*MEENAL WA LAMEEN*
*Written 2013*
*Posted 2019*'''ZEE YABOUR'''
*Follow and vote me on wattpad @ZeeYabour*'''IN DEDICATION TO'''
*Zakiya Musa Bala*
*Hafsat Salisu*_*Haske Writers Association*_
*50*
*Not edited*
Yan sanda wurin binciken su suka ga motar Al'ameen fake gefen titi, Sun lek'a ciki basu ga komai ba, Sai wayoyin sa dake kashe, Key motar a jiki, Jan ta sukayi suka nufi police station, DPO ya kira ya sanar da Bappa yace kuma zasu cigaba da bincike.
Farda da Meenal sun dawo gidan Bappa anan suka kwana, Kowannen su zaune fuska babu walwala, Meenal ta koma gefe ta rakub'e da counter a hannu, tana tasbihi, Yanzu batun la'asar ake but babu wanda ya saka abinci a ciki, Gidan ya zama tamkar gidan makoki.
Shigowar Bappa yasa kowa ya d'aga kai ya kalle shi, dafatan suji labari mai dad'i, "Yan sanda sun tsinci motar sa babu shi, wanda hakan ke nuna tabbacin sace shi akayi", Salati da kuka ne ke tashi a falo, Meenal gumtse baki tayi tana kuka, " Ya Allah ka kare shi ka kub'utar dashi", Shine addu'a da take nanatawa a zuciyarta,
"Addu'a ya kamata ku mishi ba kuka ba", Cewar Bappa, Ummi cikin shessshek'ar kuka tace " Wane azzaluman ne suka d'auke shi, Me suke buk'ata daga gare shi?", "Allah yasa ba kidnappers bane", Cewar Mami, Mubarak yace " Idan kidnappers ne da yanzu sunyo waya, Allah dai ya kub'utar dashi", Duka suka amsa da "Ameen"
"B'acewar Sir Aminu ya matuk'ar bani mamaki", Cewar wani ma'aikaci, " Hmm ba kai kad'ai ba, ni kaina abun ya d'aure mun kai", "Kuma kar kuyi mamakin da had'in bakin makusancin shi", " Sosai kuwa", "Ko su waye Allah ya tona musu asiri", " Amin dan alfarmar Annabi",
Labari yabi kafafen sada labarai Arch.Aminu Lawal an sace shi, Mahfuz da Layla na zaune a d'akin hotel inda suke bad'alar su, Aka hasko hoton shi a TV, Mahfuz yayi shewa yace "Kuyi ku gama, ba zaku tab'a gano mu ba", Layla tace " Wallahi kuwa", Ta d'auki remote ta kashe tare da cewa "Kayan haushi"
"Yaron nan fah akwai taurin kai", " Bari kawai, Dantse ya sanar dani yak'i sa hannu, na umurce su da su cigaba da azabtar dashi su mishi barazanar mutuwa", "Hakan shine daidai"
Da k'afa ya harbe shi yace "Kaii tashi", Cikin tsananin b'acin rai Al'ameen ya d'ago, " Ka shirya barin gidan nan ko har yanzu taurin kai zaka mana", Kawar da kansa yayi gefe, "Ka juyo ka saka hannu ko ka bak'unci lahira"
"Sai da ku kashe ni amma bazan taba sa hannu ba", Naushi ya kai mishi a baki, Gefe ya fashe da jini, Ya shafa yaga jini ya d'ago yana kallon sa da idonsa da suka rine suka zama jajir , A zuciyar sa tunanin irin hukuncin da zai ma wanda suka yi sanadin kawo shi nan yake,
Dantse mamakin taurin kai irin na Al'ameen yake, tun da yake bai tab'a ganin mutumin da bashi da tsoro irin shi ba, wanda azaba bata sa ya karaya, Fita yayi d'akin yana tunanin hanyar da zasu b'ullo masa.
Meenal kanta ke masifar ciwo, tana jin sanyi cikin k'ashinta, D'akinta da tun kafin tayi aure, Ta nufa, Kwanciya tayi taja bargo ta rufa, Zazzab'i ke sun rufe ta, Bata tab'a tunanin rashin Al'ameen zai zama damuwa gareta ba, Dama mutuwa yayi haka zata ji kenan,
Farda damuwa biyu ta had'a mata, Ta rashin Al'ameen, ga rashin lafiyar Haidar yana ta mata rigima, Jikinsa yayi zafi sosai, Ta rasa ya zata yi, bata son tunkarar kowa ta k'ara mishi matsala,
Rungume take dashi ita kad'ai a falon sama tana hawaye, Meenal k'ishin ruwa ne ya dameta, Ta fito, Har ta wuce su, ta dawo, "Lafiya dai?"
Farda ta d'ago tace "Haidar ne babu lafiya", A rud'e tace " Subhanallah, meya same shi?", Tana k'ok'arin karb'ar shi, "Ciwon ciki da zazzab'i"Jikin shi ta tab'a, zafi sosai Kuka ya saki yana mik'a hannu Farda ta d'auke shi, Duk k'ok'arin Meenal ya yarda da ita yak'i, Dan dole ta mik'awa Farda shi, Yayi lamo jikinta yana ajiyar zuciya, Da kallo tabi shi tana jin tsananin so, k'auna da tausayin yaron ta, Tayi gangancin rashin shayar dashi, Gashi yana gudunta, Hawayen da taji na son zubo mata tayi saurin sharewa tace "Ki fad'awa Mami ku kaishi asibiti" Bata jira amsar Farda ba ta wuce.
