad'aukakin sarki*
*Wannan littafi shekara 6 da na rubuta shi a cikin exercise book, I decided to write it online domin na fad'akar na nishad'antar daku, I hope u'll enjoy reading it*

*Gaba d'aya littafin nan sadaukarwa ne ga k'awayena masoyana kuma masoyan littafai na*

*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

*01*

'Yan mata biyu ne kyakkyawa, masu ji da kyau da gayu zaune a tantsamemen falo, Ba abunda babu a ciki na more rayuwa, naira tayi kuka a wajen, Tsakiyar su bowl ne na kayan marmari, Ta d'auki apple ta gutsiri tace

"Ke kuwa Meenal ya kamata ki bawa zuciyar ki salama, ki manta komai, Ki yafe mishi ki d'auki hakan a bisa k'addara", Wani mugun kallo ta jefa ma waccen tayi maganar tace " K'addara fah kika ce, abunda ya aikata ne k'addara, bazan tab'a yafe mishi ba, mutumin da ya zama silar rugujewar farin cikina, ban san k'unci, tashin hankali ba sai a dalilin shi, ta sanadin shi bacci ya k'auracewa idona, bashi da imani, bashi da tausayi, baya tsoron Allah, wallahi na tsani ganin shi, a duk lokacin da na ganshi na kan ji kamar na d'auki wuk'a na caka mishi"

"Ki rage zafafa abu Meenal, ki....", "Dakata Afra, maganganun ki ba abunda suke k'ara mun sai wutar tsanar shi", " Shikenan Allah ya kyauta", "Ameen", " Ni zan koma gida", Ta fad'a tare da mik'ewa, ta d'auki handbag da car key, "Ki gaishe da Dada", " Zata ji"

*Shekarun baya*

Alhaji Lawal Bukar hamshak'in mai kud'i ne wanda sunan shi yayi yawo a garuruwan Nigeria, D'an siyasa ne wanda Senator ne a garin Adamawa, Ya mallaki tarin dukiya, Asalin shi d'an Mubi ne a garin Adamawa, Iyayenshi na nan a raye a garin Mubi, Su uku ne gidansu,

Babbar yayar su mai suna Binta tana aure a da yaranta hud'u maza,

sai Alhaji Bashir shima hamshak'in mai kud'i ne yana aiki a ministry of foreign affairs matar shi d'aya Salma yayen su maza biyu tare Hafeez da Habeeb, basu cika zama 9ja ba saboda yanayin aikin shi.

Alhaji Lawal Bukar Matan shi biyu, Uwargidan mai suna Hadiza auren zumunci suka yi, Tana da yara uku maza Mubarak shekara 10, Mahad 8, Mujeeb 5, Amaryar Kwaise 'yar asalin Lebanon balarabiya ce, shekararsu biyar da aure bata tab'a haihuwa ba, Sunyi yawon asibiti likitoci sun tabbata musu lafiya take, lokacin haihuwar ne bai yi ba.

Zaman lafiya da kwanciyar hankali duka dangin suke, Ga tsantsar zumunci a tsakanin su, Allah ya azurta family da dukiya da tsantsar kyau, kunsan Fulani, Suna son samun 'ya mace a dangin, Iyayensu ma na son samun jika mace.

"Yaya ki kawo na yanka miki", " Bar shi ai na kusa", Hadiza wacce yaran ke kira da Mami ta fad'a", Kwaise wacce suke kira da Ummee tace "A'ah bana so ana wahalar mun da 'ya", " Ohh tun kafin tazo duniya kenan", Tayi dariya ta karb'i yankan alayyahu.

Tunda Mami ta samu cikin, tace idan ta haihu ta ba Ummi yarinyar, Wanda dukansu suke sa ran mace ce.

Idan ka gansu bara kace kishiyoyi bane saboda yadda suke zaman lafiya, Mijinsu Bappa mutum ne mai kyautatawa iyali, da sanin darajar mata.

Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah, Cikin Mami ya shiga watan haihuwa, Ranar asabar da yamma ta haifu yaron ta namiji, Dangin basu yi wani murna ba, Kasancewar sun sama ransu mace, Suma yaran gidan basa wani murna, Ummee kam hannu biyu ta k'arbi yaron, Ko barka aka zo sashenta ake zuwa, Nono kad'ai take kai shi ya sha wurin maman shi, but komai ita ke mishi.

Ranar suna aka sa mishi sunan mahaifin Ummee Abubakar Sadeeq, Soyayyar yaron ta k'aru a ran ta, Renon shi take sosai tamkar ita ta haife shi, Har lokacin ya'yenshi yayi, Ya fara wayo ya d'auka itace mahaifiyar shi.

Sadeeq na shekara biyu, Allah ma ji rok'on bawa yaba Ummee ciki, Farin ciki wurinta da dangi ba'a magana, Su Mubarak addu'ar su Allah yasa a haifi mace, Salma matar bashir aminiyar Ummee ce suna shiri sosai

"Yar' uwa abun murna ya samu ni ya kamata na fara sani, ba naji a shanun talla ba, Nayi fushi", Salma ta fad'a, " Haba yar' uwa kiyi hak'uri, ke na so na fara fad'awa, toh Dr na fad'awa Bappa ya fara yad'awa", "Dama nasan hakanan ba zaki k'i gaya mun ba, nayi murna sosai wallahi hadda rawa na taka", Ummee tayi dariya " Allah dai ya sawwake ki lafiya yasa ki haifa mana mace", "Ameen Allah ya kawo dai mai albarka", Sun tab'a hira, Kafin suka kashe wayar.

Mami na kula da Ummee sosai, ta kan hanata wasu ayyuka, Sadeeq an sa shi makaranta, Ummee ta k'ara samun lokacin hutawa, though tana da masu aiki amma ba komai take bari su mishi ba, tana da tsafta sosai ba komai take yarda mai'aiki ta mata ba.




*ZEELISH*💞

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now