12

926 75 2
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

   '''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*
   
          '''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

  ® _*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*_

    
   *12*

   Daidai za su shiga ciki, Meenal taci karo da wani d'an saurayi wanda ba zai wuce Lameen a shekaru ba, Tura ta yayi baya, Cikin fad'a yace "Are you blind?, bakya kallon gabanki?", Ta murgud'a mishi baki tace " Ai kai ne blind d'in", Hannu ya d'aga zai sharara mata mari, Yaji an rik'e hannun, Al'ameen ya saukar da hannu yace "Da kayi gigin marin ta, ko shakka babu jinya zata koma kan ka", Wani banzan kallo yaron ya bishi dashi, Al'ameen yaja hannun Meenal suka bar wurin, Yaron ran shi ya b'aci matuk'a baya son tada rigima a asibitin saboda jikin Yayarshi da ko shakka babu sai ya fitar wa Al'ameen da jini ya had'a da k'anwar tashi.

   Bappa ne ya rufe Hafeez da fad'a akan me zai zo dasu, Maza ya mayar dasu gida, Ba musu ya mayar dasu.

     Meenal tace " Ya Lameen na tsani wannan", "Wa kenan lil-sis?", " Na asibiti da ya ture ni", Yayi dariya yace "Nima bana son shi, ya tab'a lafiyar my one and only sis", " Idan ka k'ara ganin shi ka mishi duka, ka fasa mishi bakin da yace Am blind", Dariya sosai Yayi yace "Toh Lil sis"

   Mubarak ya kasa ya tsare, yana d'akin zaune kusa da yarinyar, addu'a yake tayi Allah ya tashi kafad'un ta, A hankali ta fara motsi, idonta na motsi alamun bud'ewa, Tana bud'ewa suka had'u da na shi, Wata fad'uwar gaba yaji da bai tab'a jin irin ta ba, A rud'e yace "Baiwar Allah kin tashi", Ido ta bi shi dashi cike da mamaki, D'aya bayan d'aya take bin mutanen d'akin da kallo, har idon ta ya sauka kan Mahaifiyar ta, Tace " Mummy", Cike da murna ta k'araso ta kama hannun 'yar ta tace "My daughter", Mubarak ya kasa d'auke kan shi a kanta, wani irin kyanta yake gani, bai san kyanta ya kai haka sai da ta farfad'o.

        Mahaifiyar ta ke gaya mata abunda ya faru, Mubarak ya shiga bata hak'uri, tayi saurin hana shi tare da cewa K'addara ce Allah ya riga ya rubuta hakan zai faru, Ya yaba da hankalin ta yaji ta burge shi.

      Dr yace zata k'ara kwana uku kafin a sallame ta, Iyayenta sunce zasu zauna da ita, Su Bappa su koma gida, Mubarak bai zo haka ba ya so ko shine ace ya zauna, amma ya d'auki alwashin kullum sai yazo ya gan ta, Cike da mutunta wa da godiya aka rabu, hadda exchanging numbers suka yi.

    Mubarak ya koma gida cike da tunanin yarinyar nan, duk yadda yaso ya cire tunanin ta ya kasa, Alla-alla yake safiya tayi ya koma.

       Al'ameen shirin exams suke ta canza aji, ya dage karatu yake ba wasa, yana sanya Meenal tayi karatu itama yarinyar akwai k'ok'ari, har double promotion aka mata daga nursery 2 aka kai ta primary 2, Yanzu primary 3 4 za ta, itace k'aramar ajin su, wayon ta ne yazo d'aya dasu har ma ya so ya zarce nasu.

       Sadeeq ya kammala SSCE, Bappa na Neman shi admission Cyprus, Su Habeeb na shirin dawowa kad'an ya rage su had'a masters d'in su, Bappa yace ba zasu dawo ba sai sunyi masters.

    Al'ameen ya k'uduri niyyar a 9ja zai yi karatu  ba zai nisa da Meenal ba, baya jin zai iya kwana d'aya ba tare da ya sata a ido ba.

      Mubarak tun da safe ya tashi ya shirya zuwa asibiti, Ya shiga sashen Ummi da Mami ya gaishe su, Ya shiga sashen Bappa yana wanka, bai tsaya jiran shi ba sauri yake yaje yaga ya lafiyar ta.

      Ita kad'ai ya samu a d'akin, K'amshin turaren da taji yasa ta d'ago ta kalle shi, Ya mata murmushi yace "Patient ya jiki?", Tare da samun wuri ya zauna, Da far'a tace " Jiki Alhamdulillah", "Allah ya k'ara lafiya", " Ina su Mummy?", "Taje gida tayi wanka", " Aka barki ke kad'ai", "Ina tare da brother na yaje ya siyo ruwa", " OK", "Ya sunan ki tunda ba za'a gaya mun ba sai na rok'o", Tayi murmushi tace " Ai baka tambaya ba", "Sai na tambaya", Tayi dariya tace " Nusaiba", "Nice name, ni kuma Mubarak", Tayi nodding kai

     Nan yayi ta jan ta da hira, Suna dariya kamar sun dad'e da sanin juna.

     Brother ta ne ya shigo, Ya gaishe da Mubarak ya amsa, tare da tambayar sunan shi, Yace "Ibrahim Khalil but anfi kirana da Khalil", " Kana da suna mai kyau", Yayi murmushi, Yana kama da Yayar tashi sosai.

    Shak'uwa sosai ta shiga tsakanin Mubarak da Nusaiba, Yayin da soyayyar junan su ta kamu su ba tare da sun ankara ba.

    *Kuyi managing wannan*

*Follow*
*Vote*
*Like*
*Comment*

*ZEELISH*💕

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now