*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*37*
Doctor ruwa ya watsawa Meenal ta farfad'o tana fad'in, "Dan Allah kace wasa kake bani da ciki", Ta fashe da kuka, Farda ta rungumeta tana lallashin ta, Ummi tace " Dan Allah Dr a cire cikin nan", A razane yace "What bama wannan aikin", Ummi ta durk'usa k'asa tace " Ka taimake mu ko nawa kake so zamu biya ka", "Baku kula da tarbiyar yaran ku sai sun kwaso abun kunya kuzo kuna kuka a cire", Yaja tsaki ya fice,
Wani kukan bak'in cikin Meenal ta saki, Ummi zuciyar ta tafarfasa take, Tace " Farda jeki mota ki jira mu", Ta jawo hannun Meenal, Suka nufi wurin Nurse Halima, Ummi tace "Meenal na d'auke da juna biyu", A tsorace Halima tace " What!", "Ina so ki taimaka a cire cikin nan", " Tabb, ai Hajiya asibitin nan ba'a cire ciki, idan aka gano ni zan rasa aikina",
Ummi tace "Zan baki kud'in da zasu ishe ki har k'arshen rayuwar ki", " Ba cire cikin ba, ina tsoron kada ya tab'a lafiyar ta", "Ko da zai yi sanadiyyar mutuwa ta ban damu ba", Cewar Meenal, Halima ta kalleta cike da tausayawa tace " Ku dawo gobe da safe", "Mun gode sosai", Ummi ta fad'a, Suka wuce, Tabi bayan su da kallo cike da tausayawa.
Ummi ta gargad'e su akan kada su fad'awa kowa har Bappa, Farda kam kanta ya k'ulle, toh waya ma Meenal ciki, Ba dai Khalil ba, Tasan Meenal yarinya ce mai natsuwa garin ya haka ta faru, sai idan fyad'e aka mata,
A Daren daga Meenal har Ummi babu wanda ya runtsa, alla-alla suke safiya tayi aje a cire.
Nurse Halima kwana tayi sak'e-sak'e, Bata san yadda zata b'ullowa lamarin ba, Hak'ik'a sun bata tausayi, amma cire ciki ba k'aramin abu bane, Ya zama dole ta samu hanyar da ba za'a salwantar da cikin ba.
Lokacin da boka ya d'ibar wa Layla ya cika, Da taje yace za'a mata wankan magani na sati d'aya, Da anyi ta auri Al'ameen ta gama, Babu musu ta amince, Ta tub'e ya mata wanka, t
yana ta shasshafa ta, Ya gama tasa kaya, Yace ta dawo gobe,K'arfe bakwai na safe asibiti tama su Ummi, Nurse Halima tama Meenal yan' gwaje gwaje, ta kalle su fuska d'auke da damuwa, Tace " Za'a cire cikin amma da sharad'i d'aya", Ummi tace "Muna ji", " Zata rasa mahaifar ta", A tsorace suka kalli Nurse, Ta d'aga musu kai, Meenal kuka tasa, tana son a cire cikin amma har ga Allah bata son ta zama juya, "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Allah ya bamu ikon cinye jarabawar nan", Ummi ta fad'a, " Amin, In shaa Allah komai zai zo muku da sauk'i", "Wane sauk'i Nurse, uwa d'aya uba d'aya", " Hakane", Ta fad'a cike da tausayawa.
Suna komawa gida, Ummi ta nufi sashen Bappa, Yana zaune falon sa yana karanta jarida, Ta sanar dashi, Sakin jaridar yayi ta fad'i, Yayi salati ya sanar da Ubangiji, "Hak'ik'a mun had'u da jarabawa, Allah ya bamu ikon cinyewa", " Ameen", "Yanzu sai a tara kowa a sanar musu abunda ke faruwa", " A'ah" Ummi tayi saurin cewa, "Ya zama dole domin a wanke Amina daga zargi", Ummi tayi shiru tasan ya zama dole a fasa tulu, Ranar wanka ba'a b'oye cibi.
Meenal na shan laulayi, yau ciwo gobe lafiya, Ummi na bata kulawa ta musamman haka Farda.
Al'ameen bai san abunda ke faruwa ba.
Daddy yazo da matar sa, da twins, Aunty ta fuskanci Ummi na cikin damuwa,
Bappa ya sanar da yaransa duka yana son ganin su, Dada ma tazo, Duka sun hallara a babban falon gida hadda Farda, Al'ameen ya zauna a takure kansa k'asa, Gabansa na fad'uwa, Bappa ya bud'e taro da addu'a, Yace " Abunda zan sanar daku zai matuk'ar girgiza ku, wani iftila'i ne ya faru da Family nan", Kowa a tsorace yake kallon Bappa, Ya zayyane musu komai,
Al'ameen wata razanannar k'ara ya saki, Farda jikinta ne ya hau rawa, taji tamkar a mafarki, Mami da Aunty kuka suka fashe dashi, Kowa ka kalla tashin hankali ne a tare dashi, Basu tab'a ji ko ganin irin haka ba ko a cikin film, Dada ma kuka take hadda su majina.
