*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu**_Haske Writers Association_*
*52*
_Sakina Marafa(Kwaise), Mom Abdallah😍(My boy) ina gaisheku💕_
Ummi da kanta ta shiga kitchen ta mishi girki mai rai da lafiya, Sau biyu yana cika plate yana cinyewa ba k'aramar yunwa ya kwaso ba, Dan tunda yaje bai ci abinci ba ko sun bashi baya ci, yana zargin sun saka mishi wani abu, ruwa kad'ai yake sha.
D'akin sa ya koma, ya kwanta, Yace Farda tazo su kwana tare, tak'i tace tana jin kunyar su Ummi, Bai fi minti 10 da kwanciya ba, Bacci mai dad'i ya d'auke sa, wanda ya kwana biyu bai yi irin sa ba.
Meenal baccin ta rabi da rabi ne, Gaba d'aya tunanin ta yadda zata wanke kanta, hanya d'aya ce ta gano masu laifi, dan ko ta masa bayani ba lallai ya yarda ba, Tunanin ta da zargin ta ya tsaya kan Layla, itace mai son mallakin dukiyar sa, a labarin da ya basu, an bashi takardu na property nashi ya saka hannu.
Washegari da safe suka yi shirin komawa gidan su, Driver ke jan motar, Al'ameen a gaba, Meenal da Farda a baya, Babu wanda yayi magana cikin su har suka isa, Al'ameen ya fara bud'e motar ya fice, Meenal da Farda rik'e da Haidar suka biyo sa a baya,
D'akin sa yake bi da kallo, yana nazirin tabbas wani ya shigo, Duban sa ya kai ga littafin, Ya ganshi yadda ya ajiye sai dai gadon d'akin shi a yamutse, wanda hakan ke nuna wani ya kwanta a kai, D'ankwalin Meenal da ya ganni, ya tabbatar da zargin sa, D'auka yayi ya fito ya nufi d'akin ta,
Tana kakkabe d'akin da ya soma k'ura, Tsaye yake bayanta yana k'are mata kallo tare da nazarin ta, Jin kamar mutum tsaye a bayanta ta juyo, Idon ta ya sark'e cikin nashi, Wani shegen kallo yake jifan ta da shi, da ya saka gabb'an jikin ta saki, A hankali ta sauke idonta k'asa,
"Ko ban ji wayar da kike ba, wannan kad'ai ya isa hujja", Ya fad'a yana mik'a mata dan' kwali, Da sauri ta d'ago, " Wallahi abunda kake tunani ba haka bane", "Me ya kai ki d'akina, bayan baki tab'a zuwa ba", Zata yi magana ya d'aga mata hannu, ya ajiye dan' kwalin kan gadon d'akin ya fice.
Zama tayi kan gado tare da furta " Ya Allah ka wanke ni daga zargin da bawan ka yake mun", Cike da k'arfafa ma kanta gwiwa da k'ok'arin kawar da damuwa, ta mik'e ta cigaba da gyaran d'aki.
Throughout ranar bai fita ba, Yana gida yana huce gajiya, Farda tayi abincin rana, Yanzu ma ta kammala na dare, Ta kaiwa Lameen sashen shi, Ta d'auki na Meenal ta kai mata.
Tana zaune falo, TV a kunne but ba kallo take ba, "Sannu da K'ok'ari", cewar Meenal, " Yawwa", "Dan Allah idan ba damuwa ina son magana dake", " Toh", Ta fad'a tare da k'arasuwa cikin falon, ta zauna kan kujera, Tasowa tayi ta zauna kusa da ita, Ta kama hannun ta tace " Ya Farda kiyi hak'uri da abubuwan da na rik'a miki a baya, Wallahi kin gama mun komai tunda har kika rik'e mun dan' da na kasa rik'ewa tamkar dan' da kika haifa"
Farda tayi murmushi tace "Ban tab'a rik'e ki a zuciyata ba Meenal, ke yar' uwata ce, idan na rik'e Haidar ai da'na ne", " Hakane Allah ya k'ara bamu zaman lafiya", "Ameen"
Ta nisa tace "Ina neman wani taimakon ki", " Ki fad'a in dai bai fi k'arfi na ba zan miki", Ta fad'a mata abunda ya faru tsakanin ta da Al'ameen tun daga ranar da ya dawo, Cike da tausayin ta tace "Wannan abun akwai rud'arwa, coincidence Al'ameen ba zai tab'a fahimta ba, ba tare da proof ba",
" Ina zargin da sa hannun Layla, taimakon da zaki mun ki bani had'in kai wurin gano ta, ke kike aiki office d'aya da ita, zaki fini kallon movement d'inta, da sanin me take ciki", "Nima na dad'e ina zargin ta akan haka, In Shaa Allah zan taimake ki Meenal ko dan Al'ameen ya fahimci babu sa hannun ki a ciki", " Nago....", Tayi saurin hana ta "Ni dake mun zama d'aya, bari na tashi na tafi yana jirana", " Toh", Ta fad'a tana jin zuciyarta na mata ba dad'i kishi, tayi saurin karanta addu'a, Ta rasa wane irin kishi ne take ma Al'ameen.
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...