*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*23*
*Bayan shekara d'aya*
Abubuwa da dama sun faru na jin dadi da sab'anin haka, Al'ameen ya zama k'waro a cikin school d'in su, Babu wanda ya iya zane kamar shi, Idan Quiz za'a dashi ake zuwa, Sunan shi yayi yawo cikin makarantar, Ya k'ara zama handsome guy.
Sun saba da Farda sosai, Duk makarantar ita kad'ai ce macen da yake shiri da ita, Tana ta dakon soyayyar sa ba tare da ya sani, a kullum k'aunar shi k'aruwa take a ran ta, Sau da yawa ta kan yi zazzab'i na k'aunar sa, Fahad na tausaya mata wani lokaci ya kan ji kamar ya sanar da Al'ameen, Sanin halin shi zai yarfa ta yace bata da class yak'i fad'a.
Layla bata sake waiwayar shi ba, ba dan bata son shi, tana tsoron abunda zai biyo baya, Tunanin ta wacce hanya zata b'ullo.
Meenal ta k'ara girma da wayo, Shirin shiga js3 take, Ta zama yar' budurwa kyawunta na k'ara fitowa, Gata da tsananin son gayu, Ummi na siyan mata kayan gayu da kwalliya, Habeeb ya k'ara rikicewa akan son ta.
Bikin Ya Mubarak da Nusaiba, Ya Hafeez da Hafeeza nata matsowa, saura wata d'aya, Shiri ta kowane b'angare suke, Meenal tafi kowa zumud'in bikin, ba dan komai ba sai dan Yayanta zai zo.
Sanye take ta riga da wando, tayi parking gashinta da ya sauka gadon baya, Tana saukowa daga stairs, rik'e da waya, Ummi dake zaune a falo tana kallo taji an fad'o jikinta, "Haba Meenal yaushe zaki girma ne?", Ta tab'e fuska da shagwab'a tace " Kai Ummi Am just 11 fah", "11yrs ai kin girma da a k'auye ne da yanzu a tsayar miki da miji", " Tabb abomination , Ummi wai meye ma aure?", "Idan kin k'ara hankali zaki sani", " Shine mace da namiji suna son juna ko, kamar ke da Bappa", "Meenal kina damuna fah, kije ga Yayanki Habeeb can kuyi hira", Sai a lokacin ta lura dashi, yana zaune kan dining table yana cin abinchi but all his attention na kanta, a ranshi yana ayyana tasan so kenan, zai fara nuna mata son da yake mata.
Da murmushi tace " Ya Habeeb", "My one", " My one kuma?", Ya d'aga mata gira, Tayi smiling, Kujerar kusa dashi ya nuna mata ta zauna, "Meyasa bakya son hira dani?", " Ba haka bane Ya Habeeb", "To yane?", " School da na dawo nayi tafi islamiyya", "OK naji, promise duk ranar da kike free, zaki rik'a zuwa muna hira", Kafin ta bashi amsa wayarta ta d'auki k'ara.
Da murna tayi receiving, " Yayana", ta fad'a tana dariya, "My lil sis Ya kike?", " Lafiya lau", "Ya school?", " Lafiya Yayana, zan shiga Js3", "Wow my sis ta zama big girl", " Yaya zaka zo bikin Ya Mubarak?", "Of course zanzo", Ta buga tsalla tace " Can't wait to see you Ya Lameen", "Same My lil sis", " Zan tafi school, I will call u later ", " OK take care Yayana", "I will lil sis" , "Bye", " Bye", Tayi hanging up
Habeeb wani abu yake ji a ranshi, zuciyar shi tace "Are u OK, kana kishin Yayan ta uwa d'aya uba d'aya", Yayi saurin kawar da abunda yake ji, " Muje musha ice cream", "OK Let me dress up", Sun je wuraren shak'atawa da Habeeb, yana ta sako mata kalaman soyayya, ba tare da ta fuskanci karatun nashi ba.
Al'ameen na zaune a library yana zane, K'amshi mai dad'i ke fita daga jikin shi, Idan yana zaune a wuri babu mai tunkarar wurin, Allah yayi mishi kwarjini da mutane ke jin shakkar shi, Farda ta zauna nesa dashi, k'amshin turaren shi na dukan hancin ta, Duk wani motsin shi akan idon ta, Tana k'ara dulmiya a kogin son sa, Yana d'ago kai, sukayi four eyes, Ya sakar mata murmushi, Rasa natsuwarta tayi, Babu macen da Al'ameen zai kalla ko ya mata murmushi ba tare da taji wani abu a ran ta ba, Saurin rufe ido tayi, Ta dafe zuciyarta dake harbawa akan tsananin k'aunar sa, A tsorace ya taso a tunanin sa bata da lafiya, Yana zuwa dab da ita , bugun zuciyar ya k'aru, Hannunsa ya d'aura kan goshin ta yaji ko da zafi, Wani zirr taji daga kanta har k'afarta, " Are u OK?", Taji muryarsa, "Fever", Taji zuciyarta ta furta, dan bata san lokacin da bakinta ya fad'a ba, " Muje na raka ki clinic", "Don't worry nasha magani, yanzu zan koma gida na k'ara sha", " OK let me drop you", "Nop nagode", " OK Allah ya bada Lafiya", "Amin", Al'ameen baya rok'on mutum, idan ya maka tayi sau d'aya kace a'ah, baya sake na biyu, Ya k'uduri a ran shi duk yarinyar da ya furta ma so, tak'i shi ba zai k'ara waiwayar ta ba.
