27

764 61 1
                                    

*MEENAL WA LAMEEN*

*Written 2013*
*Posted 2019*

   '''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*
   
          '''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*

       _*Haske Writers Association*_

*27*

  Al'ameen yayi shiga cikin designer suit, wanda yasa aka mishi specifically a London, Sun matuk'ar yi mishi kyau, Turaruka ya fesa sun kai kala goma, Duka tsadaddu, Kiran wayar shi aka yi ya d'auka, "Sir komai ya kammala isowar ka kad'ai muke jira", " On my way ", Ya fad'a a dak'ile,

     Meenal shiga tayi cikin Abaya, wacce design d'inta ya had'u, Tayi kyau a ciki, Ta yafa mayafi, Tayi make up, Kunsan fah gwanar gayu da kwalliya ce, Ta masifar yi kyau, Knocking k'ofa Al'ameen yayi, Handbag d'inta ta kamfanin LV, ta d'auka ta fito, Kallon juna suke kowannen su ya ma d'aya mugun kyau, " Yayana ka had'u", Meenal ta furta, "Kema kin had'u", Suka sa dariya a lokaci d'aya, " Mu tafi ko", Ya fad'a tare da kama hannun ta,

Sun fito harabar gidan, Su Ummi duk sun shirya cikin shiga ta alfarma, Prado 2 ne fake, Ummi, Mami Bappa, suka shiga d'aya, Sadeeq, Habeeb, Al'ameen da Meenal suka shiga d'aya, Ya kira Farda yace ta same su a can bazai samu biyowa ba, yana tare dasu Bappa, Taji ba dad'i, but ta basar, Dama tayi shirin ta cikin abaya da ta yi mata matuk'ar kyau, Driver ya aiko ya d'auke ta.

   Su Ya Mubarak kwatancen wurin aka musu, Kusan a tare suka isa Katafaren company, motocin suka yi parking, motoci ne birjik a bakin wurin, wanda duka babu k'aramar mota, motocin millions ne, Su Bappa a ransu ayyana suke meye had'in Al'ameen da wannan company, Kowa a garin yasan da Company tunda aka fara ginin sa, wanda tsabar had'uwar sa, yasa ake ta maganar shi a gari, ba'a tab'a gini irin shi ba, wasu na cewa kaf fad'in Nigeria babu mai had'uwar shi.

     Al'ameen ne ya fara fitowa rik'e da hannun Meenal, Farda sakin baki tayi tana kallon kyau da had'uwar shi, Tana jin son shi na ratsa ta tare da godiya ga Allah da zai zama miji a gare ta, Farda tazo ta jera dasu, Suka saka shi a tsakiya, Yadda suka jero kamar matan sa, Kowa a gurin na yaba kyawu irin na wad'annan mutane uku (Lameen, Meenal, Farda),

    Taro ne na bud'e company, wanda mallakin Al'ameen ne, ( MEENAL WA LAMEEN CONSILIO), Manyan mutane sun hallara ciki kuwa hadda Governor, Commissioners da Minister of works and Transport, Bappa dasu Ummi mamaki, farin ciki da al'ajabi ne ya dabaibaye su lokaci d'aya, Ga tarin tambayoyi wanda Al'ameen kad'ai ne zai baza su amsar su, Governor ya yaba k'wazo irin na Al'ameen, babu young Architecture kamar shi, Building d'in kanshi shi ya zana shi, Ummi kan hadda hawayen ta na farin ciki, jin yadda ake yaba d'an ta, Tana ta godiya ga Allah, Meenal ma kan baki har kunne, Wannan katafaren company na Yayanta ne kuma da sunanta da nashi,
Lallai ba k'aramin so Yayanta ke mata ba, Reception aka yi, a wani k'yataccen Hall cikin company,

Anci an sha an k'oshi, Kowa ya watse saura  Al'ameen da family shi, Ya zagaya dasu wurare a ciki, Bappa ya kalle shi Yace "Ya isa haka Al'ameen, ba zamu iya zagaye wurin nan, yanzu haka k'afata ciwo take", Mami tace " Nima wallahi", Suka sa dariya, Ummi tace "Al'ameen ina ka samu kud'i da har ka gina CONSILIO bamu sani ba,

Yayi smiling yace " Tun kafin na kammala makaranta, kasancewar k'arewa ta a fagen zane, Mutane da dama a London ke bani zanen gidaje na musu su biyani mak'udan kud'i, Daddy ya sani shi ya bud'e mun account ina zuba kud'in, Naira ban tab'a ci a ciki ba, Ana haka gwamnatin garin ta bani contract, Wanda na samu mak'udan kud'i kusan 200million, Nayi godiya ga Allah, domin kuwa Allah ne ya zab'e ni ba iya wa ta bace ko dabara, Cikin haka na fara tunanin bud'e CONSILIO nawa na kaina, wanda idan na gama makaranta, zan zuba ma'aikata a ciki, ina running abuna, na nemi shawarar  Daddy, ya bani goyon baya, Na fara zanawa da kaina, Wata biyu na d'auka ina zane, dana gama na samu k'wararrun builders na basu aikin, na kuma ce musu aikin sirrin ne bana so kowa yasan nawa ne, Cikin ikon Allah komai ya kammala da taimakon Farda wacce tayi designing cikin company, Interior designer ce",

    Bappa yace "Allah Mai kowa mai komai, shi zamu yi wa godiya, domin kuwa shine ya d'aukaka ka lokaci d'aya", Ummi tace " Hakane, Allah Alhamdulillah",  Mubarak yace "Am proud of you Al'ameen", Duka Yayyen shi sunyi  Congratulating d'in shi tare da nuna jin dad'in su,

   Meenal tace "Ummi ga Farda", Da Mamaki Ummi ke kallon ta tace " Dama kece Meenal ke ta bani labarin ki", Rungumeta Farda tayi, Al'ameen da Mamaki yace "Kin Santa ne?", " Yar' Cousin d'ina ce Fawwaz, Kakar mu d'aya da Babanta", Kowa a gurin yayi Mamaki, Al'ameen kam rasa yayi murna zai yi komai, Farda baki har kunne, murna fal a ranta,

Suka d'unguma su duka suka koma gida har Farda.

   _Kuyi managing wannan, bana jin dadi wlh_

*Follow*
*Vote*
*Like*

*ZEELISH*💕

MEENAL WA LAMEENWhere stories live. Discover now