Tsawon minti 20 babu wanda yace komai, Ya Mubarak yayi k'arfin halin cewa "Me zai hana a zubar da cikin?", Daddy yace " Shine daidai", Ummi tace "Nurse tace idan aka cire zata rasa mahaifar ta", Dada tace " Zancen banza ne, wallahi sai na jik'a mata darbejiya tasha cikin ya zube, ba dai a haife shi ba, wannan abun kunya har ina"
"Ya zama dole a haife sa", Kowa ya juyo yana kallon saitin da akayi maganar Nurse Halima ce ta fad'a tana shigowa, Ta k'araso cikin falon ta zauna akan kujera, Tace " Ku gafarce ni na shigo muku kai tsaye, amma kada kuce zaku zubar da cikin Meenal", "Ke baki isa ki fad'a mana abunda zamu yi ba", Cewar Dada, " Akan wane dalili?", Daddy ya jefo mata tambayar,
Ta nisa tace "Ina neman yafiyar ku da farko, ni mai laifi ce a gare ku, Amma ku saurare ni, Ina tunanin abunda zaku ji zai sa ku samu natsuwa, ku rage son cire cikin nan", " Ba abunda zamu saurara, algunguma", Dada ta fad'a, "Kiyi hak'uri Dada, muji me zata ce", Cewar Bappa, Ya juyo kan Nurse, " Muna sauraren ki",
"Shekaru ashirin da biyar da suka wuce, An kawo Hajiya Kwaise na labour asibitin mu, Ta haihu da' namiji, Aka kawo wata mata da tayi had'ari, ganin tana k'ak'arin mutuwa mukayi mata CS aka cire babyn Namiji, Babyn Hajiya Kwaise Allah ya masa rasuwa, Ana haka itama waccen matar Allah ya mata rasuwa, Babynta nata kuka, naji tausayin yaron na d'auke sa na musanya shi da babyn Kwaise, na kai mata mai raye, Al'ameen ba d'an Kwaise bane"
Ummi ta taso ta shak'e ta tace "K'arya kike Al'ameen da' na ne ina ji a jikina", Bappa ne ya taso ya janye ta, Daddy yace " Ya sunan Matar?", Tace "Salma, ta iso Nigeria daga London", Kowa ya d'auki salati, Mamaki da ban al'ajabi ya cika su.
Bappa yace " Allah mai komai, mai kowa, Mai yadda yaso a lokacin da yaso, Ashe Al'ameen dan' Salma ne", Daddy ya taso ya rungume Al'ameen yace "Ashe kai da'na ne shiyasa nake k'aunar ka",
Ummi tace " Duk da bani na haife ka ba Al'ameen ina son ka tamkar dan' da na haifa da cikina", "Nima ina k'aunar ki Ummi, ina jin ki tamkar mahaifiyata", Ta rungume shi suna kuka, Bayan yan' koke koke,
Bappa yace " Wani Al'amari sai ubangiji, Babu wanda ya tab'a zaton haka, Cikin lokaci d'aya Allah ya kawo haka, Allah yasan dalilin da yasa haka ta kasance tsakanin Amina da Aminu, Shiyasa shak'uwar su tayi yawa tun suna yara, Yanzu Meenal zata cigaba da rainon cikin ta har ta haihu, idan ta haihu za'a had'a su aure",
A razane ta d'ago ta kalli Bappa tace "Ka taimake ni Bappa kada ka had'ani aure dashi", Al'ameen shima ji yayi baya son auren ta, Bai san ma taya zasu yi zaman mata da miji ba, Yace " Bappa kayi hak'uri kada a had'amu aure", Daddy yace "Auren ku kamar anyi an gama", Dada tace " Tabbas",
Farda kuka ta saki, Kowa ya juya yana kallon ta, Bappa yace "Auren ku na nan Farda lokacin da aka saka, amma kiyi hak'uri yanzu kun zama ku biyu", " Na fasa auren shi, na hak'ura", Ta fad'a tana sake fashewa da kuka, Ran Al'ameen ya sosu da jin furucin ta yafi son auren ta akan Meenal, Ba zai tab'a iya zaman aure da Meenal ba, Itama Meenal bata san ya zata yi zaman aure da wanda ta tsana ba, Ta d'auki alwashin sai ta zubar da cikin, tunda dama plan ne Nurse ta had'a ba zata rasa mahaifar ta.*NOTE* AL'AMEEN BAI SHA NONON UMMI BA, IDAN BAKU MANTA BA FARKON LITTAFI BATA SAMUN RUWAN NONO BA SAI MADARA YA SHA, DAGA BAYA DA AKA BASHI BAI KARBA
_Comments dinku kad'an gaskiya, nima zan rage yawan typing_
*Follow*
*Vote*
*Like**ZEELISH*💕
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...