Tana shiga gida, Ta fad'a kan gado ta fashe da kuka, " So masifa ne, har yaushe son Al'ameen yamun illa haka" Hoton shi ta dauk'o ta manna a k'irjinta, ta lumshe ido, Haka take yi ta samu sassauci duk lokacin da soyayyar sa ta matso mata.
*Young star Club*
Kid'a ke tashi, Maza da mata na rawa, wasu na shan taba, wasu giya, wasu shisha, babu irin kayan mayen da babu a wurin, Layla sanye da mini skirt, da riga sleeveless, Tana tangal tangal rik'e da kofin giya, Wani yazo ya rungumota ta k'ugu, Suka shiga bad'ala, Tunda Al'ameen ya koya mata hankali, Ta fad'a rayuwar nan, Nancy ta bata shawarar ta haka zata manta da shi, Tsawon shekara d'aya tana yi ta kasa mantawa dashi, Son shi na nan a ran ta, har ynzu bata cire rai da auren shi ba.
Al'ameen ya zana Meenal, ya kai aka mishi frame mai kyau sosai, Ya saka a ciki, Ya b'oye in a safe place.
Aunty na breastfeeding twins, Al'ameen ya shigo, "Aunty ya kamata ki yaye yaran nan, ki gansu Mashaa Allah", " Ina jira ne idan munje bikin su Mubarak, nan ko naso yaye su ba wanda zan ba", "Gani ko baki san ni na yaye Meenal ba", " Meenal daban ai, wannan sai su hanaka bacci", Yayi dariya yace "Bazaki bani ba dai Aunty", Kiran Daddy ya hana ta bashi amsa, Ta ajiye su ta tashi, Da far'a suka nufi Al'ameen, sun saba dashi sosai, Yana matuk'ar k'aunar su.
" Saura sati biyu naga My lil sis, nasan ta k'ara girma", Ya fad'a cike da far'a, "Gaskiya kana son k'anwar nan taka", Cewar Fahad, Yayi smiling bai ce komai ba, Farda dake gefen su tana ji, tashin hankali ne ya saukar mata, tunanin kewar shi da zata yi (Ni zee nace ba fah ya tafi kenan ba, daga zuwa biki)
Meenal kullum countdown take na zuwan Yayanta, Ummi kanta tana murna, tana son ganin yaron ta, tayi kewar shi, Allah yayi ta da tsananin kawaici shiyasa bata nunawa.
An kai lefe na gani na fad'a, Both Dangin Nusaiba da Hafeeza sun jinjina dukiya irin tasu Bappa, dan kuwa kaya tsadaddu aka zuba.
Timetable na exams d'in su Al'ameen ya fito, yayi daidai da bikin su Mubarak, Dafe kai yayi ganin timetable, Ya furta " Ya salam", "Me ya faru?" Fahad ya tambaya, Yayi shiru idan yana b'acin rai baya son magana.
Haka ya koma gida rai a b'ace, Duka plans d'inshi na zuwa 9ja ya ruguje, ba zai ga Meenal d'in sa da Ummin sa, bai san ya Meenal zata ji ba, Throughout ranar bai fito d'aki ba, Yace ma Aunty kansa ke ciwo, Abincin da ta kawo mishi, ko bud'ewa bai yi ba.
Ya cire damuwar rashin zuwa 9ja, Yayi facing studies d'in sa, Littafi ne a gaban sa yana karatu in a quite place, "Al'ameen k'odan boko, all the time karatu", Fahad ya fad'a yana k'arasuwa wurin shi, " Ina da buri sosai a rayuwata Fahad", "Meye burin ka?", " I want to become a billionaire, sunana ya shahara a fad'in Nigeria, ina so nama k'anwata gatan da babu wani Yaya da ya tab'a ma k'anwar sa", Ya jinjina kai yace "Allah ya cika ma burin ka", " Ameen"
"Amma baka da burin aure?", " A yanzu babu aure a tsarina, har yau ban ci karo da irin matar da nake so ba", "Duk matan dake cikin school d'in nan", Dariya Fahad ya bashi yace " Mace mai class nake so, wacce ta amsa sunanta mace", "Toh Allah ya baka, mukam zamu nemi daidai mu mu lallab'a", Yayi smiling
Farda tayi murna sosai da exams yazo daidai da tafiyar Al'ameen, Tana tafiya kamar ance kalli gefe, taga wani na k'ok'arin sa zare wallet a aljihun wandon Al'ameen, Ihu ta buga tace " Thief", Mutanen wurin suka ankara dashi, Yana k'ok'arin guduwa suka kama shi,
Al'ameen ya bita da kallo, tayi kamar ba itace tayi ihun ba, Tana shirin wucewa yasha gabanta, Kanta ta sunkuyar k'asa, zuciyarta na harbawa, ga k'amshin turaren shi dake hargitsa ta, Tana jin kamar s rungume shi ko ta rage wani rad'ad'i, Sorry da Thank you sune kalmomi masu mishi nauyin fad'a, Yana son gode mata ya kasa, "Allah ya biya ki", Ya furta a hankali, Murya a sanyaye tace " Ameen", Ta rab'a ta gefenshi ta wuce, "She is Decent", Ya furta a fili.
*Follow*
*Vote*
*Like**ZEELISH*💕
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...