*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*
'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*24*
Yan'uwa na nesa da kusa nata zuwa, Gobe za'a fara biki, Meenal nata d'okin ganin Yayanta, Yau Su Daddy zasu zo not knowing ba da Lameen ba, Da kanta ta gyara d'akin, ta killace komai a muhallinsa, tasan Komai nashi tsaf ne, Ta turare d'akin da turaren wuta mai dad'i.
Saloon suka tafi da Afra, daga can su wuce gidan k'unshi, Basu dawo ba sai dare, Gashin Meenal yasha gyara, sai k'yalli yake ya zubo a gadon bayanta tamkar wata yar' india, Hannun ta da k'afa sun sha k'unshi ja da bak'i.
Harabar gidan cike yake da mutane wanda duk samarin gidan ne da abokan su, Mayafin ta ta datse a k'ofar mota, Gashinta ya bayyana ta juya tana k'ok'arin zare gyalen, Idon Khalil dake jingine jikin mota ya sauka kan gashin, "Mashaa Allah", Shine abunda ya furta, " Mu tafi koh", Cewar Aunty Hafsa(K'anwar Mamansu), Ya juyo batare da yaga fuskar mai gashin ba, "Har kun gama?", " Eh dama ba dad'ewa zamuyi ba, kwatancen gidan Amarya da zamuje jere nazo su mun, nayi ta kiran wayar Mami bata d'auka ba, ta Ummi kuma a kashe", "Dama baku san gidan ba?", " Karime kad'ai tasan gidan wai kuma ba zata gane ba", "Kai Aunty Karime kamar tsohuwa", " Kai ma ka fad'a"
Meenal burinta ta shiga cikin gida tayi ido da Ya Lameen, Aunty Saratu ta gani da gudu ta rungume ta Tace "Ina Ya Lameen?", " Yana London", "Kai Aunty bana son wasa", " Au dama bai gaya miki ba tare zamu zo ba, exams suke", Durk'ushewa tayi anan ta fashe da kuka.
"Wani irin sakarci ne wannan, Meenal kin girma fah, ya kamata ki sani", Ummi ta fad'a cike da fad'a, " Kiyi hak'uri Meenal da ya gama jarabawa zai zo", Aunty ta fad'a cikin lallashi, "Kada ma ta hak'ura, Yarinya tana girma tana mayar da kanta sakarya"
Anan ta yarda mayafinta da jaka, Ta tashi tana kumbura baki ta hau sama.
Kuka tasha a d'akin hadda su birgima, sai da tayi kukanta mai isar ta, Ta jawo waya ta kira Lameen, Ganin kiranta gabansa ya fad'i yasan bata ganshi ba, Yana d'auka ta sake fashe mishi da kuka, A daburce yace "Sorry lil-sis, Dan Allah daina kukan", K'ok'arin tsayar da kukan take ta kasa, Ya shiga lallashin ta sai da ya tabbatar tayi shiru yayi hanging up.
Ya dafe kai yace " K'anwata rigima", Zanen da yake ya kasa cigaba, Ya ajiye ya kunna karatun Qur'ani ko zai rage mishi damuwa.
Washegari kowa yaci kwallliya ya k'ure a daka, banda Meenal tana d'aki ko fitowa bata yi ba, Afra tazo gidan ba irin knocking da bata yi ba, Meenal tayi banza tak'i bud'ewa, Ta sanar da Ummi, Tace "A k'yaleta zata gaji ta fito", Afra tace " Toh", Jiki a sanyaye rai ba dad'i.
Yan'uwa kowa nata tambaya ina Meenal, Aunty ma tayi ta dubawa bata ganta ba, Ta tambayi Afra, Ta sanar da ita tana d'aki tak'i bud'ewa.
"Meenal bud'e d'akin Yayanki na son magana dake", Aunty ta fad'a, Tayi shiru, Jin muryar Lameen na cewa " Ki bud'e Lil -sis", Aunty kiran shi tayi a waya ta sanar da shi, Da sauri ta taso ta bud'e, Ta karb'i wayar hannun Aunty, "Haba lil-sis, kina so na kasa karatun exams koh, na fad'i jarabawa", Tayi saurin cewa " A'ah" Tana gigriza kai kamar yana ganin ta, "Idan bakya son haka, ki tashi ki shirya ki saki jikin ki, ana gama exams zanzo", " Toh Yayana, kayi karatu sosai", "Zanyi, tashi ki shirya, make sure kifi kowa kyau a bikin nan", Ta fashe da dariya, Suka kashe cike da nishad'i.
Aunty tace " Meenal d'in Lameen, shi kad'ai ke iyawa dake", Tayi dariya.
Cikin 1hour, ta shirya light make up tayi, sai ranar dinner zatayi heavy make up, Tayi kyau sosai cikin atamfarta ta anko wacce aka mata gown da ita, Afra ta kalleta tace "Kinyi kyau sosai", " Thank you", Ta mik'a mata waya "Snap me na tura ma Ya Lameen", Pics ta mata kusan kalla goma, Ta mishi sending baya online, Harabar gidan suka fito, Motoci sun fara tafiya wurin event (Kamu).
Habeeb sakin baki yayi yana kallon Meenal, Har suka k'araso wurin motar shi, " Ya Habeeb ina wuni?", Suka had'a baki, "My one kinyi kyau sosai", Tayi smiling tace " Thank you", Shi ya bud'e mata gaban mota ta shiga, Afra ta shiga baya, Yaja su zuwa venue.
