*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*
'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*® _*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*_
*03*
Yau Ummi ta tashi bata jin dad'in jikin ta, Da ta mik'e sai taji jiri, Shiru Mami bata ganta ba har la'asar, Kullum tana zuwa su gaisa suyi hira, Mami tacewa Mujeeb "Wai lafiya ban ga Kwaiseh ba", Mujeeb yace " Nima yau ban ganta ba", "Kamar ya, baka ganta ba, ba kaje ka gaisheta bane", Ta fad'a cike da fad'a, " Naje aka ce tana bacci", "Ohh oo bari naje naga lafiya"
Al'ameen ne ya fad'awa Ummi, Mami tazo, Ta mik'e da k'yar tana jin jiri ta sameta a falo, Zama tayi tana maida numfashi, Cike da Kulawa Mami tace "Lafiya, bakya jin dad'i ne?", " Tunda na tashi jikin nawa sai a hankali, kasala, jiri da yawan tashin zuciya", Dariya Mami tayi ta furta "Alhamdulillah", Da mamaki Ummi ta kalleta, " Al'ameen ya kusa samun k'anwa, dan wannan karan In shaa Allahu mace ce", Ihun Al'ameen suka ji, Suka juyo suna kallon shi, Tsalle yake yana fad'in "Ummi zata haifa mun little sister da zan rik'a goyawa", Dariya ya basu
Mami tace " Yanzu Kwaise baki san ciki ne dake ba, bayan signs na masu ciki duk ya bayyanar miki", "Wallahi Yaya ban sani ba", " Toh Ciki ne dake, amma tashi muje asibiti dan ki k'ara gaskatawa"
Mami taja mota zuwa asibiti, Dr ya tabbatar musu tana d'auke da ciki na wata biyu, Ummi tayi murna sosai har bakin ta ya kasa rufowa, Haka suka dawo gida kowannen su fuska d'auke da annuri, Bappa ma yaji dad'i sosai.
Al'ameen throughout ranar far'a yake, halin shi na murtuke fuska bai motsa ba, Duk wanda ya gani sai yace mishi, "Ummi zata haifa mishi little sister"
Lokacin da cikin Ummi ya fara girma, Kullum Al'ameen sai ya shafi cikin, Yana fad'in "My little sister am eager Ummi ta haifu ki, I love you so much", Yayi kissing cikin, Ummi ta kalle shi tayi murmushi, Yanzu ko laifi yayi tace " Idan ya k'ara ba zata haifa mishi little sister ba", Toh ba zai k'ara ba.
Yana kan keke yana zagaye gidan, Baba mai gadi yace "Aminu ka koma cikin gida zanyi shara", Ko kallon Mai gadin bai yi ba, halin miskilancin ya motsa, " Aminu baka ji ina magana", "Kayi sharar ka na hana ka, kuma kar ka sake ka watsa mun datti", Baba mai gadi yabi yaron da kallo a ranshi yace " Yaron nan sai yayi isa tun yana k'arami ma kenan"
*Bayan wasu watanni*Ummi kwance kan doguwar kujera, Cikinta yayi tsini sosai, zata iya haihuwa at anytime, Al'ameen yazo yana fad'in "Ummi tomorrow is my birthday, me zaki bani gift?", Ta shafa kan shi tace " Zan maka addu'a sosai, and I will suprise you with the best birthday gift ever", Ya kama hannun ta yayi kissing yace "I Love you Mum, zanje wurin Bappa na gaya mishi", Ya fice ba tare da ya jira me zata ce ba, Tabi shi da kallo tana addu'ar " Allah ya raya mata shi, yasa ta haihu lafiya"
Washegari ta kama alhamis, A ranar Ummi ta haihu santaleliyar yarinya mai tsananin kyau, Gashin kanta a kwance luf, har ya sauka kan fuskar ta, Nurse na gaya musu mace ce, Mami ta rungume ta, Al'ameen a guje ya shiga d'akin haihuwar dashi aka zo dan kafewa yayi sai da ya biyo su, Shi ya fara d'aukar babyn yace "Wow My little sister is so beautiful, Ummi kin bani best birthday gift", " Yes My boy na baka", Ya tsurawa babyn idon, Yana ji wani farin ciki na ratsa shi, Mami tace "Bamu mu ganta", Ya make kafad'a " Ku gani a hannu na, tana bacci kar ku tashe ta",
"Al'ameen fah anyi k'anwa, ba zamu tashe ta ba, ganinta zamuyi mu sa mata albarka", Yace " Gata toh, Mami ki mata addu'a da yawa", "Toh"
Labari ya bi dangi, Ummi ta haifi mace, Kowa murna yake, Kakannin su Dada da Hamma ba k'aramin murna suka yi ba, Bappa ma baki yak'i rufowa, Su Mubarak an sanar dasu kuma an tura musu hoton baby, Sunyi murna matuk'a, suna ta yaba kyanta, Suna jin kamar su gansu a 9ja.
Al'ameen ya kasa ya tsare, yana manne da baby, Yayi ta kissing d'in ta, 'Yan barka ma da k'yar yake basu ita.
Habeeb yana ganin babyn yace "Ya samu mata", 'Yan uwa kowa yace an bashi, Ummi a ran ta ta k'uduri idan baby ta girma Habeeb zata aura, ko dan matsayin salma a wurin ta.
" Bani matata in gani", Habeeb ya fad'a, "Ka nemi matar ta ka, My little sister tawa ce ni kad'ai", Habeeb yayi dariya ya lura lamarin Al'ameen hadda yarinta, Yace " Toh bani little sister ka na gani", Ya mik'a mishi yana cewa "Ka rik'e ta sosai, kada ta tashi tayi kuka", Habeeb yace " Toh Yayan baby", Ya tsura mata ido a ran shi yace "Allah yayi halitta anan, ba k'aramin kyau babyn nan zata yi ba", Ya sumbace ta a goshi, Al'ameen yace " Waya ce ka mata kiss, bani k'anwata", Ya karb'eta, Habeeb yayi murmushi.
A school kowa sai da ya sanarwa an haifa mishi little sister, Har wayan da bai tab'a ba magana ba ranar ya musu.Anyi suna wanda ba'a tab'a yi a family ba, 'Yan uwa duk sun hallara, Yarinya taci suna Amina Meenal, Wanda Al'ameen ne yace asa mata, Kusan ankon aka suka yi da Meenal, Rabin pictures na sunan na Al'ameen da Meenal ne.
*Comments*
*Vote*
*Follow**ZEELISH*💞
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...