An kaishi asibiti an mishi allura, Bayan sun dawo gida ta kwantar dashi yayi bacci, Tunani ta shiga yi, Suwa zasu sace Al'ameen, a iya saninta bashi da wasu abokan gaba, but gobe zata je office d'in sa tayi bincike.
Al'ameen bacci ya k'aurewa idon sa tunanin hanyar kub'uta yake daga miyagun mutane nan, Abunda ya hana shi guduwa yana son yaji suwaye sukayi sanadin kawo shi, Yasan yadda zai b'ullowa lamarin.
Breakfast da aka jera kan dining table babu wanda yabi ta kan sa, Da k'yar Ummi tasha kunu, shima sai da Bappa da Mami suka yi ta ban baki, Farda tunda safe ta fice bata jira fitowar mutanen gidan ba, ta bar Haidar wurin Inna.
Office na Al'ameen ta shiga, ta duba drawers tana binciken takardu, Gaba d'aya important documents d'inshi tasan anan yake ajiye su, ta duba bata gani ba, "Ko ya canza musu wuri", Ta tambayi kanta, Wata paper ta hango, ta jawo ta duba, Ta filin shi ne but fake,
Da tsananin mamaki take kallon takardar, Tunanin ranar da sukayi kaura da Layla yazo mata rai, " Definitely Layla has something to do with this, ya zama dole nayi bincike ",
Mayar da komai wurin sa tayi ta fito,Meenal da tsananin kewar Al'ameen ta tashi, baccin minti 30 da ta samu tayi bayan ta idar da sallar asuba, tayi mafarkin shi a d'akin shi, Ya juya mata baya ita kuma tana kuka tana rok'on shi, Mafarkin ya d'aga mata hankali, ya k'ara saka mata tsananin son ganin shi, Kamar wacce aka tsikara ta mik'e, ta saka hijab, bata tarar da kowa a falo ba, dan haka ta samu damar wucewa,
Driver tace ya kaita gida, Ba musu yace toh, ta shiga mota yaja.
Direct part d'insa ta nufa, Jiki a sanyaye ta murd'a k'ofar d'akin sa ta shiga, gani take tamkar zata ganshi, D'aki take bi da kallo, komai tsaf ya kama k'amshin shi, Hoton shi cikin k'aramin frame a bedside drawer wanda shi ya zana da kanshi, ta tsurawa ido, Kamanin shi sak, " Gaskiya Allah ya mishi baiwar zane", Ta fad'a zuciyarta, Idonta ne ya kai kan d'an k'aramin littafi, gefen frame d'in, Da yayi rubutu sam ya manta ya d'auke,
Zuciyarta ke ingiza ta ta d'auka taga littafin meye, Hannu ta kai ta d'auka, Ta koma gefen gado ta zauna, Ta bud'e ta fara karantawa, Fuskarta ce ta mik'e shark'af da hawaye na tausayin Al'ameen, Tabbas tayi rashin hankali na manta waye Al'ameen a wurinta, meyasa idonta ya rufe tak'i sauraren shi, ko yana neman mata bai kamata ta yarda zai aikata hakan gareta ba, Meya shiga kan shi ranar, ta bayarwa kanta tsananin sha'awa ce tunda ya saba, yasa ya aikata hakan gareta ba tare da ya sani ba, idon shi ya rufe yana buk'atar mace, Ya Al'ameen meyasa ka fad'a wannan rayuwa, ka dawo na fad'a maka na yafe maka, nayi maka Nasiha kaji tsoron Allah ka daina zina"
Rungume littafin tayi a k'irjinta, tana kuka mai cin rai, Soyayya, k'auna da tausayin wane hali yake ciki ya dabaibaye ta,
"Wannan shine gargad'i na k'arshe da zan maka, ko kasa hannu ko wallahi na harbe ka da bindigar nan", " Zanyi signing amma da sharad'i d'aya", Jin har yace zai saka hannu yasa yace "Wane sharad'i?", " Ka sanar dani wanda ya saka ka aikin nan", Dariya yayi yace "Abu d'aya zan fad'a maka macece, kuma mafi kusanci da kai", Ya jinjina kai ya karb'i paper d'aya yasa hannu, Sauran yace sai gobe,
Dantse cike da murna ya fita, ya kira Layla ya sanar da ita, cikin jin dad'i ta yaba mishi da alk'awarin k'arin kud'i idan yasa a sauran.
_kuyi hak'uri da wannan, Am too busy_
*Follow*
*Vote*
*Like**ZEELISH*💕
YOU ARE READING
MEENAL WA LAMEEN
Romance"A da ina son ka ina k'aunarka ina ganin girman ka , k'imar ka mutuncin ka darajar ka, A yanzu na tsane ka tsana mafi muni, ba wanda na tsani gani kamar ka, ka aikata abunda ko kafiri yayi sai al'umma tayi Allah wadarai dashi, Wallahi Wallahi Wallah...