Ya dawo gida so tired, exam na ranar ya chaja mishi brain, Yayi having shower, Yaci abinchi, Yabi lafiyar gado, Wayar shi ya jawo, ya kunna data, Images suka shigo, Message d'in ta ya fara bud'ewa, Bai san lokacin da ya tashi zaune ba, "My lil sis is looking so takeaway" Ya furta a fili, Ya sumbaci hoton, Number ta yayi dialing, har ta tsinke bata d'auka ba, hakan ya tabbatar mishi suna can wurin biki, "Allah ya tsare mun ke k'anwata da sharrin samarin zamani",
Kamu yayi kyau sosai, Anci ansha an k'oshi, anyi rawa da hotuna kowa ya watse, Meenal ta dawo gida a gajiye, bata bi ta kan wayarta ba, Ruwa ta watsa, tayi sallah, Bacci mai nauyi ya d'auketa.
The next day Ranar alhamis, akayi walima, Meenal tayi shiri cikin lifaya, Gashinta ya kwanto ta gaba, Tayi kyau ba kad'an ba, Tayi pics ta tura ma Lameen, Tana turawa yana bud'ewa, Ya yaba kyawonta, Yayi dialing number ta, Ringing d'aya ta d'auka, " My lil sis wane kyau ai sai ki rikita mutanen wurin", "Kaii Yayana", " Allah kuwa", Tayi dariya, "Ki kular mun da kanki kinji", " Tohm Yaya", "Allah ya tsare ki", " Ameen", "Ki gaishe dasu Ummi", " Zasu ji"
Wata arniyar riga ce a jikinta dake bayyana duka surar jikinta, rigar iya gwiwa ce, Tayi crossing legs tana busar sigari, Layla kenan.
Matashin saurayi ne ya shigo d'akin, Ya nufota, Ta dakatar dashi da hannu "Am not in d mood", Ta fad'a tana hura iskar sigari, Fita yayi rai a b'ace, Yasan matsalarta nada nasaba da Al'ameen yana jin haushin shi sosai, saboda yadda Layla ke son shi.
" Ya kamata ki manta da Wanda baya sonki, ki amshi mai sonki", Nancy ta fad'a, "Bazan tab'a mantawa da Al'ameen ba, son shi yamun mugun kamu, a cire so gefe, ko dan cin mutuncin da yamun bazan mantawa dashi ba, sai na d'auki fansa" Ta fad'a tana huro sigari har ta hanci.
Su Meenal nata shirin dinner, Wani dank'areren lace red and black mai tsada da yasha had'add'en d'inki ta saka, Mai make up har gida tazo ta mata, ta d'aura mata head, Tsayawa bayyana muku irin kyaun da tayi k'auyanci ne, Kyau sosai tayi bana wasa ba.
Kowa ya ganta sai yace "Wow", Habeeb kam sakin bakin kawai yayi yana kallonta, A ranshi yana hango ba k'aramar budurwa za'ayi nan gaba ba, Tun a yanzu hips sun fara fito mata.
Hall na dinner ya k'yatu yayi kyau ba kad'an ba, Amarya Nusaiba Da Hafeeza duk sai da suka yaba kyaun Meenal.
" Wow guy d'in can ya had'u", "Omg Soo handsome", Naji wasu group na yan'mata na fad'a, Na d'aga kaina dan ganin wane guy ne wannan.
Sanye yake da farar shadda wagambari, d'inkin tazarce, ya d'an tara gashi sanye da hula fara mai ratsin bak'i, Hannun shi d'aure da agogo bak'i(Rolex), Kaf'arshi sanye da takalmi bak'i, covered na kamfanin mister, Fari ne sosai kyakkyawa, mai cikar hibba, Ibrahim Khalil kenan.
Yana tahowa rik'e da wayar shi IPhone x max, Hankalin shi na kan wayar, Meenal ta taho rik'e da cup na Chapman, Sukayi kaura lemon ya zube a jikin shi, Zai yi masifa ta d'ago, idon su ya had'u, Bakin shi ne ya sark'e ya kasa furta ko A, Gabanta ne yayi wata irin fad'uwa, Tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa, Murya a sanyaye tace " Am sorry", "It's okay", Ya fad'a a gaggauce, Ya bar wajen, Sauke ajiyar zuciya tayi a ranta tace " Yana da sauk'in kai"
Friends d'in shi yace ma zai je gida ya dawo, A mota tunanin yarinyar yake, yana so ya tuna inda ya santa, "But she is extremely beautiful", Har ya isa gida da tunaninta, Yayi wanka ya sake shiga cikin blue shadda, Yayi kyau sosai.
Meenal taga dawowarsa a ranta tace " Wannan akwai d'aukar wanka", Ta cigaba da harkokinta, tasha rawa ita da Afra, Kallo ya koma kansu anata musu lik'i, Khalil ta burgeshi, ya shiga lik'a musu d'ari biyar-biyar, Wurin rawa takalmin ta ya murd'e, ta tafi zata fad'i, ido ta runtse tana jira taji ta a k'asa, Khalil ya rik'eta, Jin an rik'eta ta bud'e caraf cikin nashi, Dukkansu sunji fad'uwar gaba, Habeeb ne ya taso yazo ya jinyeta, shi a dole kishi, Khalil ya tab'e baki with I don't care manner.
Yana driving zasu koma gida, abokinshi Hanif dake gefe Yace "Ko dai son yarinyar nan kake?", Dariya yayi yace " Baka da hankali, me zanyi da k'waila", Hanif ya kwashe da dariya yace "Kai fah baka da mutunci", " Ai gaskiya ne, kawai ta burgeni ne", "To ni ina so", " Ah wasa kake wannan me ta sani", "Irinsu idan suka girma zo na rad'a ma", " Kai fah d'an iska ne" cewar Khalil, Sukayi dariya.
*Follow*
*Vote*
*Like**ZEELISH*💕
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...